Kungiyar Human Righs Watch Ta Yi Tsokaci Kan Shirin Trump Na Batun Tsagaita Bude Wuta A Gaza
Published: 6th, October 2025 GMT
Shirin shugaban Amurka kan rikicin Gaza bai yi magana ba game da daurawa ‘yan mamaya alhakin take hakkin dan adam ba
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta yi kira ga kasashe da su dauki matakin dakatar da cin zarafi da ake yi wa fararen hula a Gaza, inda ta yi nuni da cewa shirin shugaban Amurka Donald Trump bai yi magana kai tsaye kan batun kare hakkin bil adama.
Kungiyar ta ce shirin na Trump bai yi magana kai tsaye kan batutuwan da suka shafi kare hakkin bil’adama da kuma daukar nauyin laifuffukan da aka aikata tun daga ranar 7 ga watan Oktoba ba, tana mai cewa sojojin mamayar Isra’ila sun kashe dubun-dubatar Falasdinawan da galibinsu fararen hula ne, tare da hallaka iyalai masu yawa.
Human Rights Watch ta kara da cewa: ‘Yan sahayoniyya sun haddasa yunwa ta hanyar amfani da yunwa a matsayin makamin yaki tare da tilastawa kusan daukacin al’ummar Falasdinu barin muhallansu.
Kungiyar ta yi nuni da cewa: Hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai ya mayar da mafi yawan yankin zirin Gaza baraguzan gine-gine, tare da ruguza yankuna da garuruwa, sannan sojojin mamayar Isra’ila na kashe dimbin kananan yara ‘yan makaranta a kowace rana.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta jaddada cewa: Bai kamata gwamnatoci su jira amincewa da shirin Trump na daukar matakin hana afkuwar barna a Gaza ba, tana mai kiran da a matsa lamba ga haramtacciyar kasar Isra’ila da ta dage haramtacce matakin hana shigar da kayan agaji cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hukumar Samar Da Abinci Ta MDD Ta Yi Gargadin Rage Tallafin Jin Kai A Kasar Somaliya October 6, 2025 Janar Pakpour: Duk wani shishigi a kan Iran zai fuskanci martani mai tsanani October 6, 2025 Iran na goyan bayan duk wani shiri da zai samar da ‘yancin Falasdinawa October 6, 2025 Babban mai shiga tsakanin na Hamas ya isa Masar domin tattaunawa da Isra’ila October 6, 2025 Rahoto: A cikin shekaru biyu Isra’ila ta jefa tan 200,000 na bama-bamai a Gaza October 6, 2025 Gidauniyar Mandela ta yi tir da Isra’ila kan dakile ayyukan jin kai zuwa Gaza October 6, 2025 Afirka Ta Kudu Ta Aike Da Tawagar Bincken Musabbabin Mutuwar Jakadanta A Birnin Paris October 5, 2025 Iran: Kungiyar Kwallon Raga Ta Mata Ta Ci Kofin Asiya October 5, 2025 HKI Ta Kwace Kudin Gwamnatin Faladinu Dala Miliyan 7.5 Ta Rabawa Wasu Iyalan Yahudawa 41 October 5, 2025 Sojojin Sudan Sun Zargi Rundunar “RSF” Da Kai Hari Akan Cibiyoyin Fararen Hula October 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kare hakkin bil adama
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
Daga Usman Muhammad Zaria
Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba, ya aiwatar da wani aiki na da naira miliyan biyar domin tallafa wa aiwatar da Shirin Tallafawa Yara Mata (AGILE) a yankin.
Aikin ya hada da gyaran ajujuwa biyu da samar da muhimman kayan aiki, ciki har da injunan dinki, injin yin surfani wato (monogram) da shirin AGILE ya bayar kyauta wanda Dr. Uba ya shirya, ya taimaka wajen ganin an fara amfani da shi, tare da samar da janareta da tabarmi domin inganta koyarwa da horo.
Wannan ci gaban ya biyo bayan wani bincike da tawagar AGILE ta jihar Jigawa ta gudanar a baya, inda ta bayyana cewa wuraren koyon sana’o’in na bukatar gyara.
Shirin AGILE, wani shiri ne na Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Jigawa, wanda aka ƙirƙira domin bai wa matasa mata ƙwarewar da za su dogara da kansu, inda ake sa ran mutum 50 za su amfana a horon da ke tafe.
A lokacin ƙaddamar da aikin, Mai kula da shirin AGILE a Birnin Kudu, Hajiya Maryam Hassan Jibrin, ta yaba da jajircewar Dr. Builder Uba ga ci gaban al’umma, tana jinjinawa kokarinsa tare da yi masa addu’ar ci gaba da jagoranci mai tasiri.
Da yake tabbatar da jajircewar gwamnatinsa wajen ci gaban matasa, Muhammad Uba ya yi alƙawarin bayar da gagarumin tallafi ga mahalarta bayan kammala shirin cikin nasara.