Taro Na Uku Na Majalisar Wakilan Jama’ar Kasar Sin Ya Yi Zama Na Biyu
Published: 8th, March 2025 GMT
A yau Asabar ne aka gudanar da zama na biyu na taro na uku, na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing. Zaman da babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping ya halarta.
Albarkacin kasancewar yau ranar bikin mata ta kasa da kasa, a madadin tawagar shugabannin taron, zaman ya mika fatan alheri ga mata daga dukkan kabilu, da dukkan bangarorin kasar Sin, da mata na dukkan kasashen duniya.
Bugu da kari, rahoton ayyukan zaunannen kwamitin NPC ya nuna cewa, ana shirin bitar dokoki 34 a shekarar nan ta 2025, wadanda suka hada da samar da wata doka, don inganta hadin kai da ci gaban al’ummar kasar. Ban da hakan, zaunannen kwamitin NPC, zai kuma karfafa binciken kafa dokoki masu nasaba da fasahohin AI, da tattalin arzikin dijital da sauransu.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Manchester United ta shiga zawarcin Sergio Ramos
Ƙungiyyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester United ta fara zawarcin tsohon ɗan wasan Real Madrid Sergio Ramos, mai shekara 39,wanda ya bar Ƙungiyar Monterrey ta Mexico.
Ramos wanda a shekarun baya, United ta yi ƙoƙarin ɗaukarsa, yanzu haka yana da damar komawa ƙungiyyar a matsayin kyauta.
Zanga-zanga ta ɓarke bayan haɗarin tirela ta kashe mutum a Yobe Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-ZakzakyUnited dai yanzu haka tana fuskantar matsaloli daga ’yan wasan baya, inda Harry Maguire ke fama da rauni, yayin da sauran ’yan wasan ke tafka kura-kurai.
Manchester dai yanzu haka ta amincewa mai horarwa ta Roben Amorim ya sayi ɗan wasan baya da tsakiya a watan Januairu.
Kawo yanzu dai ƙungiyyar na mataki na 6 da maki 25 cikin wasannin 15 da ta buga a gasar Firimiyya.
A ranar Litinin ƙungiyyar zata karɓi bakuncin Bournemouth a wasan mako na 16 a filin wasanta na Old Trafford.