Ganawar da shugaba Trump ya yi a baya-bayan nan da shugabannin wasu kasashe biyar dake nahiyar Afirka, ita ma ta janyo hankalin al’ummun duniya. Inda shugaba Trump ya yabawa shugaban kasar Laberiya Joseph Boakai kan yadda ya iya Turancin Ingilishi sosai, lamarin da ya bayyana rashin fahimtarsa kan alakar tarihi tsakanin kasar Laberiya da Amurka.

Bugu da kari, Trump ya katse maganar shugaban kasar Mauritaniya Mohammed Ghazouani, inda ya nemi ya yi magana da sauri. A hakika, rashin mutuntawa da shugaba Trump ya nuna a fili, ta bayyana ainihin dalilin da ya sa aka gayyaci shugabannin Afirka biyar zuwa wajen ganawar—ba domin neman karfafa dangantaka ba ne, sai dai don tabbatar wa Amurka din damar samun ma’adanan da take bukata, da yiwuwar sanya wadannan kasashen dake nahiyar Afirka amincewa da karbar bakin haure da ake korarsu daga Amurka.

Watakila, shugaba Trump ba ya mai da hankali sosai kan da’a a fannin diflomasiyya, amma idan aka kwatanta da shugabannin kasar Amurka da suka gabace shi, to, a kalla yana bayyana kome a fili ba tare da rufa-rufa ba. Maganarsa da matakan da ya dauka, dukkansu na isar da sako zuwa ga kasashen Afirka cewa: “Ba ku cikin jerin fannonin da Amurka take nunawa fifiko.” “Za mu iya musayar wasu abubuwa, amma kada ku yi tsammanin za ku samu riba ko alfanu sosai.” (Bello Wang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Ta Dade Tana Aiki Tukuru Kan Kiyaye Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali Na Yanki

Dangane da tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka da aka gudanar a kwanan nan, Guo Jiakun ya bayyana cewa, ana fatan bangaren Amurka zai yi aiki tare da Sin wajen amfani da tsarin tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, don sa kaimi ga bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka cikin kwanciyar hankali.

Dangane da batun Falasdinu kuwa, Guo Jiakun ya ce, “manufar kafa kasashe biyu” ita ce hanya daya tilo ta hakika ta warware matsalar Falasdinu, kuma kasar Sin tana goyon bayan al’ummar Falasdinu wajen kafa kasa mai cin gashin kanta.(Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan kauce wa tasirin harajin Amurka
  • Peter Obi zai lashe jihohin Arewa idan ya koma PDP – Jerry Gana
  •  Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa  Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI
  • Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata Za Ta Fara Daukar Bayanai Ta Yanar Gizo
  • Kasar Iran Ta Bayyana Gushewar Hasashen Raunin Karfin Sojinta Kuma Ba Zai Dawo Ba
  • Sin Ta Dade Tana Aiki Tukuru Kan Kiyaye Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali Na Yanki
  • Amurka Ta Ce HKI Ba Zata Fice Daga Kasar Lebanon Ba Sai An Kwance Damarar Hizbullah
  • Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
  • Shugaban Kasar Ivory Coast Ya Bayyana Shirinsa Na Sake Tsayawa Takarar Shugabanci Karo Na Hudu