Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
Published: 31st, July 2025 GMT
Sama da mutum 5,000 ne suka tsere daga gidajensu a Jihar Katsina, sakamakon sabbin hare-haren da ’yan bindiga suka kai a Ƙananan Hukumomin Bakori da Faskari.
Mutane daga ƙauyuka sama da 10 sun nemi mafaka a garin Bakori, inda da dama ke zaune wajen ’yan uwansu, yayin da wasu ke kwana a waje ba tare da masauki ko abinci ba.
Wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun bayyana cewa, maharan sukan shiga ƙauyuka da yawa, inda suka dinga harbi, ƙone gidaje, sannan suka sace mutane ciki har da mata da ƙananan yara.
Hare-haren sun fi muni a auyuka irin su Guga, Anguwar Danmarka, Gidan Sule, da sauransu.
Wani dattijo mai shekara’u 68 daga ƙauyen Doma ya ce sama da mutum 250 aka kashe a yankinsa cikin shekaru biyar da suka wuce.
Ya ƙara da cewa ’yan bindigar sukan ƙone rumbunan abinci tare da sace dabbobi.
Wata mata da ta kuɓuta daga harin a Anguwar Galadima ta ce iyalinta su 17 sun tsere, inda ta ce an sace sama da mutum 20 a ƙauyen nasu.
Wani saurayi daga Anguwar Dan Marka ya bayyana yadda aka harbe shi sau biyu a ƙafa, kuma yanzu yana amfani da sanda wajen yin tafiya.
Wasu da dama har yanzu suna hannun maharan, yayin da suke neman fansar Naira miliyan 1.5 kan kowane mutum ɗaya.
Manoma ma na kuka da halin da suka tsinci kansu sakamakon hare-haren.
A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, wani manomi daga Ƙaramar Hukumar Sabuwa ya koka da yadda aka lalata gonarsa.
Amma a martanin da suka bayar, shugabannin Ƙaramar Hukumar sun ce an lalata gonakin da ke kusa da manyan tituna ne domin hana ’yan bindiga amfani da su wajen ɓuya da kuma kai wa matafiya hari.
Amma manoman suna kallon wannan a matsayin wata matsala a gare su.
Shugabannin ƙauyuka da hukumomin gwamnati sun tabbatar da cewa mutane suna ƙara zuwa Bakori kowace rana don neman mafaka.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Bakori, ya ce akwai sama da mutum 3,500 da ke zaune a Bakori, yayin da wasu sama da 2,000 ke zaune a ƙauyen Guga.
An fara raba wa waɗanda suka rasa matsugunansu abinci da kayan masarufi, amma ana buƙatar samum ƙarin taimako.
Ƙungiya ta buƙaci a ayyana dokar ta-ɓaci a BakoriAn buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta jiha da kuma ƙungiyoyin agaji su kai wa waɗanda lamarin ya shafa ɗauki cikin gaggawa.
Wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna ‘Grassroots Advocates for Peace’ ta nemi Gwamnatin Tarayya ta ayyana Bakori a matsayin yanki mai hatsari.
Sun buƙaci ƙarin jami’an tsaro, da ɗaukar mataki cikin gaggawa.
Sun kuma buƙaci a kula da lafiyar kwakwalwar waɗanda suka kuɓuta daga hare-haren da kuma hukunta masu kai hare-haren.
Gwamnatin Katsina na ƙoƙarin magance matsalarA nata ɓangaren, Gwamnatin Jihar Katsina, ta ce tana ƙoƙarin wajen magance matsalar.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar, Nasir Muazu, ya ce suna ƙoƙarin magance matsalolin da Ƙaramar Hukumar ke fama da su.
Ya ce akwai wasu mutane da ke ƙoƙarin yada ƙarya a kafafen sada zumunta don haifar da tsoro da ruɗani a zukatan jama’a.
Ya kuma ce an samu sauƙin kai hare-hare a wasu yankuna kamar Jibia da Batsari.
Kwamishinan, ya bayyana cewa an kafa rundunar ‘Katsina Community Watch Corps’ domin taimaka wa sojoji, ’yan sanda da ’yan sa-kai wajen shiga dazuka da ke da wuyar shiga.
Sai dai ya buƙaci jama’a da su ci gaba da jajircewa da kuma bayar da rahoton duk wani abu da su yarda da shi ba.
An samu sauƙin kai hare-hare cikin shekara 2 — RibaduA yayin da gwamnati ke cewa ana samun ci gaba, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce Najeriya ta fi samun zaman lafiya a yanzu sama da shekaru biyu da suka wuce.
Ya ce an ceto da mutum sama da 11,000 da aka sace, kuma an kashe wasu daga cikin manyan shugabannin ’yan bindiga.
Ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, bisa jagoranci da tsare-tsaren tsaro da suka haifar da wannan sauyi.
Sai dai waɗanda ke zaune a matsuguni na wucin gadi a Bakori da wasu yankuna, rayuwa cikin tsaka mai wuya.
Wasu sun ce har yanzu ba su da ƙwarin gwiwar komawa gidajensu.
Sun tabbatar da cewar sai gwamnati ta samar da tsaro mai ɗorewa, sannan za su koma muhallansu, saɓanin haka za su ci gaba da zama a inda suke a yanzu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Batsari Ɗauki Gwamnatin Katsina Gwamnatin tarayya hare hare Tsaro Ƙaramar Hukumar yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI
Shugaban kasar Lebanon wanda ya gabatar da jawabi da safiyar yau ya ce; A cikin sakwannin da mu ka aike wa Amurka, mun bukaci ganin an kawo karshen hare-haren da Isra’ila take ci gaba da kawo wa Lebanon, ta sama, kasa da ruwa, haka nan kuma kisan gillar da take yi wa mutane a cikin kasar.”
Shugaba Aun ya kuma yi jinjina ga dukkanin shahidan kasar da su ka kwanta dama saboda kare Lebanon,kuma yana a matsayin wani abu ne mai kima da daraja a wurinmu.”
Shugaba Aun na Lebanon ya kuma ce, Isra’ila abokiyar gaba ce wacce take hana mutanen da yaki ya tarwatsa komawa zuwa garuruwansu da kuma sake gina kudancin Lebanon da yaki ya rusa.”
Haka nan kuma ya ce , sojojin Lebanon sun sadaukar da kawukansu ta hanyar kasancewa a tare da mutanen kudancin Lebanon.
Danagen da makaman Hizbullah, Shugaban kasar ya ce nauyi ne da ya rataya a wuyansa da kuma dukkanin ‘yan siyasa da su ga cewa makamai suna hannun gwamnati ne kadai, a hannun soja da jami’an tsaro.”
Har ila yau ya kara da cewa, yanayin da ake ciki baya da bukatuwa da duk wani abu da zai zama tsokana da tayar da hankali, ba kuma za su bari ‘yan ta’adda su cutar da al’umar Lebanon ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Mamaya Suna Ci Gaba Da Kisan Kiyashi A Gaza July 31, 2025 Kassim: Duk Wanda Yake Neman Hizbullah Ta Ajiye Makamanta Yana Yi Wa Isra’ila Aiki July 31, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Mata July 31, 2025 Tawagar Iran Ta Fice A Taron Majalisun Dokokin Kasashen Duniya A Lokacin Jawabin Wakilin Isra’ila July 31, 2025 Kasar Iran Ta Bayyana Gushewar Hasashen Raunin Karfin Sojinta Kuma Ba Zai Dawo Ba July 31, 2025 Sojan Amurka Ya Bada Ruwayar Yadda Sojojin Sahayoniyya Suka Kashe Wani Yaro Balasdine July 31, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku July 31, 2025 Qolibaf: Barin HKI Ta Yi Abinda Taga Dama Ne Yana Karfafa Mata Giwa July 30, 2025 Yunwa Ta Kashe Karin Falasdinawa 7 A Gaza July 30, 2025 Malta Zata Amince da Samuwar Falasdinu a Cikin Watan Satumba Mai Zuwa July 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci