Malta Zata Amince da Samuwar Falasdinu a Cikin Watan Satumba Mai Zuwa
Published: 30th, July 2025 GMT
Firay ministan kasar Malta Robert Abela ya bayyana cewa gwamnatinsa zata shelanta amincewa da kasar Falasdinu mai zaman kanta a taron shuwagabannin kasashen duniya a cikin watan satumban mai zuwa.
Robert Abela ya bayyana haka ne a shafinsa na yanar gizo, ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Malta tana bukatar a samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.
Ya ce: kasar Malta tana bukatar samar da kasashen biyu\ masu zaman kansu a kasar Falasdinu da aka mamaye, sannan a halin yanzu hatta jam’iyyun adawa na kasar malta sun bayyana bukatar yin nhakan.
Firay ministan ya bada wannan sanarwan ne bayan da tokwaransa na kasar Burtaniya Keir Starmer ya bada sanarwan mai kama da tashi, na cewa idan halin da ake ciki a gaza ya ci gaba har zuwa watan satumba mai zuwa to gwamnatin kasar zata shelanta amincea da kasar Falasdinu mai zaman kanta.
Kafin haka gwamnatin kasar Faransa ta bada sanarwa amincewa da kasar falasdinu mai zaman kanta. Babban sakataren kungiyar kasashen musulmi Hussain Ibrahim Taha yay aba da matsayin da gwamnatin kasar Burtaniya ta dauka kan matsalar al-ummar Falasdinu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Ta Ce HKI Ba Zata Fice Daga Kasar Lebanon Ba Sai An Kwance Damarar Hizbullah July 30, 2025 Siriya Da HKI Zasu Gudanar Da Taro A Baku July 30, 2025 Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Kada Yankin Kamtashatka Na Kasar Rasha July 30, 2025 Yahudawa ‘Yan Share Wuri Zauna Sun Kutsa Cikin Masallacin Kudus July 30, 2025 Kasashen Yankin Caribbean Suna Son Bunkasa Alakarsu Ta Kasuwanci Da Nahiyar Afirka July 30, 2025 Shugaban Kasar Ivory Coast Ya Bayyana Shirinsa Na Sake Tsayawa Takarar Shugabanci Karo Na Hudu July 30, 2025 Kasashen Iran Da Rasha Sun Tattauna Batun Hadin Gwiwar Kafofin Watsa Labarai A Tsakaninsu July 30, 2025 MDD Zata Aiwatar Da Hanyar Warware Rikicin Falasdinawa Da Yahudawan Sahayoniyya July 30, 2025 Birtaniya Ta Yi Barazanar Amincewa Da Kasar Falasdinu A Watan Satumba Idan Yanayin Gaza Bai Canza Ba July 30, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Lod Da Ke Jaffa Da Makami Mai Linzami July 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da kasar Falasdinu a kasar Falasdinu gwamnatin kasar kasar Malta
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da cewa daga lokacin da aka tsayar da wuta zuwa yanzu adadin Falasdinawan da HKI ta kashe sun kai 200, yayin da wasu kusan 600 sun jikkata.
Sanarwar ta ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta kuma ci gaba da cewa; A cikin sa’o’i 48 da su ka gabata,an sami shahidai 22, biyar daga cikinsu basu dade da yin shahada ba, sai kuma 17 da aka tono su daga karkashin baraguzai. Haka nan kuma na kai wasu 9 zuwa asibitocin da suke a yankin.
Wani sashe na sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ya ce, har yanzu da akwai shahdai masu yawa da suke a karkashin baraguzai, wasu kuma a kan hanyoyi, saboda rashin kayan aiki da kungiyoyin agaji za su yi amfani da su.
Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu, adadin shahidai ya kai 68,858, sai kuma wani adadin da ya kai 170,664 da su ka jikkata.
Amma daga tsayar da wuta a ranar 11 ga watan Oktoba zuwa yanzu, an sami shahidai da sun kai 226, sai kuma wasu 594 da su ka jikkata. Haka nan kuma an iya tsamo gawawwakin shahidai daga cikin baraguzai har su 499.
Haka nan kuma ma’aikatar kiwon lafiyar tra sanar da karbar gawawwaki 30 da HKI ta mika wa bangaren Falasdinawa ta hannun hukumar agaji ta “Red-Corss.
Tun bayan tsagaita wutar yaki, har ya zuwa yanzu dai HKI tana ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci