Man Utd Na Tattaunawa Da Golan PSG, Chelsea Ta Nace Wa Garnacho
Published: 31st, July 2025 GMT
Manchester United ta soma tattaunawa da Paris St-Germain kan golan Italiya Gianluigi Donnarumma, mai shekara 26, amma Chelsea da Manchester City na cikin masu sha’awar golan. (Telegraph – subscription required, external)
Yayin da ɗanwasan gaba na Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, ya amince ya koma Liverpool, Newcastle ta saka ɗanwasan Brazil Rodrigo Muniz, mai shekara 24 cikin lissafinta.
Crystal Palace ta sanar da Arsenal cewa sai ta fara biya aƙalla fam miliyan 35 kafin ta ɗauko Eberechi Eze, daga baya ta cike sauran kuɗin. (Guardian, external)
Palace a shirye take ta biya fam miliyan 27.6 domin ɗauko ɗanwasan baya na Jamus Yann Bisseck, mai shekara 24 daga Inter Milan domin maye gurbin Marc Guehi, da ake alaƙantawa da Liverpool. (Gazzetta dello Sport – in Italian, external)
Chelsea na ci gaba da matsi kan Alejandro Garnacho amma Manchester United na son ta biya ta fam miliyan 40 kan ɗanwasan gaban na Argentina. (Talksport, external)
Lyon ta cimma matsaya tsakaninta da ɗanwasan tsakiya na Liverpool da Ingila Tyler Morton, mai shekara 22, amma kudin da Liverpool ta nema zai iya kawo cikas ga yarjejeniyar. (L’Equipe – in French, external)
AS Roma na nazarin ɗauko ɗanwasan gaba na Wolves Portugal Fabio Silva, mai shekara 23, yayin da kuma take da sha’awar ɗanwasan Argentina da Manchester City mai shekara 19 Claudio Echeverri. (Sky Sports, external)
Matashin ɗanwasan Ingila mai shekara 19 Leo Castledine na shirin zuwa Huddersfield Town a matsayin aro daga Chelsea. (Athletic – subscription required, external)
Ɗanwasan baya na Ingila Rob Holding, mai shekara 29, na shirin barin Crystal Palace domin komawa ƙungiyar Amurka ta Colorado Rapids. (Sky Sports, external)
Middlesbrough ta amince da tayin fam miliyan 20 da Ipswich ta yi kan ɗanwasan Ingila Hayden Hackney, mai shekara 23. (Northern Echo)
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Wasani fam miliyan mai shekara
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
An gudanar da taron tattaunawa na duniya kan kirkire-kirkire da bude kofa da ci gaba na bai daya, jiya Juma’a a birnin Lagos na Nijeriya. Yayin taron wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG da karamin ofishin jakadancin Sin dake Lagos suka shirya, ministan kula da harkokin matasa na Nijeriya Ayodele Olawande da shugaban CMG Shen Haixiong, sun gabatar da jawabai ta kafar bidiyo.
A cewar ministan na Nijeriya, cikin shekaru 5 da suka gabata, dubban matasan kasar sun ci gajiyar tallafin karatu da shirye-shiryen horo da na musaya da Sin ta samar, kuma wannan hadin gwiwa da ake yi a aikace ya kara fahimta da aminci tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewa, a shirye ma’aikatarsa take ta karfafa hadin gwiwa da sassa masu ruwa da tsaki na kasar Sin wajen ci gaba da fadada shirye-shiryen musaya da na hadin gwiwa da suka shafi matasa.
A nasa bangare, Shen Haixiong ya ce a matsayinta na babbar kafar yada labarai dake watsa shirye shiryenta ga sassa daban daban na duniya, tashar talabijin ta CCTV dake karkashin CMG da abokan huldarta, za su yayata shawarar Sin ta jagorantar harkokin duniya da gabatar da tafarkin Sin na zamanantar da kanta da karfinta na kirkire kirkire a sabon zamani ga al’ummar duniya. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA