Samar da makamashi mai tsafta na zamani shi ne fatanmu — Guterres
Published: 31st, July 2025 GMT
Babban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres,ya bayyana cewa, samar da makamashi mai tsabta da zai daidaita tsarin rayuwar dan Adam daga sarrafa wuta, ta hanyar yin amfani da tururi, zuwa rarrabuwar ma’adinan, shi ne ginshikin bunkasar al’umma.
Mista Gutterres ya bayyana hakan ne a taron inganta samar da makamshi da aka gudanar a harabar ofishin Majalisar Dinkin Duniya.
Ya ce “a yau, muna son tabbatar da yadda za a farka bisa tsarin sabon zamani. Rana tana fitowa don samar da makamashi mai tsabta ga al’umma.
A bara, kusan dukkanin sabbin qarfin wutar lantarki sun fito ne daga abubuwan da ake sabuntawa.
Zuba jari a harkar samar da makamashi mai tsafta darajarsa ta haura zuwa Dala tiriliyan 2 – Dala biliyan 800 fiye da abin da ake samu daga albarkatun mai.
Hasken rana da iska yanzu su ne hanyoyin samar da wutar lantarki mafi arha a duniya, kuma sassan makamashi masu inganci da suke samar da ayyukan yi, kuma suna kara habaka da ci gaba.
Kasashen da ke tattare da burbushin dake samar da makamashi ba sa iya kare tattalin arzikinsu, suna yi musu zagon kasa wanda ke haifar musu rasa wata babbar dama ta tattalin arziki a karni na 21.
Samar da tsabtataccen makamashi yana ba da damar ikon mallakar duk wani nau’i a fannin makamashi da tsaro.
Kasuwannin man fetur ya kasance daga cikin abubuwan yasa farashin da kuma gazawar samar da kayayyaki da rikice-rikice kamar yadda muka gani lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine.
Amma sam duk da hauhawar farashin man fetur, farashin hasken rana, da bashi da takunkumin yana samar da iska, ga kusan kowace al’umma.
A karshe, tsabtataccen makamashi yana havaka, wanda hakan zai iya kai wa ɗaruruwan miliyoyin mutanen dake rayuwa ba tare da wutar lantarki ba a cikin sauri da araha, musamman ta hanyar dakile wutar lantarki da fasahar hasken rana.
Ana barin kasashe masu tasowa a baya. Har ila yau dai makamashin ya mamaye tsarin, kuma har yanzu hayakin yana karuwa lokacin da gaza aiki don gujewa faxawa rikicin sauyin yanayi. Don gyara wannan, muna buƙatar aiki domin daukar mataki.
Na farko, dole ne gwamnatoci su ba da himma wajen samar da tsaftataccen makamashi a nan gaba. A cikin watanni masu zuwa, kowace ƙasa ta yi alƙawarin gabatar da sabbin tsare-tsare na yanayi na ƙasa. Tare da manufa ta shekaru goma masu zuwa. Dole ne wadannan tsare-tsare su kasance sunyi daidaito tare da ƙayyadaddun yanayin zafi a duniya zuwa ma’aunin Celsius 1.5. Kasashen G20, wadanda ke da alhakin kusan kashi 80% na hayakin duniya, dole ne su jagoranci hakan.
Na biyu, dole ne mu gina tsarin makamashi na karni na 21. Ba tare da wata tangarda ta zamani ba, ƙarfin sabunta tsarin yanayi zai iya cika wannan buri namu. Amma ga kowace Dala da aka saka a cikin harkar wutar lantarki.
Na uku, dole ne gwamnatoci su kudiri aniyyar tabbatar da biyan buƙatun makamashi na duniya tare da sabuntawa. Dole ne manyan kamfanonin fasaha suma su taka rawarsu.
Zuwa shekarar 2030, cibiyoyin bayanai za su iya cinye wutar lantarki mai yawa kamar yadda Japan ke yi a yau. Kamfanoni ya kamata su himmatu wajen ba da iko tare da sabuntawa.
Na hudu, dole ne mu sanya adalci a cikin samar da canjin makamashi. Wannan yana nufin cewa tallafa wa al’ummomin da ke dogaro da albarkatun mai don shirya ingantaccen makamashi a nan gaba. Kuma yana nufin sake fasalin samar da ma’adanai mai muhimmanci.
Na biyar, dole ne mu tabbatar da an tsarin samar da makamashi.
Tsabtace hanyoyin samar da makamashi na da matuƙar tasiri wajen mayar da hankali sosai kuma kasuwancin duniya zai bunkasa.
Kasashen da suka kuduri aniyar samar da makamashi dole ne su yi aiki don rarraba kayayyaki, da rage haraji kan kayayyakin makamashi da kuma sabunta yarjejeniyar saka hannun jari ta yadda za su goyi bayan sauyin.
Na shida kuma na karshe, dole ne mu fitar da kudi zuwa ga qasashe masu tasowa. Afirka ta samu kashi biyu ne kacal na jarin da za a iya sabuntawa a bara, duk da cewa tana da kashi 60% na mafi kyawun albarkatun hasken rana a duniya.
Muna buƙatar matakan kasa da kasa don hana biyan basussuka da ake tsotsewa daga kasafin kudin wadannan ƙasashe masu tasowa da kuma ba da dama ga bankunan wajen ci gaban bunkasa ƙasashe da yawa su haɓaka ƙarfin ba da lamuni, da yin amfani da kuɗi masu zaman kansu sosai.
Muna kuma buƙatar hukumomin masu saka hannun jari da su yi la’akari da alƙawarin samar da makamashi mai tsafta.
Wani sabon yanayi na makamashi yana kusa da kai wa ga samun nasara, kuma zai zama da arha, sannan ya kasance wadataccen makamashi mai tsabta da zai samarwa duniya makamshi wadatacce, wajen bunkasa tattalin arziki, kasashe na ‘yancin cin gashin kai da kuma bayar da wutar lantarki kyauta ga kowa.
A nan lokacinmu ne da za mu iya ɗaukar nauyin sauyin duniya. Mu kuma yi amfani da shi yadda ya kamata.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: samar da makamashi mai wutar lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
Daga Usman Muhammad Zaria
Kananan manoma a jihar Jigawa sun yabawa kungiyar Sasakawa Africa dangane da tallafin da take samarwa a fannin inganta noma.
Yayin tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin musamman manoman shinkafa a garin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, sun bayyana cewa tallafin Sasakawa ya habaka noman shinkafar su tare da samun karin kudade.
Manoman sun bayyana cewar shirin ya taimaka masu wajen bunkasa harkokin noma tare da tallafawa al’ummomin su.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin a yankin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, Buhari Nafi’u, yace Sassakawa Africa ta samar masu da tallafin noma daban daban.
A cewar sa tallafin sun hada da horo wanda ya taimakawa kananan manoma wajen ganin sun kara samun kudade tare da inganta rayuwar maza da mata a yankin.
Yace a wannan shekarar sun noma amfanin gona mai yawa sakamakon horon da suka samu karkashin shirin, inda suka hadu sukayi noman a kungiyance a yankin Birnin Kudu.
Buhari ya kara da cewar, a shekarun baya suna daukan kwanaki casa’in kafin su girbe shinkafa amma zuwan Sassakawa ya sa sun yi noma tare da girbe amfanin gonan su a cikin kwanaki saba’in saboda irin da kungiyar ta basu.
Yace yanzu haka sun fara amfani da shinkafar da suka noma a gidajen su.
Yace an basu takin zamani kyauta tare da sauran kayayyakin feshi.
Ya godewa tallafin na Sassakawa, yana mai cewar zai cigaba da amfani da irin da aka basu tare da koyar da mazauna yankin abubuwan da aka horar da su akai.
Shi ma Malam Rufai Nasiru daga yankin na Chandam yace sun kara samun ilimi akan sabbin dubarun noma wanda suka samu daga kungiyar ta Sassakawa.
Yace a bana ya noma buhun shinkafa 8 ba kamar a baya ba da yake noma buhu biyar, yana mai cewa shirin yana da inganci kuma zai cigaba da amfani da irin da kungiyar ta basu.
A garin Chuwasu dake karamar hukumar Taura, Aminu Babanyara ya bayyana cewar sun ci moriyar shirin ta hanyar samun iri masu inganci da takin zamani da kuma horo akan sabbin dubarun noma.
Yace wasu daga cikin abubuwan da suka koya sun hada da amfani da shara wajen yin taki a gida inda suka ce hakan yasa sun samu karin shinkafa da geron da suke nomawa idan aka kwatanta da shekarun baya.
Babanyara, yace sabbin dubarun da suka koya da kuma irin da Sassakawa suka basu, ya basu damar ninka abin da suka saba nomawa a damina sau uku.
Yace da farko suna da shakku akan amfani da sabbin irin da sabbin dubarun noman, amma kuma bayan sun gwada a shekaru biyu na farko sun ga alfanun hakan wajen bunkasa amfanin gonan da suke nomawa.
Manoman sun kuma yi kira ga kunyiyar ta Sassakawa ta samar masu da injinan casa domin saukaka masu al’amura.
Malama Amina Abdulrahman wacce tayi jawabi a madadin kungiyar mata manoma a Karamar Hukumar Taura, tace shirin tallafin Sassakawa ya kawo sauyi a rayuwar su musamman a fannin samun kasuwanci da amfanin gonar da ake sarrafawa don yin abinci mai gina jiki na yara.
A cewar ta an horar da su akan yadda za su samar da abinci mai gina jiki a yankuna tare da yadda za su yi aiki a kungiyance don inganta noma.
A don haka, tayi kira ga kungiyar Sassakawa ta samar masu da injinan sarrafa amfanin gona na zamani.
Yankunan da aka ziyarta sun hada da Chandan dake Birnin Kudu da kuma Sabon Gari shi ma a karamar hukumar Birnin Kudu.
Sauran sun hada da Baranda dake Dutse da kuma Chuwasu dake karamar hukumar Taura.