HausaTv:
2025-12-08@03:44:04 GMT

 Iraki: An Kashe Shugaban Kungiyar “Da’esh” Na Iraki Abdullahi Makki

Published: 15th, March 2025 GMT

A jiya juma’a ne dai firma ministan kasar Iraki Muhammad Shi’ya al-Sudani ya sanar da cewa sojojin kasar sun kashe babban dan ta’adda Abdullahi Makki wanda ake yi wa lakabi da Abu Hadiza.

Al-Sudani ya kara da cewa; Iraki taba cigaba da samun nasara akan ‘yan ta’adda, bayan da jami’an tsaro na kasa da kasa su ka yi nasarar kashe Abdullahi al-makki, wanda ya kasance a matsayin  mataimakin shugaban abind ake kira da Daular Musulunci a Iraki da Syria.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An kashe matashi yayin rikici a wajen raɗin suna a Bauchi

Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna, ya rasa ransa bayan fada ya barke a lokacin bikin radin suna a ƙauyen Kwata da ke Karamar Hukumar Warji ta Jihar Bauchi.

Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da sa’insa ta barke tsakanin wasu matasa ta rikide ta zama fada, wanda ya bar Haruna cikin rashin hayyacinsa.

Tinubu ya naɗa tsohon kantoman Ribas da Dambazau a matsayin Jakadun Najeriya ’Yan sandan Borno sun kama matashin da ake zargi da kashe makwabciyarsa da wuƙa

“Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna na ƙauyen Kwata, Karamar Hukumar Warji, Jihar Bauchi, ya riga mu gidan gaskiya bayan rikici mai tsanani da ya barke a bikin radin suna a ranar 2 ga watan Disamba, 2025,” in ji Zagazola Makama, masani kan harkokin tsaro a yankin arewa maso gabas.

Ya kara da cewa rashin jituwa tsakanin wasu matasa a wajen bikin ta rikide zuwa fada, lamarin da ya bar wanda abin ya shafa ya suma nan take.

An ce an garzaya da Haruna zuwa Asibitin Gwamnati na Warji, amma ya rasu a yayin da ake masa jinya.

Da aka tuntubi mai magana da yawun ’yan sanda na jihar, Ahmed Wakili, ya ce yana cikin taro kuma ya yi alƙawarin dawowa da bayani, sai dai bai yi hakan ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Benin : Har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin_fadar shugaban kasa
  • ’Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato
  • ’Yan bindiga ya hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato
  • Fadar Shugaban Kasar Benin ta ce Har Yanzu Talon Ne a Kan Mulki
  • Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167
  • Gwamnatin Iraki Ta Kore Saninta Da Shigar Da Sunayen Hizbullah Da “Ansarullah” A Cikin Na ‘Yan Ta’adda
  • Limamin Tehran:  Idan Abokan Gaba Su Ka  Sake Yin Kuskure Akan Iran Za Su Sake Cin Kasa
  • Dorinar ruwa ta kashe mutum 2, ta jikkata 6 a Gombe
  • Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — Zulum
  • An kashe matashi yayin rikici a wajen raɗin suna a Bauchi