Amurka Ta Kakabawa Jami’an Gwamnatin Falasdinawa Takunkuman Hana Shiga Amurka
Published: 31st, July 2025 GMT
Gwamnatin Amurka ta bada sanarwan kakabawa gwamnatin jeka na yi ka ta Falasdinawa takunkuman hadawa jami’anta visar shiga kasar a safiyar yau Alhamis.
Shafin yanar gizo na labarai ‘abrabNews’ na kasar Saudiya ya bayyana cewa majiyar fadar white House ta bayyana cewa gwamnatin Palasdinawa musamman Mahmood Abbas suna zagon kasa ga kokarin da kasar Amurka ta ke yi don samar da zaman lafiya a Gaza.
Labarin ya kara da cewa gwamnatin Falasdinawa tana mu’amala da wasu kasashen wai don amincewa da samuwar kasar Falasdinu a cikin watan satumba mai zuwa a MDD.
A yau Alhamis ne wakilin Amurka na musamman a gabas ta tsakiya Steve Witkoff
Yake isa HKI don tattauna da gwamnatin saboda rage matsin lambar da wa HK kan kissan falasdinawa da yunwa da take a gaza.
Kasashe da dama a turai da wasu wurare sun ce zasu, ko kuma suna tunanin amincewa da kasar Falasdinu a babban taron MDD da za’a gudanar a cikin watan satumba mai suwa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu July 31, 2025 Kananan Yan Wasan Dabben Gargajiya Na Iran Sun Zama Zakara A Gasar Wannan Shekara July 31, 2025 Canada Zata Amince Da Samuwar Kasar Falasdinu A Taron MDD July 31, 2025 Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI July 31, 2025 Sojojin Mamaya Suna Ci Gaba Da Kisan Kiyashi A Gaza July 31, 2025 Kassim: Duk Wanda Yake Neman Hizbullah Ta Ajiye Makamanta Yana Yi Wa Isra’ila Aiki July 31, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Mata July 31, 2025 Tawagar Iran Ta Fice A Taron Majalisun Dokokin Kasashen Duniya A Lokacin Jawabin Wakilin Isra’ila July 31, 2025 Kasar Iran Ta Bayyana Gushewar Hasashen Raunin Karfin Sojinta Kuma Ba Zai Dawo Ba July 31, 2025 Sojan Amurka Ya Bada Ruwayar Yadda Sojojin Sahayoniyya Suka Kashe Wani Yaro Balasdine July 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Haaretz: Sojojin Isra’ila 7 ne suka kashe kansu a watan Yuli
Gidan rediyon sojojin Isra’ila ya bayar da rahoto a wannan Alhamis cewa, wani soja ya kashe kansa bayan ya kwashe fiye da kwanaki 300 a cikin sojojin wucin gadi.
Jaridar Haaretz ta Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, adadin sojojin da suka kashe kansu a wannan watan kadai ya kai bakwai.
A cikin wannan yanayi, wani bincike na Isra’ila ya nuni da karuwar masu kasha kansu a tsakanin sojojin Isra’ila tun daga lokacin fara yakin zirin Gaza. Bincike na hadin gwiwa da jami’ar Tel Aviv da sojoji suka gudanar ya nuna cewa kashi 12% na sojoji suna fama da matsalar damuwa da kunci.
Adadin wadanda suka kashe kansu tun daga watan Oktoban 2023 ya haura sojoji 43, ya zuwa ranar da aka fitar da binciken a ranar 16 ga watan Yuli, wanda ke nuna munanan yanayin da suke sakamakon ayyukan kisan kare dangi da suke kan mata da kananan yara da sauran fararen hula a Gaza.
Wani Shafin yanar gizo na Isra’ila ya bayyana cewa, asarar sojojin da Isra’ila ke yi bai takaita ga wadanda aka kashe a wurin yaki ba, hakan ya hada har ma da sojojin da suke kashe kansu saboda damuwa, da kuma masu mutuwa sakamakon raunuka da suka samu.
Bayanai sun nuna cewa sojoji 15,000 ake kula da su sakamakon matsalolin ad suka samu a wajen yaki, kashi 35% daga cikinsu suna fama da matsaloli na kunci da damuwa ko kuma tabuwa ta hankali.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: Mutane Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Wasu Kuma Sun Jikkata August 1, 2025 Kungiyar AU Ta Yi Watsi Da Kafa Gwamnatin Adawa Da Kungiyar RSF Ta Yi A Sudan August 1, 2025 Shugaban Kasar Iran Zai Ziyarci Pakistan A Gobe Asabar August 1, 2025 Habasha Ta Kaddamar Da Shirin Shuka Bishiyoyi Miliyan 700 A Rana Daya August 1, 2025 Sayyid Abdulmalik Husi: Taimakon Da Ake Jefawa Gaza Ta Sama Yaudara Ce August 1, 2025 Amurka Ta Kakabawa Jami’an Gwamnatin Falasdinawa Takunkuman Hana Shiga Amurka July 31, 2025 Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu July 31, 2025 Kananan Yan Wasan Dabben Gargajiya Na Iran Sun Zama Zakara A Gasar Wannan Shekara July 31, 2025 Canada Zata Amince Da Samuwar Kasar Falasdinu A Taron MDD July 31, 2025 Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI July 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci