The Guardian: Isra’ila ta azabtar da Greta Thunberg ‘yar kasar Sweden mai fafutuka
Published: 5th, October 2025 GMT
Jaridar The Guardian ta Burtaniya ta tabbatar da cewa ofishin jakadancin Sweden da ke Isra’ila ya sanar da ma’aikatar harkokin wajen kasar a Stockholm cewa Greta Thunberg ta fuskanci munanan yanayi a lokacin da take tsare.
Jaridar ta bayyana cewa an ajiye Thunberg a cikin wani daki mai kazanta, inda ta yi fama da kurji da bushewar fata, kuma an hana ta isasshen ruwa da abinci.
Jaridar ta ruwaito wata mai fafutuka ta Sweden tana cewa ta ga “masu tambayoyi suna tilasta mata (Thunberg) ta daga tutar Isra’ila.”
Wani mai fafutuka ya kuma ce, “Sun ja gashin Greta, suka yi mata duka, kuma suka tilasta mata sumbatar tutar Isra’ila,” ya kara da cewa sun yi duk abin da za su yi na cin zarafi a kanta a matsayin gargadi ga wasu.
Wani mai fafutuka ya ba da rahoton cewa “sun nannade Greta a cikin tutar Isra’ila tare da nuna ta kamar kofin gasa.”
Dakarun mamaya na Isra’ila sun kama ‘yar gwagwarmayar Sweden Greta Thunberg da wasu masu fafutuka daga kasashe daban-daban a lokacin da suke cikin jirgin “Global Resilience Flotilla”, wanda ya tashi don karya shinge da killacewar da aka yi wa Gaza, bayan harin da Isra’ila ta kai wa jiragen Ruwan da suke dauke da su.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta bukaci a haramtawa Isra’ila shiga harkokin wasanni na duniya October 5, 2025 Sheikh Qassem: Falasdinawa ne suke da hakkin yanke shawara kan makomar Gaza October 5, 2025 An yi gagarimar zanga zangar goyan bayan Falasdinu a Barcelona, Rome, da Paris October 5, 2025 Malawi : Mutharika ya yi rantsuwar kama aiki October 5, 2025 Hamas: Ci gaba da kai hari kan Gaza ya fallasa karyar Netanyahu October 5, 2025 Sojojin HKI Sun Bada Sanarwan Fara Aiwatar Da Shirin Trump Na Tsagaita Wuta A Gaza October 4, 2025 Janar Qa’ani: An Boye Ranar Fara Yakin Tufanul Aksa Har Haniyya Bai Da Labarisa October 4, 2025 Iran Na Shirin Cilla Tauraron Dan’adam Da Sandarerren Makamashi A Cibiyar Chabahar October 4, 2025 Iran: Gasar Fasahar Kere-kere Na Shekara Ta 2025 Zai Sami Halattar Wakilai Daga Kasashe 65 October 4, 2025 Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 146 October 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Isa Chiroma Mafaka Ta Wucin Gagi
Gwamnatin kasar ta Gambia ta sanar da bai wa jagoran ‘yan hamayyar kasar ta Kamaru Isa Chiroma mafaka bisa dalilai na “‘yan adamtaka”.
A wani bayani da ma’aikatar harkokin waje ta kasar Gambia ta fitar, ta bayyana cewa; Chiroma dan shekaru 76 ya isa babban birnin kasar Panjul a ranar 27 ga watan Febrairu a karkashin wata yarjejeniya da aka cimmawa a tsakanin kasashen yankin domin lalubo hanyar warware takaddamar siyasar da kasar Kamaru take fama da ita.
Tun bayan da Chiroma ya fice daga kasar ta Kamaru, ya nufi kasar Najeriya, mahukunta a kasar tasa suke kiran da a kama shi.
Sai dai maimakon haka, gwamnatin kasar ta Najeriya ta cimma matsaya da mahukuntan kasar Gambia akan a bai wa Chiroma din mafaka a can bisa sharadin cewa ba zai rika gudanar da wasu ayyuka na siyasa ba.
Tun bayan zaben shugaban kasa ne dai kasar ta Kamaru ta fada cikin dambaruwar siyasa wacce ta kai ga dakatar da harkokin yau da kullum a cikin manyan birane. Dan takarar jam’iyar Adawa, Isa Chiroma ya riya cewa shi ne ya lashe zaben, tare da zargin hukumar zabe da yin magudi saboda bai wa Paul Biya damar ci gaba da zama akan kujerar mulki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makaamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin November 25, 2025 An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci