Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI
Published: 31st, July 2025 GMT
Shugaban kasar Lebanon wanda ya gabatar da jawabi da safiyar yau ya ce; A cikin sakwannin da mu ka aike wa Amurka, mun bukaci ganin an kawo karshen hare-haren da Isra’ila take ci gaba da kawo wa Lebanon, ta sama, kasa da ruwa, haka nan kuma kisan gillar da take yi wa mutane a cikin kasar.”
Shugaba Aun ya kuma yi jinjina ga dukkanin shahidan kasar da su ka kwanta dama saboda kare Lebanon,kuma yana a matsayin wani abu ne mai kima da daraja a wurinmu.
Shugaba Aun na Lebanon ya kuma ce, Isra’ila abokiyar gaba ce wacce take hana mutanen da yaki ya tarwatsa komawa zuwa garuruwansu da kuma sake gina kudancin Lebanon da yaki ya rusa.”
Haka nan kuma ya ce , sojojin Lebanon sun sadaukar da kawukansu ta hanyar kasancewa a tare da mutanen kudancin Lebanon.
Danagen da makaman Hizbullah, Shugaban kasar ya ce nauyi ne da ya rataya a wuyansa da kuma dukkanin ‘yan siyasa da su ga cewa makamai suna hannun gwamnati ne kadai, a hannun soja da jami’an tsaro.”
Har ila yau ya kara da cewa, yanayin da ake ciki baya da bukatuwa da duk wani abu da zai zama tsokana da tayar da hankali, ba kuma za su bari ‘yan ta’adda su cutar da al’umar Lebanon ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Mamaya Suna Ci Gaba Da Kisan Kiyashi A Gaza July 31, 2025 Kassim: Duk Wanda Yake Neman Hizbullah Ta Ajiye Makamanta Yana Yi Wa Isra’ila Aiki July 31, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Mata July 31, 2025 Tawagar Iran Ta Fice A Taron Majalisun Dokokin Kasashen Duniya A Lokacin Jawabin Wakilin Isra’ila July 31, 2025 Kasar Iran Ta Bayyana Gushewar Hasashen Raunin Karfin Sojinta Kuma Ba Zai Dawo Ba July 31, 2025 Sojan Amurka Ya Bada Ruwayar Yadda Sojojin Sahayoniyya Suka Kashe Wani Yaro Balasdine July 31, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku July 31, 2025 Qolibaf: Barin HKI Ta Yi Abinda Taga Dama Ne Yana Karfafa Mata Giwa July 30, 2025 Yunwa Ta Kashe Karin Falasdinawa 7 A Gaza July 30, 2025 Malta Zata Amince da Samuwar Falasdinu a Cikin Watan Satumba Mai Zuwa July 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Iran Ta Bayyana Gushewar Hasashen Raunin Karfin Sojinta Kuma Ba Zai Dawo Ba
Kakakin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran “IRGC” ya bayyana cewa: Hasashen Raunin Iran ya gushe, kuma ba zai sake dawowa ba
Kakakin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Mohammad Na’eini ya jaddada cewa: Ra’ayin cewa Iran mai rauni ce ya raguje kwata-kwata, yana mai jaddada cewa; Yakin kwanaki 12 na baya-bayan nan ya fallasa gazawar makiya wajen karya manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, sannan kuma ya nuna cewa duk wani sabon harin wuce gona da iri zai fuskanci martani mai tsanani da gauni da zai wurga makiya cikin mummunar nadama.
Hakan ya zo ne a jawabin da Birgediya Janar Na’eini ya gabatar a jiya Laraba a wajen bikin tunawa da shahidi Ramadan Ali Jobadari da shahidan yakin baya-bayan nan. Ya kara da cewa: “Babban bangare na yakin kwanaki goma sha biyu ya kasance yakin kafar watsa labarai da na kwakwalwa da kuma fahimtar hakikanin juna,” ya kara da cewa, “Sun samu gagarumar nasara a fagen yada labarai a lokacin yakin da aka yi a baya-bayan nan. Da kafofin watsa labaru ba su da tasiri, da makiya ba su kai hari kan kafofin watsa labaru da ‘yan jarida ba.
Ya bayyana cewa, “a cikin wannan yakin, makiya sun kai hare-hare kan manyan cibiyoyin kasa da suka hada da cibiyoyin kimiyya da na masana, kwamandojin soji, hedkwatar gudanarwa, cibiyoyin leken asiri da tsaro, da kuma kafofin watsa labarai a matsayin cibiyar tsara labarin.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojan Amurka Ya Bada Ruwayar Yadda Sojojin Sahayoniyya Suka Kashe Wani Yaro Balasdine July 31, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku July 31, 2025 Qolibaf: Barin HKI Ta Yi Abinda Taga Dama Ne Yana Karfafa Mata Giwa July 30, 2025 Yunwa Ta Kashe Karin Falasdinawa 7 A Gaza July 30, 2025 Malta Zata Amince da Samuwar Falasdinu a Cikin Watan Satumba Mai Zuwa July 30, 2025 Amurka Ta Ce HKI Ba Zata Fice Daga Kasar Lebanon Ba Sai An Kwance Damarar Hizbullah July 30, 2025 Siriya Da HKI Zasu Gudanar Da Taro A Baku July 30, 2025 Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Kada Yankin Kamtashatka Na Kasar Rasha July 30, 2025 Yahudawa ‘Yan Share Wuri Zauna Sun Kutsa Cikin Masallacin Kudus July 30, 2025 Kasashen Yankin Caribbean Suna Son Bunkasa Alakarsu Ta Kasuwanci Da Nahiyar Afirka July 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci