Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF
Published: 30th, July 2025 GMT
Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya sabunta hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa tun daga shekarar nan ta 2025 har zuwa 2026.
IMF ya bayyana sabon hasashen a watan Yulin da muke ciki wanda a ciki ya yi ƙiyasin samun ƙarin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya.
Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasaAsusun ya yi hasashen samun ƙarin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya da kashi 3.
Haka kuma, IMF ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai samun ƙarin bunƙasa da kashi 3.2 a 2026, saɓanin hasashen kashi 2.7 da ya yi a watan na Afrilu.
Sai dai duk da wannan, wani rahoto IMF ya fitar a watan Yunin bana, ya ce Nijeriya na mataki na 12 a cikin jerin kasashe mafiya talauci a fadin duniya.
IMF ya ce talauci na kara karuwa a cikin kasar da ta dauki shekaru biyu tana kokarin sauya fuskar tattalin arziki, amma kuma take dada fadawa cikin duhu na tattalin arziki.
A cikin kasashe 189 da aka gudanar da bincike a cikinsu, Nijeriyar na a mataki na 178, inda ta zarta kasashe irin su Yemen da Sudan ta Kudu da Kwango da Nijar da Sudan, wadanda kusan dukkaninsu ke fama da rigingimu a halin yanzu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nijeriya Tattalin Arziki tattalin arzikin Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu
Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ya fitar, ta ce a karon farko cikin shekaru da dama, daliban Nijeriya za su ci gaba da karatun tarihin Nijeriya tun daga Firamare 1 zuwa karamar Sakandare 3 yayin da daliban SSS 1 – 3 za su koyi sabon darasin da aka samar na ‘Civic and Heritage Studies’, wanda ya hada tarihin Nijeriya da Ilimin zamantakewar Jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp