Aminiya:
2025-03-28@10:06:27 GMT

Lakurawa sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Kebbi

Published: 11th, March 2025 GMT

Mayaƙan Lakurawa sun kashe mutum 13 a wani harin ramuwar gayya da suka kai yankin Birnin Debe da ke Ƙaramar Hukumar Arewa a Jihar Kebbi.

Wani mazauni mai suna Musa Gado, ya ce maharan wanda suka kai harin a ranar Lahadi, sun kuma ƙone ƙauyuka takwas daga cikin tara da ke yankin.

Tsohon shugaban Philippines ya faɗa komar ’yan sanda Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet

Shi ma wani mazaunin yankin, Suleiman Abubakar wanda ya rasa ɗan uwansa ɗaya a dalilin harin, ya ce maharan sun auka wa ƙauyukan ne da yammaci bayan sallar Magariba.

“Abin ba a cewa komai domin mun ga tashin hankali. Sun kashe mutane da dama sun ƙone mana ƙauyuka kuma babu wanda suka ƙyale hatta mata da ƙananan yara.”

Aminiya ta ruwaito cewa, galibin waɗanda suka jikkata a dalilin harin yanzu haka suna samun kulawa a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kebbi.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Arewa, Sani Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamari da cewa tuni an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin yayin da gwamnatin ke ci gaba da ɗaukar mataki a kan lamarin.

Harin wanda ake zargin na ramuwar gayya ne na zuwa ne bayan wani farmakin haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da gwamnatin Kebbi, wanda ya yi sanadin mutuwar wani shugaban ’yan ta’addar Lakurawa da ake kira Maigemu.

Majiyoyin leƙen asiri sun tabbatar da cewa an kashe Maigemu a yankin Kuncin Baba da ke Arewacin jihar, bayan fafatawar da aka yi a ranar Alhamis ta makon jiya.

Da take martani, rundunar ’yan sandan jihar, ta ce mayaƙan Lakurawa ne suka kai harin a yankunan Birnin Debi, Dogon Daji, Danmarke, Yar Goru, Tambo, Garin Nagoro da kuma Garin Rugga da ke Arewacin jihar.

Rundunar ta ce mayaƙan ɗauke da muggan makamai sun kai hari a waɗannan yankunan da ke iyaka da Jamhuriyyar Nijar, inda suka kashe aƙalla mutum 11 yayin da wasu biyu suka jikkata.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Nafiu Abubakar ya fitar ta ce maharan sun koma ƙone wasu gida ƙurmus a ƙauyukan da abin ya shafa.

Ana iya tuna cewa, a watan jiya na Fabarairu ne wasu ’yan ta’addan suka kashe wani mutum tare da jikkatar wasu shida a yayin harin da aka kai ƙauyen Gulman da ke Ƙaramar Hukumar Argungu ta Jihar Kebbi.

Kazalika, mayaƙan ake ɗora wa alhakin kashe wasu jami’an hukumar shige da fice biyu da wani farar hula ɗaya a Ƙaramar Hukumar Kangiwa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Kebbi Lakurawa Ƙaramar Hukumar

এছাড়াও পড়ুন:

Kwalara Ta Kashe Mutum 14, Ana Zargin 886 Sun Kamu A Nijeriya – NCDC

NCDC, ta ce yawan masu kamuwa da cutar a bana ya fi na shekarar da ta gabata, inda a lokacin aka samu mutum 506 kacal.

Hukumar ta shawarci al’umma suke shan sha ruwa mai tsafta, su riƙa wanke hannu da sabulu, su ci abinci mai kyau, tare da tabbatar da tsaftar muhalli don guje wa kamuwa da cutar kwalara.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano
  • Isra’ila ta sake kashe wani kakakin Hamas
  • Lakurawa sun kashe jami’an Kwastam 2 a Kebbi
  • HKI Ta Kai Hare-hare A Falasdinu Da Kasar Lebanon
  •  Nigeria: An  Kashe Sojoji Da DAma A Wani Hari Da Aka Kai Wa Sansanonin Soja Biyu Hari A Jihar Borno
  • Mutum 2 sun rasu, wani ya ji rauni a hatsarin mota a Kano
  • Kwalara Ta Kashe Mutum 14, Ana Zargin 886 Sun Kamu A Nijeriya – NCDC
  • Gobarar daji ta kashe mutum 24 a Koriya ta Kudu
  • Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Lebanon Ya Ce Basa Da Wani Shiri Na Samar Da Haldar Jakadanci Da HKI
  • Za mu ɗauko hayar sojojin ƙetare domin horas da dakarun Nijeriya — Badaru