Aminiya:
2025-10-13@20:24:30 GMT

Ba a ba mu dala 100,000 da gwamnati ta mana alƙawari ba — Super Falcons

Published: 14th, August 2025 GMT

Kyaftin ɗin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, Rasheedat Ajibade, ta ce har yanzu ba a ba su dala 100,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi musu alƙawari bayan sun lashe gasar WAFCON a ƙasar Maroko ba.

Ajibade, ta bayyana takaicinta game da jinkirin biyan kuɗin da aka musu alƙawari.

Amurka za ta sayar wa Najeriya makaman N530bn don yaƙi da ta’addanci ’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai

“Ba mu karɓi kuɗin ba tukunna, amma ina fata za a biya mu.

Duk alƙawuran da aka mana, yanzu dai ba mu samu komai ba.”

Ajibade ta jagoranci tawagar zuwa ga nasara, inda suka sake lashe kofin WAFCON a bana.

Bayan nasarar, Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ’yan wasan da masu horar da su lambar yabo ta ƙasa (Officer of the Order of Niger – OON).

Haka kuma ya yi musu alƙawarin bai wa kowannensu dalar Amurka 100,000 da gida mai ɗaki uku.

Lokacin da ya karɓe su a Fadar Shugaban Ƙasa, Tinubu ya yaba da jajircewarsu, da kuma ƙoƙarinsu, inda ya ce nasararsu ta ɗaga mutuncin Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan wasa Alƙawari Kyaftin Ƙwallon ƙafa WAFCON

এছাড়াও পড়ুন:

Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja

Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya sauke Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Ajao Adewale, daga muƙaminsa.

Ko da yake ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa aka sauke shi ba, majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa hakan ya faru ne sakamakon yadda rundunar Abuja, ta tafiyar da lamarin sanya gilishin mota mai duhu da kuma mutuwar ’yar jaridar gidan talabijin na Arise News.

Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi

Ɗaya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa waɗannan matsalolin guda biyu ne suka janyo sauya masa wajen aiki.

Ta ƙara da cewa za a tura Adewale wani waje daban, inda za a fi buƙatar ƙwarewarsa.

Da aka tambayi inda za a tura shi, majiyar ta ce Sufeton Janar na ’yan sanda ne zai bayyana hakan, tare da jaddada cewa Adewale ya yi iya bakin ƙoƙarinsa a matsayin kwamishina.

Kakakin rundunar ’yan sanda ta ƙasa, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da wannan sauyi, inda ya ce sauyin wajen aiki al’ada ce da ake yi domin inganta ayyukan jami’an rundunar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary ya lashe yankunan da Biya ke da rinjaye
  • ASUU ta tsunduma yajin aikin mako 2
  • Yajin Aikin ASUU:  Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya
  • Yaushe Lamine Yamal Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or?
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin
  • Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja
  • Daga Karshe Tawagar Super Eagles Ta Sauka A Uyo Bayan Saukar Gaggawa A Angola
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi  Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta
  • Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno