Wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu saboda ɗan Kudu ne — Onanuga
Published: 31st, July 2025 GMT
Bayo Onanuga, Mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya ce wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu ne kawai saboda ya fito daga Kudancin Najeriya.
Yayin wata hira da Trust Radio, Onanuga ya ce maganar cewa ana yi wa Arewacin Najeriya wariya ba gaskiya ba ce, face tsantsar siyasa kawai.
Ya ce ƙorafin da Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta yi na cewa an yi watsi da Arewa wajen naɗe-naɗen muƙaman gwamnati da ayyukan ci gaba, wata dabara ce kawai don rage ƙimar shugabancin wanda ya fito daga Kudu.
Ya shawarci ’yan siyasar Arewa da su yi haƙuri, kamar yadda ɓangare Kudu ya yi lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari, wanda ya shugabanci ƙasar har na tsawon shekaru takwas.
“Shugaba Tinubu ɗan Najeriya ne kamar kowa. Ya cancanci yin shekaru takwas a kan mulki kamar yadda Buhari ya yi. Ka da mu lalata ƙasa saboda son zuciya,” in ji Onanuga.
Dangane da zargin cewa an fi bai wa ’yan Kudu muƙamai, Onanuga ya ce masu sukar Tinubu su kawo hujjoji da ƙididdiga maimakon su ci gaba da yin zargin da ba shi da tushe.
Ya ƙara da cewa babu wani yanki da ba shi da matsalar hanyoyi ko ayyukan da ba a kammala gama ba, amma ya ce gwamnatin yanzu na ƙoƙarin gyara abubuwan da ta gada.
“Kafin ku zargi gwamnati, sai ku binciki gaskiyar lamarin. Wannan duk siyasa ce kawai don a raina Shugaban Ƙasa,” in ji shi.
Onanuga, ya kuma kare matakin da Tinubu ke ɗauka wajen inganta tsaro.
Ya ce an samu ci gaba sosai, inda ya kafa misalin cewar dukkanin shugabannin tsaro daga yankin Arewa suka fito.
Ya ce yanzu yana iya yin tafiya daga Kaduna zuwa Abuja cikin kwanciyar hankali, tafiyar da a da ta ke da hatsari sosai.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arewa ayyuka Bayo Onanuga Siyasa Tsaro Wariya zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta
Shugabannin Rundunar tsaro da Tinubu ya sallama sun hada da shugaban rundunar tsaro ta kasa Janar Christopher Musa da shugaban sojojin ruwa, Emmanuel Ikechukwu Ogalla da shugaban sojojin sama Hassan Abubakar.
Wadanda suka maye gurbin su da idanu ya koma kan hobbasar kwazon da za su nuna su ne shugaban rundunar tsaro Olufemi Oluyede, shugaban sojojin kasa Waidi Shaibu, shugaban sojojin ruwa Idi Abbas da shugaban sojojin sama S.K Aneke sai kuma shugaban rundunar leken asiri, EAP Undiendeye wanda ya ci-gaba da rike kujerar sa.
Yan Nijeriya sun jima suna kukan duk da kwarewa da gogewar jami’an sojojin Nijeriya da irin makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro a kowace shekara amma matsalar kullum gaba- gaba take kara yi.
Yankuna da dama a Nijeriya musamman a Arewa- Maso- Yamma, Arewa- Maso- Gabas da Arewa ta tsakiya sun zama lahira kusa a bisa ga yadda barayin daji ke garkuwa da mutane, kone garuruwa da yi wa jama’a kisan kare dangi.
Gagarumar matsalar wadda tuni ta zama tamkar ruwan dare a tsayin shekaru ta ci dimbin rayuka da dukiyoyin al’umma ba adadi ba tare da samun gagarumar nasarar dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma ba.
Masana tsaro sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan sauye- sauyen. Wasu na ganin cewa sabbin jini za su iya kawo canji, yayin da wasu suka yi gargadin cewa sauya shugabanni kadai ba zai wadatar ba idan ba a yi gyaran tsari ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA