2025-09-17@23:12:49 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1786

«Mele Kyari»:

    Gwamnatin kasar China ta bayyana cewa ba zata taba amincewa a sake dorawa JMI takunkuman tattatalin arziki wadanda MDD ta dauke mata su a watan octoban da ya gabata ba. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China Lin yana fadar haka ya kuma kara da cewa kasashen...
    Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi a garin Potiskum a daren Juma’a zuwa safiyar yau Juma’a ya haifar da ambaliya, wanda ya haifar da tashin hankali ga mazauna garin.   Kamar yadda majiyar da ke garin ta shaidawa Aminiya cewa, ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka fara shi tun kusan tsakar...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a uau shiri wanda yake kawo mako labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakrwa , tsaro da sauransu. Sannan mu yi masu Karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a uau shiri wanda yake kawo mako labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakrwa , tsaro da sauransu. Sannan mu yi masu Karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane...
    A farkon wannan shekarar da ta gabata, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito Ministan Sufurin Ma’aikatar Jiragen Sama Festus Keyamo, a wani taro ya bai wa kungiyoyin na Sufurin Jiragen Sama tabbacin cewa, Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da bi ka’ida wajen sayar da hannun jarin Tashoshin Jiragen Saman kasa. Keyamo ya kuma bai wa shugabannin kungiyoyin...
    Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta bayyana cewa: Harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan gidan yarin Evin na Iran laifi ne na yaki Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta ce: Harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan gidan yarin Evin da ke birnin Tehran fadar mulkin...
    Gwamnatin Mali ta sanar da dakile wani shiri na hargitsa kasar tare da goyon bayan wata kasar waje Gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali ta sanar da cewa: Jami’an tsaro da na leken asiri sun dakile wani yunkuri na tada zaune tsaye a kasar, wanda sojoji da fararen hula da ke samun goyon bayan wata kasar...
    Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati ta Najeriya ta yaba wa Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa bisa nada Alhaji Muhammad K. Dagaceri a matsayin shugaban ma’aikata na jiha. Shugaban  ƙungiyar na kasa, kuma mataimakin shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa TUC, Kwamared Shehu Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya kai ziyara ga shugaban ma’aikata, Alhaji...
    A cikin jahohin da aka lissafa, Kebbi ce ta fi kowacce yawan garuruwa a jerin sunayen, inda take da garuruwa kusan 10 da suka hada da Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, da Birnin Kebbi. Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar gargadin samun ambaliyar ruwa ga jihohi 15 daga cikin 19 na Arewa....
    Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna kai hari ga daukacin al’ummar Falasdinu ne Babban sakataren kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi ya tabbatar da cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna kai hari kan dukkanin al’ummar Falastinu ne, yana mai jaddada cewa: Makiyan ‘yan sahayoniyya sun...
    Kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders ta sanar da cewa: Mutane 40 ne suka mutu a Sudan sakamakon barkewar cutar kwalara mafi muni cikin shekaru Kungiyar likitocin ba da agaji ta “Doctors Without Borders” ta sanar da mutuwar mutane 40 sakamakon kamuwa da cutar kwalara a Sudan cikin mako guda kacal, tare da tabbatar da...
    “Kowa ya sani wadatar abinci yana ɗaya daga cikin alamun da ke nuna kyautatawar tattalin arziki na ƙasa baki ɗaya, don haka ne muka himmatu wajen ba da namu gudunmawar ta wannan fannin.”   Ya kara da cewa, an kafa gidauniyar ne domin taimakawa a ɓangaren kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki wanda rabon takin na...
    Shugabar Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya cancanci yabo kan daidaita tattalin arzikin ƙasar nan da yake ci gaba da yi.  Okonjo-Iweala ta shaida wa manema labarai hakan ne ranar Alhamis bayan ta gana da shugaban ƙasar a Abuja. Motar tifa ta murƙushe ɗalibai biyu...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta kama wani Mai Unguwa mai shekara 55 a garin Zambuk da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, DSP Buhari Abdullahi ne ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya...
    Hukumar kula da kumbuna ta kasar Sin ta ce nan ba da jimawa ba, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 dake cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar, za su gudanar da zagaye na 3 na ayyuka a wajen cibiyar. ‘Yan sama jannatin 3 da suka hada da Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang Jie, sun...
    Wasu mutum biyu da ake zargin ɗaliban jami’a ne a Jihar Bayelsa sun mutu bayan wata mota ƙirar tifa ta murƙushe su lokacin da suke kan babur mai ƙafa uku a kan hanyar Tombia zuwa Ammassoma. Daily Trust ta samu rahoton cewa haɗarin wanda ya afku a ranar Talata, ya kuma sa wasu fasinjojin da...
    “Na zo Banga domin jajanta muku bisa wannan mummunan hari. Lokacin da abin ya faru bana nan, sai na umarci mataimakina ya jagoranci tawaga ta musamman domin yi muku ta’aziyya. “Na dawo Gusau jiya, kuma abu na farko da na fifita yau shi ne zuwa nan da kaina. Gwamnati za ta ƙara ƙoƙari wajen yaƙar...
    Kasar Iran ta jaddada wajabcin daukar kwararan matakai na kasa da kasa don dakile muradun gwamnatin mamaya na mulkin mallaka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Ismail Baqa’i ya yi Allah wadai da kalaman fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ake nema ruwa a jallo a kotun kasa da kasa ya yi dangane da abin da...
    Babban sakataren kungiya Hizbullahi ta kasar Lebanon ya karbi bakwancin Ali Larijani ya kuma godewa Iran bisa goyon bayan da take baiwa kasar Lebanon da ‘yan gwagwarmaya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Qassem ya gana da Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran da...
    Lauyan Maïga, Cheick Oumar Konaré, ya bayyana cewa kamun bai dace ba saboda Maïga ba shi da niyyar guduwa ko lalata shaidu, yana kuma zargin cewa wannan wani mataki ne na siyasa saboda tsohon Firaministan ya daɗe yana sukar gwamnatin soja tun bayan tsawaita mulkinsu ba tare da gudanar da zaɓe ba. Maïga, ya hau...
    Gwamnan ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta yi aiki tare da hukumomi masu ruwa da tsaki domin hanzarta shari’o’i da kuma rage cunkoson gidan yarin. A lokacin ziyarar, ya lura da cewa yawancin fursunonin na zaune a ƙasa babu katifa. Don inganta rayuwarsu, ya umarci a samar musu da katifu 500. Gwamna Sule...
    Akalla ’yan ci-rani 26 sun mutu bayan jiragen ruwan da suke ciki guda biyu sun nitse a teku a kusa da tsibirin Lampedusa na ƙasar Italiya. Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana hasashen ƙarin wasu mutanen kuma sun ɓace yayin da ake ci gaba da aikin ceto su....
    Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya ziyarci wasu garuruwa a Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda, bayan jerin hare-haren ’yan bindiga da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Gwamnan, ya la’anci kisan gillar, tare da bayyana shi a matsayin marasa imani, kuma Allah zai fallasa su ya kunyata su. Majalisar Zartaswa ta dakatar da ƙirƙirar...
    Muryoyi daga ko’ina cikin duniya sun nemi a warware matsalar bisa turbar adalci. Shugabannin tarayyar Turai sun yi ta kira ga kasashen Sin da Amurka da su kiyaye bude kasuwanni da gudanar da gasa ta gaskiya. Kasashen kudu maso gabashin Asiya, sun ba da shawarar tabbatar da kwanciyar hankali. Kasashen Afirka da na Latin Amurka...
    Tinubu ya yi kira da a sake duba kudaden gudanar da aikin NNPC da ake cire kashi 30 cikin 100 wanda doka ta tanadar a karkashin dokar masana’antar mai.   Shugaban ya bayyana godiya ga mambobin majalisar bisa jajircewarsu da aiki tukuru wajen aiwatar da gyare-gyare masu tsauri da wahala wadanda suka dabaibaye ci gaban...
    Jakadan kasar Irak a washintong ya bayyana cewa kasar Iraki entacciyar kasa she, tana da yencin kulla yarjeniyar tsaro da ko wace kasa da take so, wannan bayan korafin da gwamnatin Amurka tayi na yarjeniyar tsaro wacce kasar Iraki ta kulla da JMI. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jakadan yana cewa,...
    Ƙungiyar Ci Gaban Masarautar Jama’a (JEDA), ta roƙi Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, da ya kammala manyan titunan Birnin Kafanchan, wanda aikin ya tsaya tun zamanin Nasir El-Rufai. Muƙaddashin shugaban ƙungiyar, Ahmad Usman Husain, ya ce waɗannan tituna na da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziki da rayuwar yau da kullum a Kudancin Kaduna. Majalisar Kano...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da bikin makon shari’a na shekarar 2025 wanda ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen jihar Jigawa ya shirya, inda ya yi kira da a ƙara ƙarfafa bin ƙa’idojin aikin shari’a da hanzarta gudanar da shari’a a duk fadin jihar. A jawabinsa wajen bikin bude taron a Dutse, Gwamna Namadi ya...
    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da kyakkyawar alaka da kafafen yada labarai.   Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, da ‘yan majalisar zartaswar NUJ na kasa (NEC) da suka je Kano domin...
    Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU), Jami’ar Jihar Taraba Jalingo, ta bayar da wa’adin makonni biyu ga gwamna Agbu Kefas da shugabannin jami’ar da su gana da ita ko kuma ta shiga yajin aikin.   A cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron majalisar da aka gudanar a ranar 7 ga wata. Agusta 2025,...
    Biyo bayan wani rahoto da ma’aikatar lafiya ta tarayya ta fitar na cewa sama da likitoci 16,000 ne suka bar Najeriya a cikin shekaru bakwai da suka gabata domin neman aiki a wasu kasashe, gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na cike gurbin da likitocin suka haifar.   Da yake zantawa da manema...
    Gwamnatin Iraki ta bayyana cewa: Yarjejeniyar da Iran ta kulla da Iraki zata yi gagarumar amfani a fagen tsaron yankin Ofishin jakadancin Iraki a Amurka ya tabbatar da cewa: Iraki kasa ce mai cin gashin kanta kuma tana da hakkin kulla yarjejeniyoyin da kuma yarjejeniyar fahimtar juna. An yi nuni da cewa, yarjejeniyar tsaro da...
    Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja, ya yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kama Abubakar Abba, jagoran kungiyar Mahmuda, daya daga cikin manyan kungiyoyin ta’addanci da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi a Najeriya.   An ce an kama shi ne a Wawa da ke karamar hukumar Borgu ta Jihar...
    Sojojin Yemen sun sanar da cewa: Sun kai hari kan muhimman wurare hudu na haramtacciyar kasar Isra’ila da jirage marasa matuka guda shida Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Talata cewa: Sun kai farmakin soji ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka ciki guda shida, inda suka kai hari kan wasu muhimman wurare...
    Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya ce ranar Litinin ya ziyarci Shugaban Kasa Bola Tinubu, kuma sabanin yadda ake ta rade-radi, shugaban na nan cikin koshin lafiya kuma babu abin da ke damun shi. A ’yan kwanakin nan dai ana ta samun jita-jitar cewa shugaba Tinubu na can kwance magashiyyan yana fama da rashin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      A halin da ake ciki, EFCC ta yi Allah wadai da jam’iyyar ADC bisa zargin sanya siyasa a binciken da ta gudanar kan Tambuwal. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    Ana fargabar cewa wasu fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin Keffi da ke Jihar Nasarawa bayan wani kwantan bauna da suka yi wa gandirebobi. Wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali a Nijeriya, Umar Abubakar, ta ce fursunonin da ke gidan sun yi wa ma’aikatan da ke tsaronsu...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani basarake, Mohammed Tukur mai shekaru 55, a kauyen Sabon Gari da ke yankin Zambuk na Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa a halin yanzu ma’aikatarsa ce take kula da dukkan al-amuran da suka shafi shirin makamashin Nukliya na kasar, tun bayan da majalisar dokokin kasar ta bukaci a jingine aiki da hukumar makamashin Nuikliya ta Duniya IAEA bayan yakin kwanaki 12 da HKI da Amurka suka...
    Sun fara soyayya ba da jimawa ba, inda suka fito fili suka bayyana alakar dake tsakaninsu a shekarar 2017, masoyan sun haifi yarsu ta farko, Alana, a watan Nuwamba na shekarar 2017, daga nan suka haifi tagwaye, Bella da Angel, a watan Afrilun 2022, amma jim kadan da haihuwarsu Angel ya rasu, Georgina ta kuma...
    Ministan harkokin wajen kasar Iraki ya ba da shawarar gudanar da taron kasashen Larabawan yankin tekun Pasha da Iraki da kuma Iran Ministan harkokin wajen kasar Iraki Fuad Hussein ya gabatar da shawarar gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Iraki, Iran, da kuma kasashen larabawan yankin Gulf, a tsarin na 6+2, a gefen taron...
    ‘Yan Democrats a Amurka sun zargi Donald Trump da mutumin da giyar mulki ke ruɗawa, bayan ya ce zai tura jami’an rundunar tsaro ta ƙasar birnin Washington don yaƙi da laifukan da ake ganin sun gagari ƴansandan birnin. Magajiyar birnin Muriel Bowser, ta ce matakin bai dace ba, sannan ta musanta batun da shugaban ke...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wasu mutane biyu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne tare da kwato musu wasu abubuwa na bata gari a Ilorin.   A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Adetoun Ejinre-Adeyemi ya fitar, ya ce, ‘yan sandan da ke aiki bisa sahihiyar...
    Yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Taraba, da kungiyar Kwadago (TUC) reshen jihar Taraba suka kaddamar a ranar Litinin da ta gabata, ya gurgunta ayyukan gwamnati a ma’aikatu da hukumomin gwamnati a jihar.   Matakin wanda ya fara da tsakar daren litinin, ya kasance tare da hadin gwiwar shugabannin...
    Sai dai wasu daga cikin hadiman shugaban kamar Abdulaziz Abdulaziz, mai taimaka masa a kafafen watsa labaru, ya ce labarin ba gaskiya ba ne. Batun rashin lafiyar Tinubu ba sabon abu ne, domin tun yana yaƙin neman zaɓen takara a 2023 ake kai ruwa rana kan batun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Kasashen Iran da Iraki sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro ta hadin gwiwa a wannan  Litinin, dangane da tabbatar da tsaron kan iyakokin kasashen biyu, a ziyarar da babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya kai kasar Iraki. Larijani da mai baiwa gwamnatin Iraki shawara kan harkokin tsaro, Qasim al-Araji,...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa a gobe talata mataimakin shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya zai ziyarci kasar, amma ba tare da zuwa cibiyoyin nukliya na kasar ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne ziyarar aiki na farko wanda wani jami’in hukumar ya...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shawarci matasan da ake ribatarsu a matsayin ’yan daban siyasa da suka tuba da su guji tashin hankali, yana tabbatar musu da shirye-shiryen gwamnatinsa na gyara tarbiyarsu tare da mayar da su cikin al’umma. Gwamnan ya yi wannan alkawari ne a taron wuni ɗaya da aka gudanar tare da...