Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi kakkausar suka ga sabbin takunkuman da Amurka ta kakabawa kasarta

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i, ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane, hukumomin shari’a da jiragen ruwa masu alaka da makamashi da man fetur na Iran sabbin takunkumi.

Baqa’i ya gwada rashin amincewar Iran da bakar siyasar Amurka da na ‘yan sahayoniyya musamman farmakin da Amurka da gwamnatin sahayoniyya suka kaddamar na baya-bayan nan kan kasar Iran, yana mai bayyana kakaba takunkumin a matsayin baya da wani harumi na doka kawai matakin zalunci ne kan Iran lamarin da ke fayyace kiyayyar Amurka karara kan Iran.

Baqa’i ya kara da cewa: Al’ummar Iran suna sane da mummunar manufar wadannan tsauraran takunkumin da suke da nufin raunana Iran da neman take mata kowane irin hakki, za su tsaya da dukkan karfinsu wajen kalubalantarsu domin kare mutunci da muradunsu.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya jaddada cewa: Dabi’ar da Amurka take gudanarwa na nuna son kai da kuma bin hanyar da ba ta dace ba da tilastawa wajen cimma haramtattun manufofinta a matakin kasa da kasa, da kuma rashin mutunta tsarin doka da ‘yancin bil Adama, sun yi hannun riga da tushen dokokin kasa da kasa, gami da ka’idar mutunta ‘yancin kasashe da ‘yancin cinikayya tsakanin kasashe, da kuma daukan matakan nuna barazana ga duniya da ba a taba gani ba.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tawagar Iran Ta Fice A Taron Majalisun Dokokin Kasashen Duniya A Lokacin Jawabin Wakilin Isra’ila July 31, 2025 Kasar Iran Ta Bayyana Gushewar Hasashen Raunin Karfin Sojinta Kuma Ba Zai Dawo Ba July 31, 2025 Sojan Amurka Ya Bada Ruwayar Yadda Sojojin Sahayoniyya Suka Kashe Wani Yaro Balasdine July 31, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku   July 31, 2025 Qolibaf: Barin HKI Ta Yi Abinda Taga Dama Ne Yana Karfafa Mata Giwa July 30, 2025 Yunwa Ta Kashe Karin Falasdinawa 7 A Gaza July 30, 2025 Malta Zata Amince da Samuwar Falasdinu a Cikin Watan Satumba Mai Zuwa July 30, 2025 Amurka Ta Ce HKI Ba Zata Fice Daga Kasar Lebanon Ba Sai An Kwance Damarar Hizbullah July 30, 2025 Siriya Da HKI Zasu Gudanar Da Taro A Baku July 30, 2025  Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Kada Yankin Kamtashatka Na Kasar Rasha July 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher

Qatar ta bayar da tallafin gaggawa ga mutanen da suka rasa matsugunansu a Sudan

Gwamnatin Qatar ta aika da agajin gaggawa da tallafin jin kai zuwa birnin Ad-Dabba da ke Jihar Arewacin Sudan domin rage wa dubban mutanen da suka rasa matsuguninsu da ke tserewa daga El Fasher, babban birnin Jihar Arewacin Darfur.

Ma’aikatar Harkokin Waje ta Qatar ta bayyana cewa: “Wannan tallafin ya zo ne a cikin tsarin jajircewar Qatar na tallafawa ‘yan uwantaka na Sudan, musamman idan aka yi la’akari da mawuyacin halin jin kai da fararen hula ke ciki, ciki har da karancin abinci mai tsanani da kuma karuwar bukatar matsugunai da kayan masarufi.”

Sanarwar ta kara da cewa wannan tallafin wani bangare ne na kokarin da Qatar ke yi na tsayawa tare da ‘yan uwantaka na Sudan da kuma rage musu wahalhalun da rikicin yaki da makamai ya haifar. Haka nan ya kunshi rawar da Qatar ke takawa wajen karfafa martanin jin kai da kuma gina gadoji na hadin kai da al’ummar da abin ya shafa a fadin duniya.

Tallafin ya kunshi kimanin buhuhunan abinci 3,000, tantuna 1,650, da sauran kayayyakin bukatu, wanda Asusun Ci Gaban Qatar da kuma Hukumar Ba da Agaji ta Qatar suka bayar, don tallafawa wadanda suka rasa matsuguninsu daga El Fasher da yankunan da ke kewaye. Ana sa ran sama da mutane 50,000 za su amfana daga wannan tallafin, wanda ya haɗa da kafa sansanin agaji na musamman na Qatar mai suna Qatar Charity.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci November 2, 2025 Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza November 2, 2025 Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Pezeshkian: Bunkasa Masana’antar Makamashin Nukiliyar Iran Don Inganta Rayuwar Al’ummar Iran Ne
  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher
  • Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
  • Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3
  • Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar