Yadda Yajin Aikin Ma’aikatan Jinya Ya Bar Baya Da Kura A Asibitocin Jihar Filato
Published: 1st, August 2025 GMT
Yayin da yajin aikin gargadi na kasa baki daya da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) ta kira ya shiga rana ta biyu, iyalai sun fara kwashe ‘yan uwansu daga asibitocin gwamnati zuwa masu zaman kansu a jihar Filato. A Asibitin Kwararru na Jihar Filato, dogon layin masu amsar katin asibiti don neman kulawa da lafiyarsu ya yi batan dabo a lokacin da wakilinmu ya ziyarci asibitin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ma aikatan jinya
এছাড়াও পড়ুন:
An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
“Haka kuma an kama wata mata mai shekaru 34 da ake zargi da hannu a lamarin, tare da wasu masu gidan marayu guda biyu da ke Abuja da Jihar Nasarawa, inda aka gano wasu yaran da ake kyautata zaton an yi safarar su. Wasu daga cikin gidajen marayun da aka gano ana amfani da su ne a matsayin cibiyoyin ajiye yara, inda ake jiran ‘kwace’ ko sayar da su da sunan daukar nauyin marayu.”
Ya ce, “An gano gidajen marayu guda hudu da ke Kaigini, Kubwa Edpressway Abuja; Masaka Area 1, Mararaba kusa da Abaca Road; da kuma Mararaba bayan Kasuwar Duniya suna da alaka da wannan kungiya, kuma ana ci gaba da bincike a kansu.”
Ya kara da cewa, daya daga cikin masu korafin ya bayyana cewa ya biya Naira miliyan 2.8 a matsayin kudin daukar yaro, sannan ya biya Naira 100,000 a matsayin kudin shawara ga daya daga cikin ‘yan kungiyar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wani mai korafi ya ce shi ma ya biya Naira miliyan 2.8 kudin daukar yaro da Naira 100,000 kudin shawara ga wani dan kungiyar.
“An canza sunayen yawancin yaran da aka ceto, lamarin da ya kara wahalar da bincike da gano asalinsu,” in ji sanarwar.
Darakta Janar ta NAPTIP, Binta Adamu Bello, ta bayyana damuwarta kan wannan lamari, inda ta ce safarar yara ta zama babbar matsala a kasa.
Ta hanyar Adekoye, DG din ta nuna damuwa game da yadda wasu gidajen marayu ke amfani da raunin jama’a wajen aiwatar da safarar yara.
Ta ce, “Abin takaici ne yadda wasu masu mugunta da ke da sunayen kwararru da matsayi a cikin al’umma, suke amfani da matsayin su wajen yaudarar mutanen da ke cikin mawuyacin hali, su yi safarar ‘ya’yansu, da dama daga cikinsu ma sun tsira ne daga halaka a lokacin rikice-rikicen al’umma ko na manoma da makiyaya, sannan a sayar da su ga iyaye masu neman haihuwa a matsayin daukar yaro ba tare da sahihin izinin iyayensu ba.
“Wannan abin ba za a yarda da shi ba, kuma wadanda aka kama kan wannan mugun aiki za su fuskanci hukuncin doka yadda ya kamata.
“’Ya’yanmu ba kayayyaki ba ne da za a ajiye su a gidajen marayu a sayar ga mai biyan mafi tsada. Wannan dole ya tsaya,” in ji ta.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA