Akasarin masu kai mana hare-hare daga jihohin da suka kewaye mu suke – Gwamnatin Filato
Published: 19th, September 2025 GMT
Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamna Caleb Mutfwang ya kafa kan kashe-kashen da ke ci gaba da faruwa a Jihar Filato ya ce akasarin masu kai hare-hare suna fitowa ne daga jihohin da ke makwabtaka da Filato.
Shugaban kwamitin, Manjo Janar Rogers Ibe Nicholas, ya bayyana cewa sun gana da kabilu daban-daban da kungiyoyin masu ruwa da tsaki, tare da ziyartar dukkan al’ummomin da rikici ya shafa domin samun sahihan bayanai kan tashin hankalin da kuma hanyoyin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.                
      
				
Ya ce daga binciken da suka gudanar, an gano cewa masu kai hare-hare kan al’ummomin Filato suna fitowa ne daga jihohin Nasarawa, Kaduna, Bauchi da kuma Taraba.
“Kwamitin ya karɓi rahoton korafi daga wasu kauyuka biyu da ke jihar Nasarawa da ke iyaka da Quan’pan, inda aka ce ’yan bindiga sun kafa sansaninsu, lamarin da ya tilasta wa al’ummomin Filato da ke Quan’pan tserewa.”
“A Wase da Kanam, an samu rahoton cewa akwai sansanonin ’yan bindiga da ake zargin suna da alaƙa da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.
“Dalilan da muka gano na haifar da hare-haren sun haɗa da kwace ƙasa da albarkatu faɗaɗa danniya, mamayar kabilanci da addini, rikicin siyasa, sai kuma karbar kudin fans ana masu garkuwa da mutane.
“Iyakokin da aka fi kia hari daga su sun haɗa da hanyoyin shigowa daga Nasarawa ta Wamba, Lafia da Awe; daga Kaduna ta Lere, Kaura da Sanga; daga Bauchi ta Toro, Tafawa Balewa, Bagoro da Alkaleri; da kuma daga Taraba ta Ibi da Karim Lamido.
“Wadannan hanyoyi ba sa samun kulawa sosai, kuma masu kai hari na amfani da su don kai farmaki da tserewa cikin sauri,” in ji shi.
Manjo Janar Rogers ya kuma jaddada cewa an kai hari a ƙauyuka 420, kuma kusan rayuka 12,000 sun salwanta, don haka ba za su bari a ci gaba da waɗannan kisan gillar ba.
Gwamna Caleb Mutfwang, yayin karɓar rahoton a gidan gwamnatin jihar da ke Jos, ya yi alkawarin aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
Haka kuma, Gwamnan ya bayyana shirinsa na miƙa rahoton ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ƙwararrun jami’an tsaro, domin su fahimci yadda rikicin ya shafi jihar sama da shekaru 20, tare da samar da mafita mai ɗorewa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Matsalar Abinci
এছাড়াও পড়ুন:
Karuwanci da zubar da cikin ’yan mata ’yan gudun hijira ya karu a Maiduguri
Sarakunan gargajiya, lauyoyi da jami’an gwamnati sun koka bisa yawaitar kananan ’yan mata da ke daukar ciki da kuma zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba, a sansanonin ’yan gudun hijira da ke Maiduguri, Jihar Borno.
Lamarin ya fito fili ne a wani taron tattaunawa na kwanaki biyu da ƙungiyar Grassroots Researchers Association (GRA) ta shirya tare da tallafin We Are Not Weapons of War (WWoW) a karshen makon da ya gabata a Maiduguri.
Taron ya haɗa mutane fiye da 500, ciki har da waɗanda suka tsira daga fyade da cin zarafi a lokacin rikici, sarakunan gargajiya, lauyoyi, jami’an gwamnati da abokan ci gaban ƙasa, domin tattauna hanyoyin magance wannan matsala.
“’Yan mata kanana na sayar da jikinsu, suna kuma zubar da ciki a bandaki,” in ji wata mai taimaka wa GRA, Zaynab Abdallah.
NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a Najeriya Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a KanoShugaban sansanin ’yan gudun hijira na EYN Jerusalem da ke unguwar Wulari a Maiduguri, Mista John Gwoma, ya bayyana yadda kananan ’yan mata da ƙananan yara ke fadawa tarkon lalata da kuma zubar da ciki a asirce.
Ya ce, “Wasu maza daga cikin gari kan zo cikin manyan motoci su ɗauki waɗannan ’yan mata ƙanana, su yi lalata da su har su sami ciki. Saboda haka yanzu zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba ya zama ruwan dare a sansanin.”
Ya ƙara da cewa, “Bandakunan mata sun koma kamar mayanka. Ana samun jini ko’ina saboda waɗannan ’yan matan na shiga su zubar da ciki sannan su bar tayin a ciki. Wasu iyaye na sane da abin da ’ya’yansu ke yi”
Wata mai taimaka wa GRA, Zaynab Abdallah, ta tabbatar da wannan zargi, tana mai cewa karuwanci da kuma zubar da ciki tsakanin ƙananan yara na ƙara yaduwa a Maiduguri.
Ta ce, “Wasu daga cikin waɗannan ’yan mata ƙanana suna lalata ne domin samun kuɗin abinci ga iyalansu. Amma abin takaici, wasu iyaye suna sane da hakan, amma suna yi shiru saboda suna amfana da abin da ’ya’yansu ke samu.”
Zaynab ta ci gaba da cewa, “Talauci ya kai ga karuwanci ya zama tamkar wani ɓangare na rayuwarsu. Ba za ka iya hana su ba. Idan sun sami ciki, sai su zubar da shi a ɓoye domin guje wa tozarci.”
Rikici da talauci sun kai mata ga lalacewa”A yayin zaman, waɗanda suka tsira daga fyade da sauran masu ruwa da tsaki sun ruwaito irin raɗaɗin da suka sha na fyade, da kuma yadda matsin tattalin arziki ke tura mata cikin harkar karuwanci.
Sai dai sun kuma bayyana yadda gangamin wayar da kai na GRA ya taimaka wajen rage tozarci da suka sha, tare da ƙara musu ƙarfin guiwa wajen neman adalci a kotuna.
Daraktan gudanarwa na ƙungiyar GRA, Mista Friday Bitrus, ya ce sakamakon tattaunawar da suka samu daga mahalarta zai zama ginshiƙi wajen fitar da takardar “Kira ga Daukar Mataki” domin tursasa gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su ɗauki matakai na gaskiya.
Ya ce, “Abin da muka tattara daga bakin waɗanda abin ya shafa da sauran mahalarta ya nuna cewa akwai gaggawar buƙatar tsari na musamman don kare ’yan mata da mata daga fyade, ciki da kuma zubar da ciki a sansanonin.”
Kira ga gwamnatiMasu ruwa da tsaki a taron sun yi kira ga gwamnati ta ƙara tsaurara matakai wajen tsaron sansanonin, ta samar da abinci da kayan masarufi, da kuma hanyoyin koyar da sana’o’in dogaro da kai ga ’yan gudun hijira — musamman mata da matasa.
Sun kuma bukaci a hukunta duk wanda aka kama da laifin lalata da yara a sansanonin, tare da samar da ingantattun cibiyoyin kula da lafiya domin dakile zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba.
A cewar wani mahalarcin taron, “Wannan matsala ba wai ta Borno ce kawai ba, tana iya bazuwa zuwa sauran jihohi idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba.”
Taron ya ƙare da amincewa da kafa kwamitin bin diddigi domin tabbatar da cewa an aiwatar da shawarwarin da aka cimma.