Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [5]
Published: 13th, March 2025 GMT
Wannan magana tana nuni da cewa idan mutum ya nemi kariya a wurin Allah da zuciya ɗaya, to Allah zai amsa roƙonsa kuma zai kare shi daga duk wani abu mai cutarwa. Wannan yana da asali a cikin koyarwar Musulunci, inda ake koyar da Musulumi su nemi tsari wurin Allah kaɗai daga sharrin Shaiɗanun aljanu da mutane da duka wani maicutarwa a cikin halittu baki ɗaya, da kuma neman tsari da kariya daga miyagun halaye, da duk wani abu da zai cutar da su a duniya da lahira.
A taƙaice, wannan magana ta Ibnu Juzai a-Kalbi tana da muhimmanci sosai a rayuwar Musulumi, domin tana ƙarfafa imani da cewa duk wanda ya dogara ga Allah kuma ya nemi kariya da gaske, Allah zai kare shi daga duk wani sharri. Wannan yana ƙarfafa Musulumi su kasance masu gaskiya a addu’arsu da neman tsari da Allah cikin kowane hali.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Abu Razina Nuhu Ubale Paki Ramadan
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya naɗa Janar CG Musa sabon Ministan Tsaron Nijeriya
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan tsaron, Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaron Nijeriya
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata.
Sanarwar ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio wasiƙar sanar da shi sabon naɗin da ya yi.
Naɗin Janar Musa na zuwa ne kwana guda bayan murabus ɗin Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya sauka daga muƙaminsa ranar Litinin saboda dalilai na rashin lafiya.
Musa wanda zai cika shekara 58 a ranar 25 ga Disamba, ya yi aiki a matsayin Babban Hafsan Tsaro daga 2023 har zuwa Oktoban 2025 lokacin da Shugaban Kasa ya sauke shi daga muƙamin a watan Oktoba, bayan wani yunkurin juyin mulki da aka yi.