Za A Sabunta Filin Jiragen Sama Na Ilori Zuwa Cibiyar Jigilar Kayayyaki Ta Zamani
Published: 16th, August 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kwara ta ce za ta yi haɗin gwiwa da Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) da sauran masu ruwa da tsaki domin mayar da jihar cibiyar fitar da kayan gona da na kasuwanci.
Kwamishinan Noma da Ci gaban Karkara na jihar, Dakta Afees Abolore, ne ya bayyana haka a wani taron da Hukumar FAAN ta shirya domin sanar da shirin fara jigilar kayayyaki a Filin Jiragen Sama na Ƙasa da Ƙasa na Janar Tunde Idiagbon da ke Ilori.
A cewarsa, wannan shiri na nufin kara inganta matsayin jihar tare da ƙarfafa rawar da take takawa a harkokin kasuwanci na cikin gida da waje.
Ya jaddada cewa aikin ya yi daidai da manufofin wannan gwamnati na buɗe sababbin hanyoyin fitar da kayayyaki, bunƙasa harkokin kasuwanci, da kuma ƙara samun kuɗaɗen shiga ga masu samar da kayayyaki da ‘yan kasuwa.
Dakta Abolore ya ce jigilar kayayyakin ta jiragen zai sauƙaƙa daukarsu daga gonaki, zuwa masana’antu, da wuraren sana’o’i zuwa kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje, wanda hakan zai ƙara musu daraja, sarrafawa da a fannoni daban-daban.
Kwamishinan ya bayyana cewa shirin zai rage asara, ya kiyaye ingancin kayayyaki, sannan ya bunƙasa damar kasuwanci a fannin kayayyakin gona, masana’antu, da kayayyakin da aka sarrafa.
Ya nuna cewa saboda cunkoson da ake samu a tashoshin jiragen sama da na ruwa da ke Legas, garin Ilori na wata dama ta musamman wajen samun fitar da kayayyaki cikin lokaci da inganci, tare da ƙara wa jihar damar gogayya da jihohi da ma kasashen duniya.
Dakta Abolore ya yi kira ga manoma, ƙungiyoyi, masu masana’antu, masu saka jari, ƙungiyoyin sufuri, ‘yan kasuwa, masu sarrafawa, da hukumomin da ke kula da doka da tsari, da su haɗa kai wajen kara inganci, yadda ake shirya kayayyaki daidai da zamani, da amfani da fasaha domin bin ka’idojin kasuwannin ƙasashen waje.
Shi ma Manajan Filin Jirgin Sama na Janar Tunde Idiagbon, Mista Suraju Aderibigbe, ya bayyana cewa za a sabunta tsohon ginin tashar zuwa sabuwar cibiyar jigilar kaya mai amfani da fasahohi na zamani domin tabbatar da tsaro wajen sarrafa nau’ukan kayayyaki daban-daban.
Ya tabbatar da cewa wannan gyara zai ƙara bunƙasa kasuwanci, samar da ayyukan yi, da kuma ci gaban tattalin arziki a fannoni da dama a jihar.
Ali Muhammad Rabi’u
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Filin Jiragen Sama Kwara da kayayyaki
এছাড়াও পড়ুন:
Faduwar Darajar Kuɗi Na Kara Tsananta Kalubale Ga Kotunan Shari’a — CJN
Babbar Mai Shari’ar ta kasa , Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta jaddada cewa alkalai suna da nauyin tabbatar da adalci cikin gaskiya da daidaito a lokacin da matsalolin tattalin arziki ke kara tsananta wa al’umma.
Ta bayyana haka ne a Taron Alkalai na Shekara-shekara Karo na 26, wanda Cibiyar Nazarin Shari’ar Musulunci ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta shirya tare da haɗin gwiwar Cibiyar Koyar da Ayyukan Shari’a ta Kasa (NJI), a harabar Jami’ar da ke Kongo, Zariya.
Mai Shari’a Kekere-Ekun, wadda Sakatare na NJI, Barista Abdulazeez Aluwo ya wakilta, ta ce dole ne kotuna su yi hukunci da ke la’akari da yanayin tattalin arziki da kuma hakkokin masu nema da wadanda ake binsu hukunci.
Ta ce hakan ne kadai zai tabbatar da zaman lafiya da daidaiton al’umma.
Barista Abdulazeez Aluwo
CJN ta yi nuni da cewa rikice-rikicen harkokin kuɗi na zamani kamar hauhawar farashi da faduwar darajar naira, da canjin musayar kuɗi suna buƙatar tsantsar fassarar hukunce-hukuncen Shari’a bisa ilimi na zamani.
Ta yi kira da a kafa Kwamitin Tuntuba da zai kunshi Alkalai na kotu daukaka kara da Khadi da Manyan malamai na Shari’a da Kwararru a fannin kuɗi na zamani.
A cewarta, wannan kwamiti zai taimaka wajen ba kotuna jagoranci kan sabbin al’amuran da ke tasowa, tare da wayar da kan jama’a a kan dokokin kuɗin Shari’a.
Tun da farko, Daraktan Cibiyar Nazarin Shari’ar Musulunci, Dakta. Sa’ad Abubakar, ya ce faduwar darajar kuɗi da hauhawar farashi suna barazana ga mu’amalar kasuwanci da aiwatar da shari’a.
Ya ce wannan al’amari na kara jefa kotunan Shari’a cikin matsaloli, musamman wajen tabbatar da adalci kan batutuwa masu alaƙa da mu’amaloli.
A sakonsa Mai martaba, Sarkin Zazzau, Mal. Ahmed Nuhu Bamalli wanda Wazirin Zazzau Khadi Muhammad Inuwa Aminu ya wakilta, ya bukaci a hanzarta gyare-gyare a fannin Shari’a, musamman saboda yadda matsalar tattalin arziki ke shafar shari’o’in hul’i, da sadaki da dai sauransu.
Ana Shi bangare, Shugaban NJI, Mai Shari’a Babatunde Adejumo wanda Barista Zainab Salim ta wakilta ya yabawa sabon MOU da aka kulla tsakaninsu da ABU a fannin horaswa da bincike, da jagoranci da kuma inganta cancanta.
Ya ce taken taron na bana ya dace matuka, domin ya shafi manyan hakkoki na Shari’a kamar bashi da gado da sadaki, da mu’amaloli na yau da kullum.
Da yake Jawabi, Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Adamu Ahmad, Wanda Mataimakinsa a fannin Sha’anin Mulki Farfesa Suleiman Sabo ya wakilta ya ce taron alkalai na shekara–shekara muhimmin mataki ne da ke zurfafa tattaunawar shari’a da bunkasa bincike a fannin Shari’a a Najeriya.
A jawabinsa, tsohon Daraktan Cibiyar, Farfesa Muhammad Bello Usman, ya jaddada cewa adalci ba zai samu ba sai an dora nauyi da alhaki a kan mutanen da suka cancanta da kwarewa.
Taken Taron Shi ne : Shari’a a Yanayin Tattalin Arzikin Zamani: Tasirin Darajar Kuɗi da Canjin Musayar Kuɗi a Kan dokokin Shari’a.
Daga Ibrahim Suleiman