An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya
Published: 11th, April 2025 GMT
Kungiyar Afica city of Refugee ta gabatar da taron bukatar da kuma muhimmancin samun zaman lafiya a tsakanin Makiyaya da Manoma a garin Saka wanda ya ke karkashin jagorancin gundumar ci gaba ta Karshi da Uke,Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa saboda a tattaunakan lamarin daya shafi zaman lafiya tsakanin Fulani Makiyaya da kuma Manoma.
Mutane da dama ne suka samu halartar taron wanda aka yi a Saka a makarantar Sakandare ta Saka daga cikin Shugaban kungiyar zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista na Karamar HUkumar Karu Reberend Timothy.
Sin Ba Za Ta Razana Da Zuwan Yakin Cinikayya Ba Huawei Ya Daddale Yarjejeniya Da Kenya Don Habaka Kwarewar Ma’aikatan Kasar A Fannin DijitalReberend Justin darekta wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar ya yi jawabi ne mai daukar hankali kan muhimmancin zaman lafiya,shi ma Sarkin Saka,Injiniya Adamu ya nuna farincikinsa dangane da shi taron.
A na shi jawabin Bound Bradam ya yi kira da makiyaya Fulani da manoma da cewar su hada kansu da Sarakuna,Hakimai,Dagatai,da masu Unguwanni, domin habaka,da kuma inganta harkar zaman lafiya a tsakaninsu,a kuma kara da cewa yana son Fulani makiyaya a zuciyarsa, hakan ya sa yake ta ta duk yin abinda zai iya ba domin komai bas a don ya ga an ci gaba da zaman lafiya tsakanin su Manoma da Fulani makiyaya wadanda a shekarun da suka gabata ba jin tsakaninsu,zama ne suke na ‘yan’uwantaka da zumunci domin kuwa suna amfana da juna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Makiyaya zaman lafiya tsakanin
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 3 sun mutum yayin haƙar rijiya a Kano
Wasu mutane uku sun rasu yayin da suke tsaka da aikin yasar rijiya a garin Badume da ke Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano.
A yayin da suke aikin haƙar rijiya, ɗaya daga cikinsu ya shiga domin yasowa biyu kuma na janyo ƙasar da aka haƙo.
Ana cikin haka igiyar ta tsinke, inda nan take ƙasa ta koma kan dattijon mai shekara 65 da ke haƙar rijiyar.
Hakan ya sa ɗansa mai shekara 20 shiga rijiyar domin fito da shi amma abu ya tura.
A nan ne na ukunsu mai 60 Yakubu Abdullahi shi ma ya shiga domin ceto su, amma duka dai abu ya gagara.
A ƙarshe jami’an Hukumar Kashe Gobara sun yi nasarar ceto su ukun a sume, amma daga baya likita ya tabbatar da rasuwarsu bayan kai su asibiti kamar yadda mai magana da yawun rundunar ya bayyana.