Ukraniya Ta Hai Wa Birnin Moscow Hari Da Jirage Marasa Matuki
Published: 11th, March 2025 GMT
Tare da cewa Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki fiye da 60 da Ukiraniya ta harba, sai dai an sanar da mutuwar mutum daya a birnin Moscow.
Kantoman yankin Moscow Andrey Vorobyov ne ya sanar da cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu 3 su ka jikkata, sanadiyyar hare-haren da Ukiraniya ta kai wa birnin da makamai masu linzami masu yawa da safiyar yau Talata.
Kantoman Mascow ya rubuta a shafinsa na “Telegram’ cewa; “ ya zuwa yanzu an sami labarin mutuwar mutum guda da kuma jikkata wasu 3 a garin Fidnoveh a kudancin Moscow.”
Sai dai daga baya wasu kafafen watsa labarun Rasha sun ambaci cewa adadin wadanda su ka jikkata din ya karu zuwa 5.
Haka nan kuma Andrey Vorobyov ya kara da cewa; Wasu gidaje bakwai sun illata saboda faduwar jirgin maras matuku a kansu.
A garin Domodedovo kuwa an sanar da tashin gobara sanadiyyar faduwar jirgi maras matuki da Ukiraniya ta harba, kuma wasu baraguzan jirgin da su ka fadi a kusa da tashar jirgin kasa ya yi barna sai dai ba mai girma ba. Tuni aka dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a yankin.
Kantoman birnin Moscow ya kuma sanar da cewa, sojoji sun yi nasarar kakkabo jiragen sama marasa mutuki 73 da ukiraniya ta harba wa birnin.
Saboda wadannan hare-haren an dakatar da tashi da saukar jiragen saman a cikin filayen sama fiye da uku da suke kusa da Moscow.
A ranar Lahadin da ta gabata ma dai sojojin Rasha sun sanar da kakkabo fiye da jirage marasa matuki 88 a saman yankunan kasar mabanbanta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Karatun Baya Dangane Da Tarihi Shi Ne Abun Da Ya Kamaci Japan
CGTN ta gabatar da kuri’un jin ra’ayin jama’ar ne ta harsunan Turancin Ingilishi, da Sifaniyanci, da Faransanci, da Larabci, da harshen Rasha. Inda masu bayyana ra’ayoyi 10,451 suka fayyace mahangarsu cikin sa’o’i 24. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA