Denmark na nazarin kakaba wa Isra’ila takunkumi kan batun Gaza
Published: 17th, August 2025 GMT
Firaministar kasarDenmark Mette Frederiksen, wadda a halin yanzu kasarta ke rike da shugabancin kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana a wata sanarwa ga manema labarai a jiya Asabar cewa, kasarta na shirin kakabawa Isra’ila takunkumi, sakamakon yakin da take yi a zirin Gaza da yammacin kogin Jordan.
A wata hira da ya yi da Jyllands-Posten, Frederiksen ta ce “Yanzu Netanyahu ya zama matsala shi a kan kansa,” tana mai cewa “gwamnatin Isra’ila ta wuce gona da iri.
Ta bayyana halin da ake ciki na jin kai a Gaza a matsayin “mummunan bala’i,” tare da sukar shirin Isra’ila na ci gaba da aikin tsugunar da jama’a a Yammacin Kogin Jordan.
Firaministar Denmark ta jaddada cewa kasarta na cikin kasashen da ke neman kara matsin lamba kan Isra’ila, amma har yanzu baki bai zo daya kan wannan batu a tsakanin dukkanin mambobin kungiyar EU ba.
Ta kara da cewa tana son yin amfani da “matsi na siyasa da takunkumi, ko a kan ‘yan share wuri zauna ko ministoci, ko ma a kan gwamnatin Isra’ila baki daya.
Kimanin mako guda da ya gabata ne ministan harkokin wajen Denmark Lars Løkke Rasmussen ya yi kira ga Isra’ila da ta gaggauta janye matakin da ta dauka na mamaye yankin zirin Gaza, yana mai nuna matukar damuwarsa kan halin da ake ciki na jin kai da kuma wahalar da ake fuskanta wajen kai agajin jin kai ga al’ummar Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jakadan Iran a Saudiyya: Kasashen biyu na tuntubar juna a kan muhimman batutuwa na yankin August 17, 2025 Gaza: A cikin sa’o’i 24 Mutane da dama sun yi shahada daruruwa sun jikkata a hare-haren Isra’ila August 17, 2025 An kashe mutane 17 a harin da dakarun RSF suka kai a El Fasher, Sudan August 17, 2025 Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Yi Allah Wadai Da Kalaman Netanyahu Kan Mamaye Yankunan Kasashe August 16, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Furucin Jami’ar Kotun ICJ Na Goyon Bayan Isra’ila August 16, 2025 Araqchi Ya Gode Wa Gwamnatin Iraki Da Al’ummarta Kan Kyakkyawar Tarbar Masu Ziyarar Arba’een August 16, 2025 Hamas Ta Yi Allah Wadai Da Sanya Ta Cikin Jerin Sunayen Bakin Littafin MDD August 16, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Tafka Muggan Ayyukansu A Yankin Zirin Gaza August 16, 2025 Mataimakiyar Shugaban Kotun ICJ Ta Ce Tana Goyon Bayan HKI August 16, 2025 Burtaniya Zata Gurfanar Da mutane 60 Saboda Goyon Bayan Falasdinawa August 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A cikin ‘yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya.
Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da ‘yan uwa sau da yawa suna fuskantar babban zabi mai wahala: biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko tsayawa da kafafun tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi.
Shin ko ya kamata alumma su cigaba da biyan kudin fansa idan an yi garkuwa da ‘yan uwansu?
Wannan shine batun da shirin Najriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a akai.
Domin sauke shirin, latsa nan