2025-09-18@01:08:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1926
«Hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya»:
Sarkin Zuru na Jihar Kebbi, ritaya Manjo-Janar Muhammadu Sani Sami, ya rasu yana da shekaru 81 a duniya. Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Kebbi, Garba Umar-Dutsinmari, ne ya tabbatar da rasuwar mai martaba a cikin wata sanarwa da aka fitar a Birnin Kebbi ranar Lahadi. Ya bayyana cewa Sarkin ya rasu ne...
Mutum sama da 600 sun rasa matsuguni sanadiyyar wata mummunar ambaliya da ta afku a garin Potiskum da ke Jihar Yobe. Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta bayyana cewa kimanin mutane 612 ne ta samarwa matsuguni bayan ambaliyar ruwa ta mamaye sama da gidaje 102 a garin Potiskum. Wannan ambaliya ta afku...
Jakadan Iran a Saudiyya Alireza Enayati ya tabbatar da ci gaba da tuntubar juna tsakanin babban hafsan hafsoshin sojin Iran da ministan tsaron Saudiyya. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na IRNA Alireza Enayati ya yi nuni da cewa, Saudiyya na kallon alakar ta da Iran a matsayin alaka mai matukar muhimamnci, kamar yadda...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Suna godiya ga Iraki saboda karimcin da ta yi wa masu ziyarar Arba’een na Imam Husain {a.s} Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yaba da kokarin gwamnati da al’ummar Iraki wajen karbar bakwancin masu ziyarar juyayin Arba’een na Imam Husaini {a.s}. A yayin da yake...
A wasu yankunan Jihar Katsina da suka daɗe cikin fargaba da hare-haren ’yan bindiga, zaman lafiya ya fara dawowa sakamakon sulhu da al’umma suka yi da masu tayar da ƙayar baya. Wannan sulhu, wanda ba a haɗa gwamnati ba, ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu cikin daminar bana. Manoma sun fara noma cikin...
Wani babban jami’in diflomasiyyar Iran ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai da kuma kare hakkinta na nukiliya cikin lumana. Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da tashar dillancin labaran Turkiyya, a lokacin da...
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi a garin Potiskum a daren Juma’a zuwa safiyar yau Juma’a ya haifar da ambaliya, wanda ya haifar da tashin hankali ga mazauna garin. Kamar yadda majiyar da ke garin ta shaidawa Aminiya cewa, ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka fara shi tun kusan tsakar...
“Sama da yara miliyan 10.1 ne ba su kai makaranta, kashi 70 masu zuwa makarantar kuma ba su da dabarun koyo, kuma fiye da kashi 60 na malaman firamare na gwamnati ba su da ilimin dijital,” in ji ta Da take yaba wa gwamnatin Koriya ta Arewa bisa tallafin da ta samu ta hannun hukumar...
“Manufar ita ce a ninka adadin likitoci, ma’aikatan jinya, masu hada magunguna, kwararrun dakunan gwaje-gwaje da sauran kwararru a fannin kiwon lafiya. Wannan ko shakka babu zai kara habaka harkokin kiwon lafiya a kasar,” in ji shi. Tsohon gwamnan Jihar Katsinan ya bayyana cewa, a bana, TETFund ta samu tallafinta mafi girma na Naira Tiriliyan...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja domin ziyarar aiki zuwa ƙasashen Japan da Brazil. Ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 11:15 na safiyar Juma’a, inda zai tsaya a Birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Matsalar ƙofa ta hana fasinjoji 58 hawa jirgin Abuja zuwa Landan Matsalar tsaro...
Wata kotun tarayya a kasar Kanada ta ayyana manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci yayin da ta hana wani tsohon dan siyasa, Douglas Egharevba, mafaka a kasar saboda alakarsa da jam’iyyun. Jaridar Peoples Gazette ta rawaito cewa alkalin kotun, Phuong Ngo, a hukuncin da ta yanke ranar 17 ga watan...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Suna buƙatar kawar da makaman nukiliya da kuma kawo ƙarshen maganganun rashin jin daɗi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya yi kira da a dauki matakin gaggawa kan kawar da makaman nukiliya da kuma amincewa da laifukan tarihi a hukumance kamar harin bam din da...
Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da miƙa wa mataimakinsa, Malam Faruk Jobe, ragamar mulkin jihar, inda shi kuma zai tafi hutun mako uku domin duba lafiyarsa. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Salisu Zango, ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar ta bayyana cewa hutun zai fara...
A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan...
A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan...
“Kowa ya sani wadatar abinci yana ɗaya daga cikin alamun da ke nuna kyautatawar tattalin arziki na ƙasa baki ɗaya, don haka ne muka himmatu wajen ba da namu gudunmawar ta wannan fannin.” Ya kara da cewa, an kafa gidauniyar ne domin taimakawa a ɓangaren kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki wanda rabon takin na...
Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen Sayyeed Abdulmalik Badruddeen Huthi , a jawabinsa na mako-mako da ya saba gabatarwa, dangane da Falasdinu da kuma sabbin al-amura da suka faru ko suke faruwa a yankin da kuma duniya gaba daya ya tabo al-amura da dama. Tashar talabijin ta Al-Alam wacce take watsa shirye shiryenta da harshen...
A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan...
Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ), ta ce rahotannin da ake yaɗawa cewar ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji, ya miƙa wuya ba gaskiya ba ne. Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye ne, ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Alhamis yayin bayani kan ayyukan sojoji. Rashin Lantarki: Babu...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Furucin Netanyahu Game Da Kafa “Babbar Kasar Isra’ila’
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi tsokaci kan furucin Netanyahu game da kafa ‘Babban Kasar Isra’ila’ Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana a safiyar yau alhamis cewa: Kafafen yada labaran yammacin duniya a al’ada na zargin duk wanda ya ambaci ra’ayin ‘yan sahayoniyya na kafa “Babban kasar Isra’ila” da kiyayya ga wata...
Akalla ’yan ci-rani 26 sun mutu bayan jiragen ruwan da suke ciki guda biyu sun nitse a teku a kusa da tsibirin Lampedusa na ƙasar Italiya. Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana hasashen ƙarin wasu mutanen kuma sun ɓace yayin da ake ci gaba da aikin ceto su....
Masar ta yi Allawadai da kalaman Benjamin Netanyahu game da abin da ya kira shirinsa na kafa babbar kasar yahudawa ko kuma Isra’ila Babba. Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar, bayan da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi magana kan wanann batu, wanda ya tayar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da kara wayar da kan direbobi da fasinjoji da Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta ce tana yi, ana kara samun ƙaruwar wadanda ke rasa rayukansu sakamakon hadura a titunan kasar nan. A shafinta na internet, FRSC ta ce a watanni uku na farkon 2024, mutane...
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta dakatar da Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano, Muhammad Nazir Yau, na tsawon wata uku domin gudanar da bincike kan zargin yin amfani da kujerarsa ba bisa ƙa’ida ba. Kansilolinsa sun zarge shi da karkatar da kayayyaki da kuma almundahana wajen tafiyar da dukiyar jama’a. Kullum a Kamaru muke kwana, mu yini...
An yi kira ga kwararrun kafafen yada labarai da su tabbatar da madogararsu domin tabbatar da samar da kyakykyawan rahoton abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma. Babban Limamin Masallacin Al-Waheed Central, Imam Mustapha Luqman ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa da kungiyar ‘yan jarida...
Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU), Jami’ar Jihar Taraba Jalingo, ta bayar da wa’adin makonni biyu ga gwamna Agbu Kefas da shugabannin jami’ar da su gana da ita ko kuma ta shiga yajin aikin. A cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron majalisar da aka gudanar a ranar 7 ga wata. Agusta 2025,...
Gwamnatin jihar Katsina ta ce shirye-shirye sun kankama domin bin sahun sauran sassan duniya a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya a za ake gudanarwa ranar 26 ga watan Agustan kowacce shekara. Shugaban Hukumar Kula d Tarihi da Al’adu ta jihar, Dr Kabir Ali-Masanawa ne ya bayyana hakan yayin wani jawabi ga manema labarai a...
Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya tabbatar da cewa, Isra’ila da Amurka ne suka bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa bayan da suka fuskanci martani mai tsanani a lokacin da suka kaddamr da hare-hare kan kasar Iran. A yayin da yake karbar bakuncin babban kwamandan rundunar tsaron kasar a Afirka...
Bankin Duniya ya amince da bayar da dala miliyan 300 domin aiwatar da wani sabon shiri da zai inganta rayuwar ’yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suka ba su matsugunni a Arewacin Nijeriya. Bankin ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda...
Nijeriya da Isra’ila sun sake jaddada aniyarsu ta karfafa haɗin gwiwar tsaro a fannoni daban-daban, kamar batun yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, samar da kuɗin tsaro da kuma bayar da horo na musamman ga jami’an tsaron Nigeria. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar haɗin gwiwa wadda Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani basarake, Mohammed Tukur mai shekaru 55, a kauyen Sabon Gari da ke yankin Zambuk na Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen kasar Armenia Ararat Mirzoyan ya tabbatarwa JMI kan cewa yarjeniyar sulhu da suka cimma da kasar Azairbaijan ba zai shafi bukatun kasar Iran ko kuma hanata wani hakkinta a yankin kaukas ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Armenia yana fadar haka a safiyar yau...
Nijeriya da ƙasar Isra’ila sun sake jaddada aniyarsu ta ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro a fannoni masu muhimmanci kamar yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, samar da kuɗin tsaro da kuma horaswa ta musamman. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar haɗin gwiwa wadda Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, da Mataimakiyar Ministan Harkokin Waje...
Hakan ya gudana a ƙarƙashin jagorancin hukumomin da ke lura da yadda ake tafiyar da gasar da kuma kare haƙƙin masu amfani da kaya (FCCPC), hukumar kula da tallace-tallace ta Nijeriya (ARCON), da hukumar kula da harkokin caca da wasanni ta Jihar Legas (LSLGA). Zaɓen ya kasance cikin gaskiya da adalci, inda waɗanda yi nasara...
Hukumomin Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Gwamnatin Tarayya sun ufe makarantar a sakamakon zanga-zangar da dalibai suka gudanar domin nuna fushinsu kan harin da ’yan fashi suka kai dakunan kwanansu. Daliban sun tayar da tarzoma ne da sanyin safiyar Talata bayan harin ’yan fashin ya ya yi sanadiyyar jikkatar wasu dalaibai da dama, suna mazu...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Babban abin kunya ne shirun da gwamnatocin yammacin Turai suka yi game da muggan laifukan ‘yan sahayoniyya Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya dauki kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suka yi wa ‘yan jaridun Falasdinawa a matsayin wata shaida ta ta’addancin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila...
Kasar Italiya ta janye jirgin ruwanta daga tekun Bahar Maliya bayan gazawarta a fage kwamawa da kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Kasashen Turai sun ci gaba da janye jiragen ruwa da jiragen yaki daga tekun Bahar Maliya, lamarin da ke tabbatar da hukuncin da kasashen nahiyar suka dauka na cewa ci gaba da zamansu a...
Wani dattijo ya rasu a sakamakon hatsari da gobarar tankokin sakon iskar gas da ta auku a yankin Zariya da ke Jihar Kaduna. Aliyu Ramalan Babbale mai shekara sama da 70 ya rasu ne a lokacin da yake ƙokarin tsira da ransa a sakamakon hatsarin tankokin a safiyar ranar Litinin. Dattijon ya gamu da ajalinsa...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa ‘yan jarida biyar a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai a zirin Gaza, yana mai bayyana wannan laifi a matsayin shaida ta yanke kauna daga gwamnatin da duniya ta juya mata baya saboda munanan laifukanta. A...
Ministan tsaron kasar Italiya Guido Crosetto ya bayyana cewa gwamnatin Isra’ila ta fita hayyacinta a yakin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza, yayin da kuma yake nuni da cewa Italiya a shirye take ta bi sahun kasashen duniya wajen kakaba wa Isra’ila takunkumi. A cikin wata hira da jaridar La Stampa ta...
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya ce yaki da talauci muhimmin mataki ne na hanzarta ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi. Ya bayyana haka ne a lokacin shirin gwamnatin jihar mai taken “Gwamnati da Jama’a” wanda aka gudanar a karamar hukumar Ringim. Malam Umar Namadi ya jaddada muhimmancin horas da matasa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A safiyar wannan Litinin ɗin ce aka wayi gari da wani mummunan hatsarin tankoki biyu na dakon iskar gas a Zariya, inda direba ɗaya kacal ya tsira da rai, yayin da wasu da dama suka ƙone ƙurmus. Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe tara na safe, a kusa...

Mahukuntan Iraki Sun Bayyana Cewa: Akwai Yiwuwar Masu Ziyarar Arba’een Na Imam Husaini {a.s} Zasu Zarce Miliyan 4
Birnin Karbala mai tsarki na sa ran karbar bakwancin masu ziyara sama da miliyan 4 daga kasashen ketare domin gudanar da juyayin Arbaeen Jama’a masu dimbin yawa na tururuwa zuwa birnin Karbala mai tsarki daga Najaf domin halartar yuyayin ranar Arbaeen a cikin tsauraran matakan tsaro da na hidima. Wakilin Al-Alam da ke kan titin...
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kashe wani fitaccen dan jarida na kafar yada labarai ta Al Jazeera Anas al-Sharif tare da abokan aikinsa hudu a wani hari da ta kai Gaza. Isra’ila ta zarge shi da kasancewa wani jagora na Hamas sannan ta ce ta hallaka shi saboda irin rahotannin da yake bayarwa masu...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce dole ne dukkan kasashen duniya su yi kokarin kawo karshen laifukan da Isra’ila ke aikatawa a zirin Gaza da kuma kawo karshen killacewa da take yi wa yankin. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake karbar takardar shaidar sabbin jakadun kasashen...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa “babu wani abu da aka yanke ya yanzu game da tattaunawa da Amurka,” ya kara da cewa “babu wani tabbci kan zabar wata kasa da za ta karbi bakuncin tattaunawar.” A jawabin da ya yi a gefen taron majalisar ministocin a jiya Lahadi, Araqchi ya...
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zaman gaggawa a hedikwatar MDD da ke birnin New York a jiya Lahadi, bayan matakin da majalisar ministocin Isra’ila ta dauka na fadada ayyukan soji da kuma mamaye yankin zirin Gaza. Mataimakiyar Sakatare-Janar mai kula da harkokin Turai, Tsakiyar Asiya da Amurka, Miroslav Jenča, ta jaddada...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abba Aragchi ya bayyana cewa kara karfin da dangantaka tsakanin Iran da Saudia yake yi, yana taimakawa zaman lafiya a yankin. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar iran ya kara da cewa Aragchi ya bayyana haka ne a lokacinda ya gana da jakadan kasar Iran a Saudiya Ali Reza Enayati...