Aminiya:
2025-07-31@20:10:22 GMT

An kama wasu mata na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka sace

Published: 24th, April 2025 GMT

Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta kama wasu mata biyu a lokacin da suke yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da aka yi garkuwa da shi a Owerri kan kuɗi Naira miliyan 2.7.

An yi garkuwa da yaron ne a Abuja a lokacin da yake tallan kayan miya, sannan aka kawo shi Owerri a sayar da shi kafin a sa’ar kuɓutar da shi daga masu son sayar da shi.

An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe Na ba ku wata 1 ku murƙushe ’yan ta’adda — Olukoyede ga sojoji

Waɗanda ake zargin sun haɗa da Joy Ugwu daga garin Idah ta jihar Kogi, da Rosella Michael daga garin  Zamba da ke Abuja, yayin da ta ukun da ake zargin ma’aikaciyar jinya ce da ta tsere a yanzu.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Henry Okoye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Okoye ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a Owerri, babban birnin jihar a ranar 14 ga watan Afrilu, biyo bayan wani samame da jami’an tsaro suka yi a lokacin da suke ƙoƙarin siyar da yaron kan kuɗi Naira miliyan 2.7.

Ya ce, an kama mutanen ne biyo bayan ƙoƙarin haɗin gwiwa tsakanin rundunar ’yan sandan Jihar Imo da hedikwatar ’yan sandan shiyya ta 7 da ke Abuja, duk da cewa an miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na shiyyar Abuja, domin ci gaba da bincike da gurfanar da su gaban kuliya.

Okoye ya ce, “Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta gano wani mutum da ake zargi da safarar ƙananan yara, lamarin da ya kai ga cafke wasu mata biyu da ake zargi tare da kuɓutar da wani yaro ɗan shekara huɗu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Owerri da ake zargin

এছাড়াও পড়ুন:

Cikin Wata 2 Ƴansanda Sun Damƙe Mutane 5,488, Sun Ceto 170 Da Aka Sace

IGP ya yabawa tawagar Interpol reshen Nijeriya bisa ceto Ghanawa 46 da aka yi safararsu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Horas Da Mata 600 Kan Abincin Yara Mai Gina Jiki A Jigawa
  • Zargin Da Wasu ’Yan Siyasar Amurka Ke Yi Wa Sin Na Fitar Da Hajoji Fiye Da Kima Ya Sabawa Hujjoji Na Hakika
  • ‘Yan Sandan Niger Sun Hada ‘Yan’uwa Mutanen 35 Da Aka Ceto Da Iyalansu 
  • Kwara Ta Kwashe Mabarata Daga Titunan Jihar Su 94
  • ’Yansanda Sun Ceto Mutane 28 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
  • Shugaban SUBEB Yayi Alkawarin Bayar Da Tallafin Ilimi A Jihar Nasarawa
  • An Kaddamar da Makon MNCH na 2025, Ya Rarraba Fakitin Bayarwa 6,000, Kayan C/S 500
  • Cikin Wata 2 Ƴansanda Sun Damƙe Mutane 5,488, Sun Ceto 170 Da Aka Sace
  • ‘Yan Sanda A Kano Sun Kama Kasurgumin Dan Fashin Nan Barga Da Wasu Mutum 14
  • Jami’an Tsaron Katsina Sama Da 100 Sun Rasu A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda – Gwamnati