2025-05-24@01:41:41 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1054

«Hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya»:

    Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta na wata guda a yaƙin da ta shafe shekaru uku tana fafatawa da kasar Rasha. Matakin na zuwa ne bayan tattaunawar da wakilan ƙasar ke ci gaba da yi yanzu haka da Amurka a birnin Jedda na Saudiya. Matashin da ke ƙera jiragen sama da bindigogi daga robobi...
    Ukraine ta amince da kudurin tsagaita wuta na wata guda a yaƙin da ta shafe shekaru uku tana fafatawa da kasar Rasha. Matakin na zuwa ne bayan tattaunawar da wakilan ƙasar ke ci gaba da yi yanzu haka da Amurka a birnin Jedda na Saudiya. Matashin da ke ƙera jiragen sama da bindigogi daga robobi...
    Alamomin cutar sun haɗa da ciwon kai mai tsanani, ciwon wuya, tari, da amai. Yaɗuwar cutar a Kebbi na iya shafar sauran jihohin da ke maƙwabtaka da ita, musamman Zamfara, Sakkwato, da Neja, inda ake yawan tafiye-tafiye tsakanin jihohin. Hakan na nuni da buƙatar gaggauta ɗaukar matakan kariya don hana cutar yaɗuwa zuwa sauran yankuna....
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba...
    Kungiyar tarayyar turai ta jaddada bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomatsiyya. Da taek sanar da hakan babbar Jami’ar kula da harkokin ketare ta kungiyar ta ce babu wata hanyar da za’a bi wajen warware matsalar Iran in ba ta diflomasiyya ba. ‘’ta hanyar diflomatsiyya ne za’a warware takaddamar da ake game da batun yarjejeniyar...
    Tare da cewa Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki fiye da 60 da Ukiraniya ta harba, sai dai an sanar da mutuwar mutum daya a birnin Moscow. Kantoman yankin Moscow  Andrey Vorobyov ne ya sanar da cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu 3 su ka jikkata, sanadiyyar hare-haren da...
    Hukumar da take fada da yi wa tattalin arzikin kasar Najeriya ta’annatii ta kwato da kudaden da sun kusa dalar Amurka miliyan 500. Haka nan kuma hukumar ta kwato man fetur da  sauran dangoginsa da sun kai  ton 931,000, sai kuma gidajen da sun kai 975. A cikin rahoton da ta fitar a ranar litinin...
    Kimanin fararen hula 1,000 ne aka kashe tare da jikkata wasu daruruwa a hare-haren jiragen yaki marasa matuki a nahiyar Afirka, yayin da ake ci gaba da yin amfani da jirage marasa matuka a nahiyar. A cewar jaridar The Guardian, masu sharhi da nazari na cewa , daga shekara ta 2021 zuwa 2024, jami’an tsaro...
    Wani babban jami’in ‘yan sanda a jihar Uttar Pradesh ta Indiya ya bukaci musulmi da su yi sallar Juma’a a gida. A cewar radiyon gwamnatin Pakistan, Firimiyan Jihar Uttar Pradesh Yogi Adityanath ya kare kalaman jami’in ‘yan sandan game da musulmi, inda ya ce, “A yayin da ake gudanar da bukukuwan Holi sau daya a...
    Majalisar Dinkin Duniya, ta yi tir da matakin Isra’ila na kate wutar lantarki a Gaza, tana mai matukar gargadi game da ilan da hakan zai janyo wa Zirin. Matakin da Isra’ila ta dauka na katse wutar lantarki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya zai hana yankin Falasdinawa samun “ruwa mai tsafta,” in ji...
    Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya isa kasar Saudiyya domin ganawa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, gabanin wata muhimmiyar ganawa tsakanin tawagogin Ukraine da na Amurka domin share fagen shawarwarin zaman lafiya da Rasha a nan gaba. Taron dai na nuni da wani gagarumin yunkurin diflomasiyya na magance rikicin da ke faruwa...
    Shugaban kasar Ghana, John Darmani Mahama ya nemi kungiyar Ecowas da ta amince da kungiyar kawancen kasashen Sahel din nan guda uku da suka balle daga cikinta. Mista Mahama, ya bayyana hakan a kafofin sada zumunta a ranar Litini jim kadan gabanin ya ziyarci kasar Burkina faso, bayan ya kai irin wanan ziyara kasashen Mali...
    ’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 14 yayin wani hari da suka kai yankuna huɗu a Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa da ke Jihar Ondo. Yankunan da abin ya shafa — Aba Alajido, Aba Sunday, Aba Pastor da Ademekun— galibi mazaunansu ƙananan manoma ne. Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano Yadda za a samu...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce shirin makamashin Nukliyar kasar Iran, na zaman lafiya ne, kuma babu wani shiri na samar da makaman Nukliya a cikinsa, sannan ya kara da cewa Iran ba za ta taba shiga tattaunawa da kasar Amurka mai cin zalin wasu kasashe ba. Kamfanin dillancin labaran IP na...
    Manya-manyan Jiragen ruwan yaki na kasashen Rasha da China sun isa tashar Jeragen ruwa ta Chabahar dake kudu maso gabacin kasar Iran a bakin tekun india don fara atisayen soje a tsakanin kasashen uku, wanda aka sanyawa suna ‘damarar tsaro na shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan...
    Yau Litinin, aka rufe taro na 3 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 14 a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran manyan jami’an gwamnati da jami’yyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, sun halarci taron. A gun bikin rufe taron, an zartas...
    Jam’iyyar APC ta yi kira ga Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi. Shugaban APC na Jihar Ribas, Tony Okocha ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau Litinin a birnin Fatakwal. An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa Abin da ya sa...
    Shugabana kasar Ghana John Dramani Mahama, ya ziyarci kasashen Mali da Nijar a wani bangare na ran gadin diflomatsiyya da ya fara a kasashen sahel din nan uku da suka balle daga kungiyar Ecowas. Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu...
    Kasar Qatar ta bukaci hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa da ta sanya ido kan cibiyoyin nukiliyar Isra’ila. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta bayyana cewa, Doha ta bukaci hukumar ta (IAEA) da ta sanya damar gudanar da bincike da ka’ida daga hukumar ta MDD, kan...
    Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce manufar Iran ta ginu ne kan  samar da hadin kai a yammacin Asiya, kamar yadda kuma ta yi imanin cewa duk wani rikici da tashin hankali a yankin to zai illata kowa. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da Firaministan Norway Jonas Gahr Støre a...
    Rahotanni daga kasar Syria na cewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Jableh da ke yankin Latakia na kasar Siriya a karon farko a daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya ta kasar ta shaida wa Al Mayadeen. Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya sun  zagaya a unguwannin Jableh, inda suka duba shaguna da...
    A yayin bikin Ranar Mata ta Duniya, Hajiya Sa’adatu Ali Isa JC, matar Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Balanga da Billiri, ta tallafa wa mata 150 da injinan markaɗe domin su samu hanyar dogaro da kai. Da ta ke jawabi yayin rabon kayan, Hajiya Sa’adatu ta ce manufar wannan tallafi ita ce taimaka wa mata...
    Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Iran ta zauna teburin tattaunawa da gwamnatin Amurka alhali tana yi ma ta barazana. Har ila yau ya ce zancen bayan nan na shugaban kasar Amurkan akan tattaunawa manufarsa ita ce yaudara da kuma kokarin raba Iran da...
    Isyaku Mahmud, makaho ne dan shekara 28 da ke sana’ar sayar da data a yankin Kudancin Kaduna. Ya shaida wa Aminiya cewa har sana’ar hada-hadar kudi ta POS yana yi a baya, amma yanzu ba shi da jari. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai...
    Abin da ya sa wannan tsari ya yi daban shi ne ba wai domin irin tsarin gine-gine da za a yi ba; akwai allunan batun siyasa da kuma ‘yancin Falasdinawa. A jawabinsa a wajen taron, shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya yi kira da a samar da tsare-tsare guda biyu da za su tafi lokaci...
    Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar da fara atisayen sojan ruwa na hadin gwiwa da kasashen Rasha da Iran, wanda za a ci gaba da gudanarwa har zuwa mako mai zuwa a kusa da tashar ruwa ta Chabahar  ta kasar Iran. Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar a yau Lahadi cewa, kasashen Sin, Rasha da...
    Manyan kasashen Turai, da suka hada da Burtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya, sun goyi bayan shawarar Masar na sake gina Gaza a matsayin mai adawa da shirin “riviera” na shugaban Amurka Donald Trump wanda ke ba da shawarar korar Falasdinawa da karfi daga yankin. Duk da goyon bayansu da kuma wanke ayyukan kisan kare dangi...
    Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta naɗa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu...
    Hakan ya sa yanzu ba kasafai masu shirya fina finan Hausa ke mayar da adadin abinda su ka kashe wajen shirya fim ba, don kuwa ba kowane yake da yawan mabiyan da za su kalli abinda ya dora a YouTube ba da har zai samu wani abin kirki, hakazalika gidajen Talabijin da ke saye ba...
    A dai dai lokacinda ake bukukuwan ranar mata ta duniya kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, ta yi allawadi da HKI saboda kissan mata kimani 12.000 a gaza a cikin yakin tufanul Aksa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar Hamas na fadar haka a yau Asabar, ta kuma kara da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-hare a kan cibiyoyin makamashin Nukliyar kasar ba zasu dakatar da ayyuka a cibiyoyin ba. Sai dai yin haka zai kara yada yaki a yankin kudancin Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana cewa cibiyoyin nukliya na kasar Iran suna...
    Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Nijeriya, NMDPRA, ta bayar da lasisin kafa sabbin matatun man fetur uku a wasu jihohin ƙasar uku. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar, wadda shugabanta, Farouk Ahmed ya bayyana ta nuna. Dalilin...
    Majaliar Dattawa ta ce ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ne saboda saɓa dokokin majalisar da ta yi, ba don zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar ba. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Bamidele Opeyemi ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a madadin majalisar. Kotu ta saki...
    Kasashen Iran da kuma Iraki sun nuna damuwa kan tashe tashen hankulan dake faruwa a Siriya. A wata sanarwa da ta fita ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana matukar damuwarta kan yadda tashe-tashen hankulan da ke yaduwa a fadin kasar ta Siriya, tana mai gargadin cewa, wannan yanayi mara kyau zai share fagen rashin...
    Jagoran kungiyar Ansar Allah ta kasar Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya baiwa masu shiga tsakani wa’adin kwanaki hudu na tabbatar da shigar da kayayyakin jin kai a Gaza, yana mai gargadin cewa idan har Isra’ila ta ci gaba da toshe hanyoyin kai kayan agaji a Gaza, to dakarun Yemen za su ci gaba da kai...
    Gwamnatin tarayya ta nuna damuwarta kan cewa kasar nan ta yi asarar tiriliyoyin naira sakamakon ayyukan masu hakar ma’adanai ta barauniyar hanyoyi musamman a jihohi. Gwamnatin ta kuma cafke da gurfanar da ‘yan kasan waje su hudu wadanda suka shiga harkar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, yayin da wasu mutane 320 kuma aka cafke kan...
    Alake ya bayyana cewa majalisar zartarwar ta amince da wani sabon shiri na inganta tsari da kuma dakile asarar kudaden shiga a fannin ma’adinai. A wani bangare na shirin, ya ce gwamnati za ta tura fasahar tauraron Dan’adam don sa ido kan muhimman wuraren hakar ma’adinai da kuma bin diddigin ayyukan ma’adani. Alake ya kara...
    Shugaba Zelensky   na Ukiraniya zai kai ziyara kasar Saudiyya a ranar Litinin, gabanin bude tattaunawar da za a yi tsakanin kasarsa da kuma Amurka da zummar kawo karshen yaki da Rasha. Shugaban na kasar Ukiraniya ya wallafa wani sako a shafinsa na X cewa; Manufar ziyarar tashi ita ce haduwa da yarima mai jiran gado...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa; Tattaunawa da Amurka kaskanci ne, ga shi kuwa al’ummar Iran tana da tunani ne irin na Ashura, ba ta karbar kaskanci. Limamin na Tehran ya yi ishara da yadda duniya ta ga yadda Donald Trump ya wulakanta shugaban kasar Ukiraniya, don haka ya kamata...
    Shuwagabannin kasashen Turai, sun amince da kara kudade mai yawa a bnaren tsaro da kuma tallafawa kasar Ukraine, a yakin da take yi da kasar Rasha, saboda janyewar Amurka dukkan taimakon da take bawa kasar ta Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar taron shuwagabannin kasashen na Turai, sun zuba kudade...
    Kungiyar ta yi tir da tsarin da hukumar kulawa wutar lantarki ta yi,wanda take neman ta ba masu amfani da wuta, nau’i- nau’in da suke ko ta kai su,ba domin komai ba don wata magana ta kara bunkasa samun wutar lantarki fiye da irin halin da ake ciki yanzu. Kamar dai yadda kungiyar tace tsarin...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi watsi da zarge-zargen da jami’an Birtaniya suka yi na cewa Tehran na barazana ga tsaron kasar ta Burtaniya. A cewar jami’an Iran, Ingila na zargin Iran da wani abu da ta yi fice a kai. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya mayar da martani da kakkausan lafazi...
    Wani nazari da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar, wanda mutane 15,257 daga fadin kasashe 38 suka bayar da amsa, ya bayyana cewa manufar sanya muradun Amurka gaba da komai tana da mummunan tasiri kan dangantakar Amurkar da Turai, yayin da adadin wadanda suka aminta da Amurka daga kasashe kawayenta daga cikin masu bayar...
    Har ila yau, jim kadan bayan ficewar Zelenskyy daga Washington, shugabannin kasashen Turai da suka hada da na Jamus da Faransa da Italiya da kuma Birtaniya suka yi gaggawar mara masa baya, yayin da wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka suka yi kakkausar suka ga Ukraine wanda a cewar Sanata Lindsey Graham na jam’iyyar Republican ta...
    Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, FRCN Kaduna Chapel, ta jaddada kudirinta na inganta jin dadin mambobinta ta hanyar bullo da sabbin tsare-tsare da shirye-shiryen tallafi. Shugaban kungiyar, Kwamared Umar Adamu Sarikin Fada ne ya bayyana haka a lokacin rabon kayan abinci na Ramadan ga ‘yan kungiyar a Kaduna. Umar Adamu Sarikin Fada ya bayyana...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Bakai, ya ce, Iran tana kokarin ganin cewa an gudanar da taron kungiyar kasashen musulmi domin tattauna batun barazanar tilasta mutanen Gaza yin hijira. Haka nan kuma ya ce, wannan tunanin na korar falasdinawa daga Gaza, ba wani abu ba ne sai cigaba da kisan kiyashi, ta hanyar amfani...
    Jaridar Telegraph da ake bugawa a Birtaniya ta buga wata kasida da a ciki ta bayyana  zancen aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya a matsayin abin dariya wanda yake son komawa da gaske bayan da ya kasance abin dariya. Marubuciyar wannan kasida Allison Pearson ta ce ba a taba yin wani lokaci da fira ministan...
    Wakilin ɗan wasan, Jorge Mendes, ne ya tabbatar da batun sabon kwantiragin, yana mai cewa, duba da yadda Yamal ke taka leda a halin yanzu, yana da muhimmanci ya ci gaba da kasancewa tare da Barcelona. Ƙungiyoyi da dama sun nuna sha’awar ɗaukar Yamal, amma Barcelona ta dage cewa ba za ta bari ya bar...
    A wani yunkuri na bunkasa sana’o’in hannu da kuma karfafa wa masu bukata ta musamman, wata kungiya mai zaman kanta mai suna Women Farmers Advancement Network (WOFAN) ta kaddamar da wata cibiyar kasuwanci ta mata masu sarrafa kayayyaki tare da baiwa masu bukatar su 450 a yankin Karfi. Wannan yunƙurin na da nufin ƙarfafa su...