Aminiya:
2025-09-18@00:44:35 GMT

A ɗora min laifin hatsarin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja — Shugaban NRC

Published: 27th, August 2025 GMT

Shugaban hukumar kula da jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC), Kayode Opeifa, ya ce ya ɗauki alhakin hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da ya auku a ranar Talata.

Aminiya ta ruwaito cewa hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11 na safe bayan jirgin ya taso daga Abuja zuwa Kaduna.

Dilan ƙwaya ya shiga hannu a Borno ASUU: Malaman Jami’ar FUK sun yi zanga-Zanga kan rashin cika musu alƙawura 

Da yake zantawa da gidan talabijin na Channels a yau Laraba, Opeifa ya ce ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen binciken abin da ya haddasa lamarin.

“Bayan neman gafarar ’yan Najeriya, a matsayina na shugaban hukumar, na ɗauki alhakin duk abin da ya faru,” in ji shi.

“Ba za mu ɗebe tsammanin faruwar irin wannan lamari ba, amma duk lokacin da hakan ta kasance, tana ƙara mana fahimtar wuraren da suke buƙatar mu inganta.”

Hukumar agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta tabbatar da cewa mutum bakwai suka ji rauni bayan aukuwar hatsarin waɗanda tuni sun samu kulawar gaggawa daga likitoci.

A jiyan ne dai NRC ta sanar da dakatar da sufurin jirgin ƙasan da ke jigila tsakanin Kaduna da Abuja har zuwa lokacin da za ta kammala bincike kan musabbabin faruwar lamarin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jirgin Ƙasa Kayode Opeifa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya janye dokar ta-ɓaci da ya ayyana ta tsawon watanni shida a Jihar Ribas.

Tinubu, ya ayyana dokar tun a ranar 18 ga watan Maris, 2025, saboda rikicin siyasa da ya haifar da tsaiko a harkokin mulki tsakanin ɓangaren Zartarwa da Majalisar Dokokin jihar.

NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025 Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi

A jawabin da ya gabatar a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Laraba, Tinubu ya ce matakin dokar ta-ɓacin ya cimma manufarsa, kuma ba za a tsawaita ba ƙarewar wa’adin da aka gindaya.

“Ina farin ciki yau game da bayanan da ke hannuna, an samu yanayin fahimta a tsakanin dukkanin masu ruwa da tsaki a Jihar Ribas domin dawo da mulkin dimokuraɗiyya cikin gaggawa,” in ji Shugaban Ƙasa.

Gwamnan Jihar, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, tare da ‘yan majalisar dokokin jihar, za su koma kan kujerunsu daga ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba, 2025.

Tun da farko, dokar ta-ɓacin ta dakatar da manyan jami’an gwamnati da masu madafun iko na jihar sakamakon rikici da aka daɗe ana yi a jihar.

“Da ban ayyana wannan dokar ta-ɓacin ba, da hakan ya zama babbar gazawa a wajena a matsayina na Shugaban Ƙasa.

“Amma yanzu da zaman lafiya da doka suka wanzu, al’ummar Jihar Ribas za su sake cin moriyar dimokuraɗiyya,” in ji Tinubu.

Ya kuma yi kira ga gwamnoni da majalisun dokokin jihohi na faɗin Najeriya da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin ɓangaren zartarwa da na majalisa.

Har ila yau, ya jaddada cewa zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci su ne tubalin kawo ci gaban dimokuraɗiyya ga al’umma.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
  • Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
  • Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara
  • Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara