Peter Obi zai lashe jihohin Arewa idan ya koma PDP – Jerry Gana
Published: 31st, July 2025 GMT
Ɗaya daga cikin jigo da suka kafa Jam’iyyar PDP, Farfesa Jerry Gana ya yi iƙirarin cewa tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi zai kayar da duk wani ɗan takara a jihohin Arewacin Najeriya idan ya tsaya takara a PDP.
Da yake bayabni a tashar talabijin ta Arise TV a ranar Laraba, Gana ya ce, “Ni mai nazari ne, kuma ina nazarin ra’ayoyi, a jihohin Arewa Peter Obi a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP zai doke duk wani ɗan takara, saboda mutanenmu suna da gaskiya.
Peter Obi ya fice daga Jam’iyyar PDP a watan Mayun 2022 inda ya jagoranci Jam’iyyar LP a zaɓen 2023.
Da yake waiwayen tushen PDP, jigon na PDP ya tunatar da ’yan Najeriya irin ƙarfin da jam’iyyar ke da shi da kuma rawar da take takawa wajen maido da mulkin dimokraɗiyya.
Ya ce, “Dole ne in shaida cewa mutane da yawa sun manta cewa an kafa Jam’iyyar PDP ne a matsayin ƙungiya mai zaman kanta, a shekarar 1998 aka kafa mu, sannan muka shiga zaɓe a 1999, muna cikin kowace rumfar zaɓe, domin mu ne muka ci zaɓen farko.
“Mutane da yawa sun manta cewa PDP ce ta lashe mafi yawan ƙananan hukumomi, lokacin da aka zo batun zaɓen shugaban ƙasa, mun ci zaɓen shugaban ƙasa, mun ci na majalisar dattawa, muka ci majalisar tarayya, mu ne ke riƙe da madafun iko, shi ya sa muka yi matuƙar farin ciki da cewa mun maido da dimokuraɗiyya a Najeriya, muka sake kafa mulkin farar hula.
“Saboda shekaru da dama ana mulkin soja, amma mun samu nasarar kawo ƙarshen hakan ta hanyar dimokuraɗiyya, don haka PDP ta kasance jam’iyyar talakawa ce, shi ya sa idan muka ce mulki ga jama’a, muna nufin hakan ne saboda abin ya kasance, kuma ya kasance haka.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Farfesa Jerry Gana Jam iyyar PDP
এছাড়াও পড়ুন:
Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala
Da yake mayar da martani ga wannan zargin na Amurka, Bwala ya ce gwamnatin Tinubu tana jajircewa wajen kare dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ba, yana mai cewa Amurka da Nijeriya sun dade suna hadin gwiwa a yaki da ta’addanci.
“Shugaba Bola Tinubu da Shugaba Donald Trump suna da kudiri iri ɗaya a yaƙi da ta’addanci da duk wani nau’in ta’addanci a kan bil’adama,” in ji Bwala.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA