Darasi daga rayuwar Dakta Idris AbdulAzeez Dutsen Tanshi
Published: 11th, April 2025 GMT
Rasuwar Sheikh Dakta Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi rasuwa ce da ta jijjiga al’ummar Nijeriya da ma ƙasashen ƙetare, bisa la’akari da irin faɗakarwarsa da karantarwarsa da gwagwarmayarsa.
Hakan ya jawo dandazon al’ummar Musulmi suka halarci sallar jana’izarsa kuma fitattun mutane da malamai suka yi ta yin ta’aziyyar rasuwarsa.
Lokacin da Malamin yake raye kusan a kulum sai ya gabatar da huɗuba ko darasi na wayar da kan al’umma ko kuma ilmantar da su kan wani abu mai muhimmanci a masallacinsa da makarantarsa.
A ’yan shekarun nan Allah Ya jarrabe shi da rashin lafiya, wanda a sanadiyyar haka ya xauki tsawon lokaci ba a ji huɗubarsa ko karantarwarsa ba da suke xaukar hankalin dubban masu sauraro a faɗin Afirka, lamarin da ya jawo damuwa a tsakanin almajirai da kuma al’umman da ke bin karantarwarsa.
Rahotanni sun bayyana cewa, Malamin ya ɗauki lokaci mai tsawo yana fama da rashin lafiyar, kuma a wasu lokutan yana zuwa jinya, ya dawo, ya ci gaba da koyarwa kamar yadda ya saba.
Dakta Idris ya rasu ne daren Alhamis 4 ga watan Afrilun 2025, a gidansa da ke Bauchi bayan ya dawo daga jinya daga ƙasar Indiya.
Dakta Tauhid kamar yadda ake yi masa laƙabi, a bana ma bai samu gabatar da wa’azin da ya saba gabatarwa ba duk shekara cikin watan azumi kamar dai yadda bai yi ba a bara ba sakamakon rashin lafiya.
Malamin ya yi suna wajen karantar da Tauhidi da dogewa a kan gaskiya ko faɗar gaskiya komai ɗacinta ba tare da tsoron kowa ba ko kuwa shakka.
A lokacin da yake raye ya sha gwagwarmaya walau da malamai ko da ’yan siyasa waɗanda suke samun savanin fahimta da shi, musamman wajen ɗabbaƙa wata sunna ko kuma yi musu raddi kan wasu kurakurai da ya fahimta.
Dakta Idris mutum ne mai gudun duniya da ba ya shayin ɓoye fahimtarsa a kan duk wasu lamura da suka shafi addini ko siyasa ko da kuwa yin hakan zai zamo mai hatsari a gare shi.
Marigayin ya sha fama da tashe-tashen hankula da dama da kuma rashin jituwa da gwamnatocin baya a Jihar Bauchi, da ma samun savani da malaman ƙungiyoyin addinin Musulunci, wanda hakan ya sanya aka xaure shi a lokuta da dama tare da sanya shi yin gudun hijira ta wani ɗan lokaci.
Duk da irin saɓanin fahimta da yake yawan samu da malamai da kuma ’yan siyasa, da yawa daga cikinsu sun fito, sun yi addu’oi’n neman gafara gare shi, tare da bayyana shi a matsayin wani ginshiƙi na jaddada addini ta hanyar ƙarfafa tauhidi da ya shafe fiye da shekara 30 yana yi.
Hatta ma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulƙadir Muhammed, wanda a zamanin mulkinsa saboda savanin da suka samu, an kai Dokta Idris gidan gyaran hali har sau biyu, ya je, ya yi ta’aziyyar rasuwar Malamin inda ya ce, ya yafe masa abin da duk ke tsakaninsu har ma ya yi alƙawarin mayar wa ɗaliban Malam Idris filin Sallar idi da a da gwamnatinsa ta ƙwace daga hannun marigayin.
Wasu daga cikin waɗanda suka yi mu’amala da malamin, sun bayyana shi da cewa, mutum ne mai godiyar alherin da aka yi masa kuma yana da zumunci da kyauta da yawan alheri.
Musa Azare ya ce, ‘‘ko kafin rasuwarsa na kira wani makusancin Imam Idris don in ba shi saƙo ya isar masa na gaisuwa da addu’ar Allah Ya ba shi lafiya, kamar yadda daman ta hanyar wannan mutumin muke sada zumunci da Malam. Sai mutumin ya ce min jikin malam fa ya yi tsanani. A taya shi da addu’a.”
Bayanai sun nuna, a asibitin da Malam ya je a ƙasar Indiya, sun nemi ya zauna a wajensu domin yana shan wasu magunguna, kuma magungunan za a xauki tsawon lokaci ana shan su, kafin a yi masa tiyata da kuma kula da shi a-kai-akai. Amma sai ya ce, shi ba zai zauna, ya mutu cikin waɗanda ba Musulmai ba. Gara ya dawo gida Nijeriya, idan ya gama shan magungunan sai ya koma asibiti. Idan kuma lokacinsa ne ya yi, to mutuwa ta riske shi cikin iyalai da ’yan uwansa Musulmi.
Dakta Tauhid ya gina makarantun sakandare da Kwalejin Horar da Malamai Ilimi Mai Zurfi wato, ‘College Of Education Dutsin Tanshi Bauchi’, kuma yana ba da ilimi kyauta ga ’ya’yan talakawa da marayu waɗanda ba su da halin biyan kuɗin karatu.
Har ma wani lokaci a watan Oktoba na shekarar 2023, saboda tsananin ƙuncin talauci da jama’a suka shiga, Malam Idris Abdul’aziz Bauchi Hafizahullah ya yafe wa duk wani ɗalibi kuɗin rajistar zangon karatu na farko a matakin NCE da Diploma a makarantarsa ta College of Education Dutsen Tanshi.
Ba Musulmi ne kawai suka ji daɗin mu’amala da malamin ba, har ma da Kiristoci, inda hatta Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Honarabul Yakubu Dogara a saƙon ta’aziyyarsa ya ce, ‘‘na sami labari mara daxi na rasuwar ɗan uwana, abokina kuma ɗan kishin ƙasa, Sheik Dakta Idris Abdulazeez. Na san malam da alaƙa ta ƙut-da-ƙut da kuma dangantakarmu ta ƙara ƙarfi kuma mun haɗa kai a matsayinmu na ’yan uwa, musamman a shekarar 2023 yayin da muke haɗa kan ’yan Bauchi don ƙwato kansu daga sarƙaƙiyar da ta ɗaure su.
“Zan iya cewa zuciyar malam ta kasance tana jin tausayin waɗanda aka zalunta. Ya kasance mai jaruntaka, ba shi da tsoro kuma a kodayaushe ba ya jin tsoron faɗin gaskiya ga mai mulki ko da wane ne yake kan mulkin. Shi ba malamin addinin Musulunci ba ne kawai, shugaba ne marar son kai kuma mai taimakon jama’a da ba a saba gani ba. Kowa zai yi kewar sa sosai,”
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya turo Babban Mai Ba shi Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, inda ya zo tare da Sanata Shehu Buba wanda ya biya duk bashin da ake bin malamin. Haka ma Shugaban Gwamnonin Arewa, Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya isar da ta’aziyyar dukkan gwamnonin game da rasuwarsa.
Gwamna Inuwa ya ce, rasuwar Sheik babban rashi ne, ba wai ga iyalansa da al’ummar Jihar Bauchi kaɗai ba, har ma da fannin ilimin addinin Musulunci, musamman ga waɗanda suka samu ƙwarin gwiwa suka samu ilimi mai nagarta daga hikima da jagoranci irin na malamin.
Ya miƙa sakon ta’aziyyar gwamnonin ga iyalan mamacin da gwamnatin Jihar Bauchi da sauran al’ummar Musulmi. Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya saka wa Dakta Idris da Aljannar Firdausi.
A cikin wasiyyarsa, Marigayi Malma Idris ya hana ɗaukar hoto a wajen jana’izarsa kuma ya soke taron ta’aziyya ko na tunawa da shi a gidansa. Haka kuma ya hana mutane yin turereniya wajen ɗaukar gawarsa da kuma shiga maƙabartar da takalmi. Dubban mutane ne suka yi dandazo kuma suka halarci jana’izarsa
Imam Idris ya yi shekara 58 a duniya kafin rasuwarsa, inda ya yi karatun addini a nan gida Nijeriya da ƙasar Saudiyya, inda ya samu digiri a fannin shari’ar Musulunci a Jami’ar Musulunci ta Madina, ya kuma yi digiri na biyu a Jami’ar Jos da kuma digiri na uku a fannin shari’a a wata jami’ar da ke qasar Sudan.
Za a ci gaba da tuna Malam da irin darussan da ya koyar, musamman yadda ya shahara da wa’azin da ba tsoro, wanda galibi yana sukar manufofin gwamnati, musamman kan batutuwan da suka shafi mulki da cin-hanci da rashawa da take haƙƙin al’umma. Marigayin ya rasu ya bar mata da ’ya’ya da dama da kuma tarin ɗalibansa da dubban masoya a faɗin duniya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Bauchi
এছাড়াও পড়ুন:
Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
Daga Usman Muhammad Zaria
Kananan manoma a jihar Jigawa sun yabawa kungiyar Sasakawa Africa dangane da tallafin da take samarwa a fannin inganta noma.
Yayin tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin musamman manoman shinkafa a garin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, sun bayyana cewa tallafin Sasakawa ya habaka noman shinkafar su tare da samun karin kudade.
Manoman sun bayyana cewar shirin ya taimaka masu wajen bunkasa harkokin noma tare da tallafawa al’ummomin su.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin a yankin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, Buhari Nafi’u, yace Sassakawa Africa ta samar masu da tallafin noma daban daban.
A cewar sa tallafin sun hada da horo wanda ya taimakawa kananan manoma wajen ganin sun kara samun kudade tare da inganta rayuwar maza da mata a yankin.
Yace a wannan shekarar sun noma amfanin gona mai yawa sakamakon horon da suka samu karkashin shirin, inda suka hadu sukayi noman a kungiyance a yankin Birnin Kudu.
Buhari ya kara da cewar, a shekarun baya suna daukan kwanaki casa’in kafin su girbe shinkafa amma zuwan Sassakawa ya sa sun yi noma tare da girbe amfanin gonan su a cikin kwanaki saba’in saboda irin da kungiyar ta basu.
Yace yanzu haka sun fara amfani da shinkafar da suka noma a gidajen su.
Yace an basu takin zamani kyauta tare da sauran kayayyakin feshi.
Ya godewa tallafin na Sassakawa, yana mai cewar zai cigaba da amfani da irin da aka basu tare da koyar da mazauna yankin abubuwan da aka horar da su akai.
Shi ma Malam Rufai Nasiru daga yankin na Chandam yace sun kara samun ilimi akan sabbin dubarun noma wanda suka samu daga kungiyar ta Sassakawa.
Yace a bana ya noma buhun shinkafa 8 ba kamar a baya ba da yake noma buhu biyar, yana mai cewa shirin yana da inganci kuma zai cigaba da amfani da irin da kungiyar ta basu.
A garin Chuwasu dake karamar hukumar Taura, Aminu Babanyara ya bayyana cewar sun ci moriyar shirin ta hanyar samun iri masu inganci da takin zamani da kuma horo akan sabbin dubarun noma.
Yace wasu daga cikin abubuwan da suka koya sun hada da amfani da shara wajen yin taki a gida inda suka ce hakan yasa sun samu karin shinkafa da geron da suke nomawa idan aka kwatanta da shekarun baya.
Babanyara, yace sabbin dubarun da suka koya da kuma irin da Sassakawa suka basu, ya basu damar ninka abin da suka saba nomawa a damina sau uku.
Yace da farko suna da shakku akan amfani da sabbin irin da sabbin dubarun noman, amma kuma bayan sun gwada a shekaru biyu na farko sun ga alfanun hakan wajen bunkasa amfanin gonan da suke nomawa.
Manoman sun kuma yi kira ga kunyiyar ta Sassakawa ta samar masu da injinan casa domin saukaka masu al’amura.
Malama Amina Abdulrahman wacce tayi jawabi a madadin kungiyar mata manoma a Karamar Hukumar Taura, tace shirin tallafin Sassakawa ya kawo sauyi a rayuwar su musamman a fannin samun kasuwanci da amfanin gonar da ake sarrafawa don yin abinci mai gina jiki na yara.
A cewar ta an horar da su akan yadda za su samar da abinci mai gina jiki a yankuna tare da yadda za su yi aiki a kungiyance don inganta noma.
A don haka, tayi kira ga kungiyar Sassakawa ta samar masu da injinan sarrafa amfanin gona na zamani.
Yankunan da aka ziyarta sun hada da Chandan dake Birnin Kudu da kuma Sabon Gari shi ma a karamar hukumar Birnin Kudu.
Sauran sun hada da Baranda dake Dutse da kuma Chuwasu dake karamar hukumar Taura.