Tun watan Ramadan muke cikin duhu — Al’ummar Jauro Jatau
Published: 17th, August 2025 GMT
Al’ummar unguwar Jauro Jatau da ke kan hanyar Bypass a Ƙaramar Hukumar Akko, Jihar Gombe, sun koka kan dogon lokacin da suka shafe ba tare da samun wutar lantarki ba.
Sun roƙi gwamnati, ’yan siyasa da masu hannu da shuni da su kawo musu ɗauki cikin gaggawa.
Tun a watan RamadanAl’ummar sun bayyana cewa tun watan azumin Ramadan da ya gabata suke cikin duhu, sakamakon ƙonewar transforma da ke yankin, lamarin da ya bar su cikin ƙunci har tsawon watanni, da ke shafar rayuwar su ta yau da kullum.
Wani daga cikin mazauna yankin, Muhammad Idris Gargajiga, ya bayyana cewa duk lokacin da suka kai ƙorafi ana gaya musu cewa yankin ba shi da rumfar zaɓe, abin da ya kira da rashin adalci.
Sarkin Zuru ya rasu yana da shekara 81 NNPP ta lashe zaɓen Bagwai/Shanono a Kano“Mafi yawanmu, kusan kashi 90 bisa 100, mun fito ne daga cikin babban birnin Gombe muka zauna a nan. Amma har yanzu ana tauye mana kallon-kallon ba ‘yan asalin yankin ba,” in ji Idris.
Ya sake yin kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da kuma ’yan siyasa da su dubi halin da suke ciki, su samar da transformer domin dawo da wutar lantarki.
Kasuwanci da walwala sun tsaya cikAl’ummar sun ce rashin wutar ya haifar da tsaiko a harkokin kasuwanci da walwala, tare da shafar rayuwar su ta yau da kullum. Sun bukaci hukumomi su gaggauta ɗaukar mataki domin dawo da wutar yankin.
JED ba ta amsa baWakilinmu ya yi ƙoƙarin tuntubar hukumar samar da hasken wutar lantarki ta Jos Electricity Distribution Company (JED), wadda ke da alhakin samar da wuta a yankin, amma hakan ya ci tura.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja
Wata tankar mai ta yi gobara a wani gudan mai a yankin Tungan-Bunu da ke Ƙaramar Hukumar Rijau a Jihar Neja, lamarin da ya janyo ƙonewar gidaje da kadarori da masu yawa.
Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne a lokacin da tankar take shirin sauke mai a ranar Litinin da yamma, inda wutar ta bazu zuwa gidajen da ke kusa.
Duk da cewa babu wanda ya rasa ransa, lamarin ya haifar da firgici inda mazauna yankin suka yi ta tserewa suka bar gidajensu yayin da tankar ke ci da wuta.
Tankar mai ta yi hatsari a hanyar Lapai-Agaie Amurka za ta tallafa wa Nijeriya daƙile matsalar tsaro Mayaƙan Boko Haram sun fille kan mata 2 a BornoA wani lamari ba daban, wata tankar mai ta kife a kan hanyar Lapai zuwa Agaie, lamarin da ya toshe hanya tare da haddasa cunkoson ababen hawa.
Shaidu sun ce tankar, wadda ke ɗauke da fetur daga Legas zuwa Gombe, ta kife ne da misalin karfe 10 na safe a ranar Litinin bayan jikinta ya rabu da kan motar, ya ƙetare hanya, abin da ya tayar da hankalin jama’a.
Wani mazaunin yankin, Malam Mahmud Abubakar, ya ce jami’an tsaro sun garzaya wajen domin tsare yankin, sannan aka tura ma’aikatan kashe gobara don kauce wa tashin wuta.
Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne a yankin Efu-Nda-Egbo na Ƙaramar Hukumar Lapai, inda ya haddasa cunkoson ababen hawa mai tsanani.
Kokarin tuntuɓar Darakta-Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran wayar da wakilinmu ya yi masa ba.