Aminiya:
2025-06-15@11:15:42 GMT

Zanga-zangar da za mu yi babu gudu babu ja da baya — Take It Back

Published: 7th, April 2025 GMT

Ƙungiyar Take It Back ta ce zanga-zangar da za gudanar a yau babu gudu babu ja da baya domin nuna adawa da dokar ta-baci da aka sanya a Jihar Ribas da kuma abin da ta kira cin zarafin bil’adama da kuma amfani da dokar ta’addancin yanar gizo ba bisa ka’ida ba.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta gargaɗi masu shirin yin zanga-zanga ranar Litinin 7 ga watan Afrilu a faɗin ƙasar su sake tunani domin a ranar ce ‘yan sandan ƙasar suke bukukuwa domin nuna gudunmawar da suka bayar don ci-gaban Nijeriya.

Rundunar ta ce zanga-zangar da wata ƙungiya mai suna “Take It Back” ta shirya tana zuwa ne a lokacin da bai dace a yi zanga-zanga a ƙasar ba.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan ƙasar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce rundunar ba ta adawa da ‘yancin ‘yan ƙasar na taruwa da yin gangami da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba su.

Sai dai kuma sanarwar ta ce rundunar na fargaba game da burin waɗanda suka shirya yin zanga-zangar rana ɗaya da ranar da aka ware domin yaba wa irin jajircewa da sadaukar da kai na ‘yan sandan Nijeriya.

“Bisa ga ingatattun ɗabi’un da ƙasashen duniya ke bi wajen yabawa da nasarorin ‘yan sandansu, gwamnatin Nijeriya ta ɗauki matakin ayyana ranar 7 ga watan Afrilu a matsayin ranar ‘yan sandan Nijeriya,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa bikin zai samu halartar baƙi daga ciki da wajen ƙasar daga fannoni daban-daban, ciki har da sufeto janar na ‘yan sandan ƙasashen ƙetare da kuma jami’an diflomasiyya.

“Dalilin gudanar da zanga-zanga a irin wannan ranar abin dubawa ne kuma a iya cewa wani mataki ne na ɓata sunan ‘yan sandan Nijeriya da ƙasar ma baki ɗaya,” in ji sanarwar.

“Saboda haka rundunar ‘yan sandan Nijeriya tana bai wa waɗanda suka shirya wannan zanga-zangar shawarar janyeta saboda lokacin bai dace da ita ba kuma tana da manufar aikata ɓarna,” in ji Olumuyiwa.

Sai dai duk da wannan gargaɗi, ƙungiyar ta Take It Back ta ce tana nan kan bakarta domin nuna adawa kan abin da ta kira mulkin kama karya da gwamnatin Shugaba Tinubu ke yi a ƙasar nan.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan sandan Nijeriya zanga zangar

এছাড়াও পড়ুন:

Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka

Da yake nasa jawabin, Sangare ya ce, Nijar na bin manufar Sin daya tak a duniya, kuma tana ba da fifiko ga hadin gwiwarta da kasar Sin, da mayar da hankali sosai kan harkokin tsaro, kana tana son kara amincewa da juna, da ci gaba da yin shawarwari bisa mutunta juna a tsakaninsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Trump ya dakatar da kamen baƙin haure a wasu wurare na Amurka
  • An Yi Zanga-zangar Nuna Goyon Baya Ga Kin Amincewa Da Bakin Haure A Amurka 
  • Damina: NiMet ta gargaɗi jihohi 13 kan barazanar ambaliyar ruwa
  • Iran : Halin da ake ciki ba zai iya bada damar tattaunawa da Amurka ba
  • An kama ’yar Najeriya da laifin safarar ɗalibai 15 a Australia
  • Hajjin 2025: Yadda Alhazan Nijeriya 7 Suka Rasa Rayukansu A Saudi Arabiya
  • Cikakken Jerin Sunaye: Tinubu Ya Karrama ‘Yan Nijeriya 102 Don Bukin Ranar Dimokuradiyya Ta 2025
  • Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka
  • Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamna Zulum ya yi wa fursunoni 66 afuwa
  • Ranar Dimokuraɗiyya: Gwaman Zulum ya yi wa fursunoni 66 afuwa