UNRWA ta bukaci Isra’ila da ta bari a shigar da kayan agaji a Gaza
Published: 11th, March 2025 GMT
UNRWA ta yi kira ga Isra’ila da ta kawo karshen hana shigar da kayan agaji a zirin Gaza domin dakile bazuwar yunwa da wahala a yankin.
“Mun riga mun ga alamun farko na karin farashi a kasuwa,” in ji Kwamishinan UNRWA Philippe Lazzarini yayin taron manema labarai a wannan Litinin, ya kara da cewa yayin da lokaci yake kara kurewa, tasirin haramcin yana karuwa a Gaza.
Lazzarini ya kara da cewa “akwai hadarin komawa ga yanayin da muka fuskanta watannin da suka gabata, game da kara yaduwar yunwa a tsakanin mutanen zirin Gaza sakamakon matakan da Isra’ila take dauka.
“Isra’ila” ta sanar da dakatar da isar da kayayyakin jin kai zuwa Gaza a ranar 2 ga Maris, tare da yin barazanar kara matsin lamba kan Hamas, yayin da bangaren ‘yan gwagwarmayar Falasdinu ya ki amincewa da shawarar Amurka na tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta farko, maimakon shiga mataki na biyu kamar yadda yarjejeniyar tanada tun daga farko.
A wani mataki na baya-bayan nan na kara matsa lamba kan al’ummar zirin Gaza, Ministan Makamashi na Isra’ila Eli Cohen ya sanar da cewa, ya rattaba hannu kan wata doka ta katse wutar lantarki a yankin Gaza daga ranar 9 ga Maris, yana mai jaddada cewa “Isra’ila za ta yi amfani da dukkan kayan aikinta wajen dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma tabbatar da kawo karshen samuwar Hamas a cikin Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Salami: Makiyan Iran Ba Su San Wani Abu Ba Sai Karfi
Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran manjo janar Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin tunawa da shahid Mahadi Bakiri a garin Tabriz ya bayyana cewa;; Babu yadda za ayi jamhuriyar musulunci ta Iran ta bude tattaunawa da Amurka a karkashin barazana, yana mai kara da cewa; yin gwawarmaya da jajurcewa a gaban masu girman kai da daga hanci, yana daga cikin muhimman koyarwar alkur’ani mai girma da kuma tsarin musulunci.
Manjo janar Salami ya kara da cewa; ta hanyar tsayin daka da dunkulewar al’umma wuri daya, za a kai ga samun nasara.
Haka nan ya kara da cewa; A tsawon shekaru 46 da su ka gabata, al’ummar Iran ta kasance a cikin fadaka wajen fuskantar duk wata barazana.
Bugu da kari kwamandan dakarun kare juyin juya halin musuluncin na Iran ya kuma ce; Makiyan jamhuriyar musulunci ta Iran masu kekashewar zukata ne, ba su aiki da mandiki, kuma ba su aiki da duk wata halayya ta ‘yan ta ‘yan adamtaka,abu daya tilo da su ka yi imani da shi, shi ne amfani da karfi.
Har ila yau, kwamandan dakarun kare juyin musuluncin na Iran ya yi ishara da halayyar HKI da Amurka a yakin Gaza, Lebanon, Syria, Yemen, Iraki da Afghanistan; yana mai kara da cewa; sun tabbatar da cewa, su masu karya alkawali ne, don haka batun tattaunawa da wadannan makiyan kuskure ne