Binciken CGTN: Za A Ci Gaba Da Nuna Kyakkyawan Fata Ga Bunkasar Sin Nan Da Shekaru 5
Published: 31st, July 2025 GMT
Bayanin da ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya yi a baya-bayan nan game da hasashe kan tattalin arzikin kasar Sin cikin shekaru biyar masu zuwa ya jawo hankalin duniya sosai. Kuma sakamkon binciken jin ra’ayoyin jama’a da CGTN na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya yi a tsakanin masu bayyana ra’ayoyi 47,000 a kasashe 46 daga shekarar 2023 zuwa 2025, ya nuna jama’ar sun nuna yakini game da karfi da juriyar tattalin arzikin kasar Sin.
Binciken ya nuna cewa, yawancin masu bayyana ra’ayoyin daga sassan duniya suna da kyakkyawan fata ga tattalin arzikin kasar Sin wajen samun bunkasa mai kyau a dogon lokaci, inda amincewarsu ta kai kashi 74.7 bisa dari, da 81.3 bisa dari, da kuma 81.9 bisa dari cikin shekaru uku a jere.
Binciken da aka yi a bana ya kuma nuna cewa, masu bayyana ra’ayoyin suna da kwarin gwiwa game da samun damammaki masu kyau a kasuwar Sin a cikin yanayin kasa da kasa mai sarkakiya da tashe-tashen hankula. A cikinsu akwai kashi 79.8 bisa dari da suka bayyana cewa, babbar kasuwar Sin ta ba da muhimman damammaki ga kasashen da suke gudanar da kasuwanci a ciki.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake.
A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, sassan biyu za su tattauna batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba jerin haraji daga bangare guda, da keta matakan kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp