2025-10-13@22:07:51 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6889
«dukiya»:
Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce ta ware naira biliyan biyu domin biyan kudaden tallafin karatu da alawus alawus na guraben karatu a jihar. Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da biyan alawus-alawus na shekarar 2023/2024 da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta karamar hukumar Akwanga ta jihar. Gwamnan...

Shugaban Gidauniyar Malala, ya jaddada kudirin gidauniyar na bunkasa ilimin yara mata a fadin Najeriya.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a fadarsa da ke Zariya. Da yake jawabi, shugaban gidauniyar Malala, Mista Ziouddin Yousafzai ya yaba da kyakkyawar tarba da aka yi masa tare da tawagarsa, inda ya bayyana Masarautar Zazzau a matsayin...
Hukumar Kwastam ta Kano/Jigawa ta kama jimillar kafso guda 261,750 na Polyglycine (miligiram 300) da allunan Tramadol hydrochloride 228,700 (miligiram 225) da aka boye a cikin buhunan jumbo guda biyar. Shugaban hukumar kwastam na yankin Kano, Dalhatu Abubakar, ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce an...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya isa birnin bandar Abbas a jiya alhamis gari na 10 ke nan a ci gaba da ziyarar aiki yi a fadin jihohin kasar, da yake kaddamar da ayyukan ci gaba da aka kammala. Ziyarar ta shugaban kasa a jihohi tana taimakawa wajen samar da cundanya...
Fira ministan kasar malesiya Anwar Ibrahim da na Pakistan shehbaz sharif suna tir da matakin da HKI ta dauka kan jiragen tawagar Sumud Flotilla ajiya Alhamisi a shafukansu na X , bayan da jagororin tawagar suka sanar da cewa sojojin HKI sun kama jiragen ruwa guda 14 dake dauke da yan kasashen waje da kayayyakin...
Wani abu da ya ja hanklan mutane shi ne, irin muggan makaman da ‘yan bindigar suka hallara da su a wajen kulla yarjejeniyar, wadanda kuma babu wani mahaluki da ke da ikon kwace makaman daga hannunsu, a yayin kulla yarjejeniyar, ta jeka nayi ka. Kazalika, a cikin daya daga cikin faifan Bidiyon, an ga yadda...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A zamanin yau na fasahar zamani, musamman fasahar kirkirarriyar basir ta (AI), harkokin sana’o’i da dama suna fuskantar sauye-sauye masu girma. Daya daga cikin sana’o’in da ke cikin babban hadari shi ne sana’ar ɗaukar hoto musamman irin wadanda ke kashe makudan kudi wajen sayen kyamara da bude katafaren gidajen...
Ministar kula da shari’a da harkokin majalisar dokoki da hakkin mata ta kasar Sao Tome and Principe Vera Cravid ta yi kira a maida dangantakar dake tsakanin kasarta da kasar Sin a matsayin misalin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, domin dangantakarsu tana da tarihi mai zurfi da kuma samun ci gaba a zamanin...
Sule ya bayyana cewa, “ilimi shi ne abu mafi mahimmanci da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali akai, hakan ne ya sa aka ware kashi 36 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025 ga sashen ilimi”. Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta dawo da tallafin karatu na ƙasashen waje, inda a...
Gomman matasa a Jihar Kano sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a ranar Alhamis domin bayyana goyon baya ga Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP AI Bakori. Matasan da suka gudanar da zanga-zangar sun daga kwalaye da alluna dauke da sakonnin “A bar mana CP”, “Mutanen Kano suna bayan CP,” da “Gwamna Abba Kabir Yusuf ka...
A nasa jawabin, gwamnan ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tsige CP Bakori, yana mai nuni da rashin halartar rundunar ‘yansanda daga faretin bikin a matsayin rashin mutuntawa da tsoma baki cikin siyasa. Sai dai ga dukkan alamu, kalaman gwamnan sun janyo rashin amincewar jama’a musamman a tsakanin matasan Kano. Zanga-zangar...
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kori dukkan Kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa. A cewar wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal babban birnin jihar a yammacin Laraba ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi matakin korar ya fara aiki nan take, kuma ya biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli...
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun jaddada aniyarsu ta watsi da duk wata barazanar makiya tare da alwashin mayar da martani mai tsanani fiye da harin alkawarin gaskiya da ya gabata A cikin wani sako mai kakkausar murya, Dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun yi gargadi ga haramtacciyar kasar Isra’ila game da...
Masar ta jaddada goyon bayanta ga zaman lafiyar Sudan tare da yin watsi da matakan bangare guda kan kogin Nilu Kasar Masar ta jaddada cikakken goyon bayanta ga zaman lafiyar kasar Sudan da kuma yankinta a jiya Laraba, tare da tabbatar da hadin kan matsayar kasashen biyu da kuma kin amincewa da matakan bangare daya...
Rundunar ta kuma bayyana cewa, a ranar 30 ga watan Satumba da misalin karfe 11:15 na safe, wata tawagar rundunar ta kama wasu mutane biyu a filin tirela na Dangauro. Sanarwar ta kara da cewa, “An samu wadanda ake zargin dauke da buhu bakwai da ake zargin kayan maye ne wanda aka fi sani...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta yi wata babbar nasarar kama masu baiwa ’yan bindiga makamai da kama wani fitaccen mai safarar miyagun ƙwayoyi da kuma dillalan makamai ba bisa ƙa’ida ba a wurare daban-daban a faɗin jihar. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da...
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kori dukkan Kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa. A cewar wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal babban birnin jihar a yammacin Laraba ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi matakin korar ya fara aiki nan take, kuma ya biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli...
Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana matuƙar alhininta kan mummunan hatsarin kwale-kwale da ya faru a kan Kogin Neja, inda aƙalla mutum 26 suka rasa rayukansu. Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo ya fitar a ranar Laraba ta ce wannan mummunan lamari ya rutsa da ‘yan kasuwa da suka taso daga ƙaramar hukumar Ibaji ta jihar...
Matan Sojoji da aka tsare bisa laifuka daban-daban a yaƙin da ake yi da ’yan Boko Haram ko Ƙungiyar ISWAP a garin Maiduguri jihar Borno, a bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai sun roƙi shugaba Bola Tinubu da hukumomin soja da su tausaya musu ta hanyar yi wa mazajensu afuwa. Matan da yawansu...
Matan Sojoji da aka tsare bisa laifuka daban-daban a yaƙin da ake yi da ’yan Boko Haram ko Ƙungiyar ISWAP a garin Maiduguri jihar Borno, a bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai sun roƙi shugaba Bola Tinubu da hukumomin soja da su tausaya musu ta hanyar yi wa mazajensu afuwa. Matan da yawansu...
Mazauna unguwar Sabon Gero, dake bayan Millennium City a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, sun roƙi gwamnatin jihar da ta gaggauta kammala aikin gyaran titin unguwar, wanda suka ce an bar shi a cikin mawuyacin hali duk da cewa an bai wa wani kamfani aikin kusan shekara guda da ta gabata. Mazauna...
Makarantar Kwalejin Kagara da ke Jihar Neja, wadda ta yi fice wajen yayi ɗalibai masu hazaƙa, yanzu ta zama kufai. A shekarar 2021, Boko Haram ta kai hari makarantar ta sace aƙalla dalibai da malamai 27. 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Jiya na...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kasashen duniya na ci gaba da yin Allah wadai da farmakin da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kan jiragen ruwan ‘yan fafatuka dake dauke da kayan agaji ga al’ummar Gaza. Kungiyoyin Falasdinawa, kwararru na Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatocin Turai sun bi sahu inda sukayi tir da harin baya bayan nan da aka...
Kotun koli ta Soji a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta yanke wa tsohon shugaban kasar Joseph Kabila hukuncin kisa bisa samunsa da laifin cin amanar kasa da laifukan yaki ciki har da jagorantar kungiyar ‘yan tawayen M23. An samu Kabila da laifuffuka da dama da suka hada da shiga wani yunkuri na tayar da kayar baya,...
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce idan bukatar hakan ta taso, zai iya janye burinsa na takarar shugaban kasa a 2027 don mara wa matashi baya. Atiku, wanda jigo ne a haɗakar jam’iyyun adawa ta ADC, ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da BBC Hausa a ranar Laraba. NAPTIP ta kama mahaifin...
Ya ce bambancin Nijeriya na ƙabilu, addinai da al’adu bai kamata a ɗauka a matsayin matsala ba, illa ma ya zama ƙarfin ƙasar. “Idan aka tafiyar da bambancin nan da kyakkyawan shugabanci, Nijeriya za ta samu girmamawa a duniya,” in ji shi. Obasanjo ya jaddada cewa ilimi shi ne tushen ci gaba, ba tare da...
Iran ta yi kira da a gaggauta kakaba wa gwamnatin Isra’ila takunkumi mai tsauri kan kisan kiyashin da take ci gaba da yi a zirin Gaza, sakamakon rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a baya-bayan nan. Da yake jawabi a wajen taron kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya karo na 60...
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce soke faretin zagayowar ranar ’yancin kai karo na 65 da sojoji ke yi ya ba shi damar yin lafiyayyen barci da kuma yin kyakkyawan kari a ranar Laraba. Aminiya ta rawaito cewa Gwamnatin Tarayya ta soke bikin da aka shirya domin murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin...
Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya yaba da hadin kai, tsayin daka, da ci gaban Gombe da Najeriya a daidai lokacin da jihar ke cika shekaru 29 da samun ‘yancin kai tare da bikin cikar kasar shekaru 65 da samun ‘yancin kai. A cikin sakon fatan alheri mai dauke da sa hannun babban...
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa, ya taya gwamnati da al’ummar Nijeriya murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, inda ya bayyana ranar a matsayin abin tunawa da hadin kai, juriya, sadaukarwa da suka gina kasar. A sakonsa na fatan alheri, Gwamna Namadi ya ce bikin ba wai kawai lokacin yin tunani ne...
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Jibril Ismail Falgore, ya mika sakon taya murna ga ‘yan Najeriya a daidai lokacin da kasar ke cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar, shugaban majalisar ya bayyana tafiyar Najeriya bayan samun ‘yancin kai...

‘Yan siyasa a Nijar sun nemi da su yi aiki tare domin tabbatar da ba a samu cikas a zaben kananan hukumomi ba
An shawarci ‘yan siyasa a jihar Neja da su kiyaye mutuncin da aka san jihar da su domin tabbatar da nasarar zaben kananan hukumomin jihar da ke tafe. Zaben da aka shirya gudanarwa a ranar farko ga watan Nuwamba na wannan shekara, ya yi alkawarin za a yi shi cikin gaskiya ba tare da...
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya taya al’ummar Jihar Nasarawa murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai da kuma Jihar Nasarawa da ta cika shekara 29 da samun ‘yancin kai. Wata sanarwa da ta sanyawa hannu kuma ta raba wa manema labarai, mashawarci na musamman ga gwamna kan harkokin yada labarai Malam...

Kwara ta bukaci a sanya ido sosai, yayin da jami’an tsaro ke kara kai hare-hare a maboyar masu garkuwa da mutane
Gwamnatin jihar Kwara ta shawarci al’ummar da ke kewayen kananan hukumomin Ekiti, Ifelodun, Isin, Oke Ero, da Irepodun, da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita harkokin a wuraren da sojoji ke aikin musamman. A wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Bolanle Olukoju ya fitar t cea shawarar ta biyo bayan tsaurara matakan tsaro...
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana damuwarta kan yadda likitoci ke kin zuwa aiki musamman a lokutan da suke kai ziyara wuraren kiwon lafiya da ba a shirya ba. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar, Suleiman Isah ya fitar, ya ce kwamishinan lafiya Dr. Nafisa Muhammad Maradun ta...
Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Gombe, Julius Ishaya Lepes, ya rasu. Ishaya, ya riƙe mukamin Kwamishina a farkon gwamnatin Inuwa Yahaya na tsawon shekaru huɗu, amma ya yi murabus domin yin takara. Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina yin maganganu ɓatancin ga ƙasar. Ya ce Najeriya ƙasa ce mai girma, mai cike da damar ci gaba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina yin maganganu ɓatancin ga ƙasar. Ya ce Najeriya ƙasa ce mai girma, mai cike da damar ci gaba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9...
Manyan garuruwan da suka shiga cikin wannan jerin sun haɗa da Mubi, Gusau da Azare. Ma’aikatar ta roƙi jami’an gwamnati a jihohi da sauran masu ruwa da tsaki da su sa ido sosai kan halin da ake ciki kuma su bayar da rahoto a kan lokaci. Haka kuma, ta shawarci jama’a da ke zaune kusa...
Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemah Mohajerani ta fayyace cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta maraba da yaki, amma tana ci gaba da shirye-shiryen tsaro mafi girma don kare kanta. Ta kara da cewa Tehran ta bayar da shawarar tattaunawa da Amurka kai tsaye a wata ganawa tare da ministocin Turai, amma wakilin...
Batun siyasar Najeriya ya sake ɗaukar hankali yayin da jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa a 2027. Wannan batu ya tayar da muhawara mai zafi a tsakanin masana, da ‘yan siyasa da ma al’umma. Idan za a iya tunawa dai, an rantsar da tsohon...
Aƙalla mutum huɗu suka rasu yayin da aka sace wasu tara a wani hari da ’yan bindiga suka kai a ƙauyuka da dama na Ƙaramar Hukumar Magama; ciki har da garin Ibeto a Jihar Neja. Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa mutum huɗu aka kashe, an jikkata wasu 11, sannan an yi garkuwa...
Collins mutum ne mai jajircewa da azama. Bayan gaza cin nasara da ya yi a ƙoƙarinsa na kafa tarihi a shekarar 2024, ya ɗauki tsawon shekara guda yana ɗaukar horo da shiri sosai domin wannan rana. Ya ce, “Na koyi darussa da dama daga ƙoƙarina na farko. Yanzu na shirya sosai. Tare da goyon bayan...
Adadin wadanda suka yi shahahda a yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke aiwatarwa kan al’ummar yankin zirin Gaza ya kai shahidai 66,148 da kuma jikkata wasu 168,716, tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Bisa kididdigar baya-bayan nan da ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta fitar, adadin wadanda suka yi shahada tun...
Aƙalla makarantu 188 na gwamnati aka rufe a Arewacin Najeriya sakamakon ta’azzarar matsalar tsaro. ’Yan bindiga sun kai wa wasu makarantun hari, yayin da wasu kuma yanzu ana amfani da su a matsayin mafakar ’yan gudun hijira ko sansanonin sojoji. Antoine Griezmann ya ci ƙwallo 200 a Atletico Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan...
Ɗalibi a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Collins Whitworth, ya yi ƙoƙarin karya tarihin Kundin Tarihi na Duniya, na zane a fuska mafi yawa cikin mintuna uku. Ɗalibin ya samu tallafi daga kamfanin da ke yin taliyar yara Indomie, inda ya yi zane a fuskar mutum 17 cikin mintuna uku, wanda hakan ya ba shi...
Fitaccen ɗan wasan gaban Atletico Madrid, Antoine Griezmann ya kafa tarihin zama na farko a ƙungiyar da ya ci mata ƙwallaye 200. Griezmann ɗan asalin Faransa ya kafa wannan tarihin ne a ranar Talata yayin Gasar Zakarun Turai, inda Atletico ta lallasa Eintracht Frankfurt ta Jamus da ci 5-1. Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake tallafawa...
Majiyoyin tsaro sun ce waɗannan hare-haren wani ɓangare ne na yunƙurin karya ƙarfin ’yan ta’adda da kuma katse hanyoyin samun kuɗaɗensu ta hanyar safarar miyagun ƙwayoyi, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma sata man fetur. Sun kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da ba da bayanai ga hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen...