Kare Ya Ciji Tsohon Ɗan Wasan Barcelona A Mazakuta
Published: 31st, July 2025 GMT
Tsohon ɗan wasan tsakiyar Barcelona, Carles Perez, yana kwance a asibiti a ƙasar Girka bayan da wani kare ya cije shi a al’aurarsa yayin da yake yawo da nasa karen a Thermi, a wata unguwa a Thessaloniki, ranar Talata.
Perez, mai shekaru 27, yana ƙoƙarin raba karensa da wani da suke fada lokacin da ya ji ciwo mai tsanani a wajen.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aris FC, wacce ta karɓi Perez aro daga Celta Vigo, ta tabbatar da cewa ya samu “cizon da ya haddasa kumburin naman wajen,” kuma hakan ya sa ba zai buga wasan UEFA Conference League da za su kara da Araz-Nakhchivan ranar Alhamis ba.
Kocin ƙungiyar, Marinos Ouzounidis, ya bayyana cewa an tsara Perez zai fara wasan kafin lamarin ya faru. “Carles zai kasance cikin ƴan wasa 11 na farko da zasu fara fafatawa” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Barcelona
এছাড়াও পড়ুন:
Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Ziyarci Jama’a, Ya Daina Sauraron Gwamnoni — ADC
Ya ce har yanzu matsalar tsaro tana addabar sassan Nijeriya da dama, kuma ana yaudarar shugaban ƙasa game da hakan.
Ya ce, “Idan Shugaba Tinubu yana sauraron labarai masu daɗi kawai daga waɗanda ke son faranta masa rai, to yana rayuwa ne a cikin duhu.”
Abdullahi ya bayyana cewa al’umma da dama a Nijeriya har yanzu na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga, kuma mutane na rayuwa cikin tsoro da fargaba.
Ya ce ba daidai ba ne a riƙa nuna kamar abubuwa sun inganta, alhalin jama’a na cikin hali na ƙunci ba.
Jam’iyyar ADC ta kuma soki gwamnatin Tinubu da cewa ba ta ɗauki matakan da suka dace ba wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Sun ce maimakon fadar shugaban ƙasa ta riƙa kare shugaban da labaran da ba su dace ba, kamata ya yi su mayar da hankali kan nemo hanyoyin da za su kawo zaman lafiya da tsaro ga ‘yan kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp