NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa?
Published: 13th, March 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya na ci gaba da tsananta, lamarin da ya sa wasu al’umma ke neman hanyoyin kare kansu.
Ɗaya daga cikin hanyoyin da wasu yankuna suka ɗauka shi ne yin yarjejeniya da ’yan bindiga da ke addabar su, domin samun zaman lafiya.
NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin AzumiShin yin sulhu da ’yan fashin daji ita ce mafita? Kuma yaya halin yankunan da suka ƙulla irin wannan yarjejeniya yake a yanzu?
Shirin NAJERIYA A YAU, zai yi duba kan yadda wasu al’umma ke ƙoƙarin tsira daga matsalar tsaro ta hanyar yarjejeniya da ’yan bindiga, da kuma irin tasirin da hakan ke haifarwa.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda Birnin Gwari Tsaro NAJERIYA A YAU
এছাড়াও পড়ুন:
Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Yi Wani Hatsari a Neja
Wani jirgin Sojin saman Najeriya ya yi haɗari jim kaɗan bayan tashi daga sansanin Sojin ƙasar da ke Kainji a jihar Neja, sakamakon tangarɗar inji.
Kakakin rundunar sojin saman na Najeriya Ehimen Ejodame lokacin da yake tabbatar da faruwar haɗarin ya ce babu ko mutum guda da ya rasa ransa sanadiyyar wannan haɗari, sai dai fasinjan da ke cikin jirgin yanzu haka suna karɓar kulawar gaggawa a asibiti.
Tuni dai aka jiyo hafson sojin saman Najeriyar Air Marshal Sunday Aneke, na yabawa matuƙan jirgin wanda ya bayyana da jajirtattu, da ya ce ƙwarewa da jarumtarsu ce ta tseretar da asarar rayuka a haɗarin.
Jiragen sojin Najeriya a lokuta da dama na gamuwa da haɗari wanda ke kaiwa ga asarar ɗimbin rayuka kama daga na sojojin da kuma fararen hula, dai dai lokacin da ƙasar ke buƙatar agajin sojojin na sama wajen yaƙi da matsalolin tsaron da suka dabaibaye ƙasar.