Ɗan Uwan Gwamnan Kano Da Malaman NNPP Sun Koma APC
Published: 8th, March 2025 GMT
Haka nan, wasu manyan jiga-jigan NNPP daga ƙaramar hukumar Gwale, Mahmoud Salisu Gwale da Farouk Ahmed Gwale, su ma sun koma APC.
Sanata Barau ya tabbatarwa da al’ummar Nijeriya cewa kofa a buɗe take ga kowa.
“A matsayina na Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ina yi wa kowa hidima. Ko da kai ɗan PDP ne, LP, Kwankwasiyya, ko wata jam’iyya, ina tare da kai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Yan Sanda Sun Kama Muhuyi Magaji, Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci a Kano
Gwamnatin Kano ta tabbatar da kama Muhuyi Magaji Rimingado, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar ranar Juma’a, inda ta yi zargi wasu ‘yansiyasa da hannu a kamen nasa.
Wata sanarwa daga ofishin Kwamashinan Shari’a Abdulkarim Maude ta ce jami’an ‘yansanda ne suka kama lauyan a ofishinsa da ke kan titin Zariya da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, kuma suka tafi da shi hedikwatarsu da ke Bompai.
Kwamashinan ya siffanta kamen da “abin damuwa sosai” wanda “ya yi kama da yanayin aikin soja”. Ya yi iƙirarin cewa dakaru kusan 40 ne ɗauke da makamai suka je kama Muhuyi.
“Kwamashinan ya nuna cewa akwai yiwuwar lamarin yana da alaƙa da binciken da ake yi wa wasu manyan ‘yansiyasa,” in ji sanarwar.
Abdulkarim Maude ya kuma yi kira ga rundunar ‘yansandan Najeriya ta yi cikakken bayani game da dalilin kama Muhuyi.