Firaminista Mark Carney ya ce Canada ta shirya amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu a cikin watan Satumba, inda ta zamo ƙasa ta uku daga cikin ƙungiyar G7 da ta fitar da irin wannan sanarwa a cikin kwanakin nan.

Carney ya ce za su ɗauki matakin ne ta la’akari da wasu sharuɗɗan gyara daga ɓangaren hukumomin Falasɗinu da suka haɗa da amincewa da tsarin dimokuraɗiyya da kuma gudanar da zaɓe ba tare da ƙungiyar Hamas ba a shekara mai zuwa.

Sanarwar tasa na zuwa ne kwana ɗaya bayan Birtaniya ta bayyana goyon bayan ta ga kafa ƙasar Falasɗinun a watan Satumba mai zuwa, kuma mako ɗaya bayan Faransa ta yi irin wannan sanarwa.

Ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta yi watsi da sanarwar ta Canada tana mai cewa matakin tamkar jinjinawa ƙungiyar Hamas ne.

Daga cikin ƙasashe 193 na Majalisar Dinkin Duniya, 147 sun goyi bayan kafa ƙasar Falasɗinu.

Amma Mr Carney ya ce Canada za ta goyi bayan kafa ƙasar Falasɗinun ne a babban taron Majalisar Dinkin Duniya mai zuwa.

Ya kafa hujja da yadda Isra’ila ke ƙara mamaye sassan gaɓar yamma da kogin Jordan da taɓarɓarewar ayyukan jin ƙai a Gaza da kuma harin da Hamas ta kai wa Isra’ila a ranar bakwai ga watan Oktoba a matsayin dalilan da suka sa Canada ta sauya matsayarta a kan batun.

Carney ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa “Mawuyacin halin da ake ciki a Gaza na ƙara taɓarɓarewa,”

Ya ce kafa ƙasar Falasɗinu zai bai wa jagororin Falasɗinawa damar gudanar da tsare-tsaren mulki da gudanar da zaɓuka ba tare da Hamas ba a 2026 da kuma kawo ƙarshen ayyukan ƙungiyoyi masu riƙe da makamai a yankin.

Dama can Canada ta daɗe tana goyon bayan shirin kafa ƙasashe biyu masu ƴancin kansu a matsayin hanyar warware rikicin Falasɗinawa da Isra’ila.

Carney ya kuma ce ya tattauna da shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas a kan batun.

Hukumomin Falaɗinawa dai suna iko da wasu sassa na gaɓar yamma da kogin Jordan a ƙarƙashin jam’iyyar Fatah da shugaba Abbas ke jagoranta, yayin da ƙungiyar Hamas ke tafiyar da Gaza. Dukkan su ba su taɓa gudanar da zaɓe ba tun a 2006.

Firaminitan Canada ya fuskanci matsin lambar neman ya sanar da matsayar sa kan kafa ƙasar Falasɗinu tun bayan da manyan ƙawayen ƙasarsa, Birtaniya da Faransa suka sanar da goyon bayan su.

Jakadun Canada da jami’an diflomasiyyarta fiye da 200 suka sanya hannu kan wata takarda mai neman Carney ya amince da shirin

A cikin wasiƙar da suka aikewa Carney jami’an sun ce yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza ya yi hannun riga da tsarin ƙasar.

Da aka tambaye shi ko Canada ta goyi bayan kafa ƙasar Falasɗinun ne saboda Birtaniya ta janye hankalin ta, sai Mr Carney ya ce ƙasarsa ta ɗauki matakin ne ba tare da katsalandan daga wata ƙasa ba.

Carney ya jaddada cewa Canada ƙasa ce mai ƴancin kanta kuma wadda ke da ikon tsara yadda za ta yi alaƙa da ƙasashen duniya.

Da wannan mataki dai ana iya cewa Canada ta bi turbar da sauran ƙawayenta na Turai suka bi game da kafa ƙasar Falasɗinu.

Idan Birtaniya da Faransa suka jaddada goyon bayansu ga kafuwar ƙasar Falasɗinu, zai rage saura Amiurka ce kaɗai ke adawa da hakan a cikin ƙasashe mambobin dindindin a kwamitin taro na Majalisar Dinkin Duniya.

Ma’aikatar lafiya ta Hamas ta ce mutane aƙalla 60,034 aka kashe a Gaza tun bayan fara yaƙi a Gaza, kuma ta ce aƙalla 1,200 daga cikin su sun mutu ne saboda rashin abinci mai gina jiki, yayin da 89 a cikin su ƙananan yara ne.

BBC/Hausa

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: kafa ƙasar Falasɗinu Carney ya ce goyon bayan

এছাড়াও পড়ুন:

Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu

A cikin kwanakin bayan nan ana samun karuwar sojojin HKI da suke kashe kawunansu saboda tabuwar kwakwalensu sanadiyyar yakin Gaza.

Kafafen watsa labarun HKI sun kunshi rahotanni da suke bayani akan yadda sojojin mamayar da su ka yi yaki a Gaza, suke samun tabuwar hankali, da hakan yake sa su kashe kawukansu bayan sun baro Gaza.

Wasu rahotannin sun ambaci cewa, sojojin na HKI suna rayuwa ne a cikin tsaro da ranaza saboda munanan ayyukan da su ka aikata marasa kyau.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutane 44 Suka Mutu Bayan Mamakon Ruwa Da Aka Tafka A Beijing
  • Faransa Za Ta Fara Jefa Kayan Agaji Ta Sama A Gaza
  • DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure
  • Za mu halasta kafa ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ila ba ta cika wasu sharuɗa ba — Birtaniya
  • Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
  • Muddin Isra’ila ba ta cika wasu sharuɗa ba za mu amince da kafa ƙasar Falasɗinu — Birtaniya
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a Alkaleri
  • Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu
  • Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata