Aminiya:
2025-11-27@21:46:04 GMT

Yadda A ‘Daidaita Sahu’ ya ƙwace kasuwar bas da tasi

Published: 27th, September 2025 GMT

Gabanin shekarar 2005 da gwamnatin Kano ta hana sana’ar haya da babur saboda matsalar tsaro da ta kunno kai jihar, jigilar fasinjoji ta ta’allaƙa ne da motocin haya na hayis, ko tasi, a kuma farashi mai sauƙi.

Sai dai sannu a hankali, waɗannan motocin hayar suna neman zama tarihi musamman a birane saboda zuwan babura masu ƙafa uku, waɗanda aka fi sani da ‘A Daidaita Sahu’ a lunguna da saƙo.

Wata ƙididdiga da Hukumar Samar da Kuɗaɗen Shiga ta Jihar Kano ta fitar, na nuna gwamnatin jihar tana samun aƙalla Naira miliyan shida a kullum daga harajin Naira 100 da ta sanya wa masu sana’ar A Daidata Sahu — wanda a shekara ya kai Naira biliyan 2.1.

Haka kuma rahoton da Hukumar Kula da Titunan Kano (KAROTA) ta fitar a shekarar 2021 ya nuna sama da baburan A Daidata Sahu 60,000 ne ta yi wa rajista a jihar.

Ƙasashen duniya sun ƙaurace wa Isra’ila a Babban Taron MƊD Me ya sa wasu ƙasashen Afirka ba sa goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinu?

Sai dai ƙungiyar masu sana’ar ta musanta alƙaluman, inda ta yi iƙirarin cewa adadin na iya ninka hakan saboda ba duka ne aka yi wa rajista ba.

A hannu guda kuma ƙididdigar Ƙungiyar Ma’aikatan Sufuri ta Ƙasa (NURTW) reshen Jihar Kano, ta nuna a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023, an rufe sama da kashi 65% na tashoshin bas a jihar sakamakon ƙarancin fasinjoji da tsadar kula da motocin haya.

Wannan ya bayar da gudummawa wajen ƙaruwar matasan da suka ajiye sana’ar haya da bas suka rungumi A Daidaita Sahu, wasu kuma suka durƙushe baki ɗaya.

Abdullahi Gadanya, tsohon direban bas ne da ya shafe shekaru yana sana’ar a Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana halin ha’u’la’in da durƙusheawar sana’ar ta jefa su cikin halin ƙaka-na-ka-yi.

“Samun A Daidaita ya taka rawa wajen mayar da sana’armu koma-baya. A da nakan iya ɗaukar fasinja 15 a sa’a ɗaya, amma yanzu kuwa sai godiyar Allah kawai. Jama’a sun fi karkata zuwa A Daidaita.

“A shekarun baya nakan samu N20,000 a sa’a ɗaya zuwa biyu, amma yanzu sai dai idan na shiga tashar da ake yin lodi zuwa wasu jihohin na ɗauki fasinja wuni guda nake iya samun rabin hakan.

“Motata ta tsufa, saboda haka lodi ɗaya kawai nake yi, ba ta riƙe ni saboda ina da iyali. Sai ka ga a rana bai fi ka yi N10,000 ba saɓanin a baya da kuɗin ya ninka haka, kuma a cikin gari ne.”

Gadanya ya ce a dalilin wannan tasgaron, dole ta sanya shi bai wa mai ɗakinsa jari inda take cinikin kayyakin girki kamar su man gyaɗa da daddawa.

Ya fi sauƙi — Fasinja

Habiba Sabo guda ce daga cikin fasinjojin da har yanzu suke hawabas, ta kuma ce ba wani abu ne ya sanya ta rungumar motar hayar ba face kasancewarta mafi arhar hanyar sufuri har a yanzu.

“Ni daga Ƙarfi nake zuwa Kano domin sayar da masara. Idan na hau A Daidaita, ribar sana’a takan ɓace saboda tsada. Amma idan muka haɗu da abokan sana’ata muka hau bas, bayan kuɗin bai kai na A Daidaita ba, ana ƙara yi mana ragi sosai.”

Sai dai a ɓangaren Harira Ado da ita ma ’yar kasuwa ce, lalura ce kaɗai ke tilasta ta hawa bas a yanzu.

“Idan kana sauri, bas ɓata maka lokaci za ta yi. Sau da yawa gara na hau A Daidaita. Amma idan zan saro kaya daga Kura ko Bata, bas nake hawa saboda N300 kacal ta ishe ni zuwa da dawowa tare da lodin kayana. Amma a A Daidaita sai na kashe wajen N1,500 a zuwa kaɗai saboda kayana.”

Matsalar tsaro da asarar rai

Rahoton Bloomberg na shekara (2022) ya nuna cewa ƙasashe masu tasowa kamar Nijeriya na fama da matsalar amfani da ƙananan ababen hawa musamman baburan A Daidata wajen aikata laifuka saboda rashin rajista da rashin tsauraran matakan tsaro daga ɓangaren gwamnati.

Haka kuma, Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta ce yawaitar A Daidata Sahu ya haifar da ƙaruwar haɗari a tituna, inda ta ce a Kano kaɗai, sama da kashi 60 na haɗuran shekarar 2023 na A Daidaita Sahu ne.

Kazalika matsalar tsaro a baburan A Daidaita, musamman ƙwacen waya, na ci gaba da yawaita a jihohin Arewacin Nijeriya, har ta kai al’umma suna ɗaukar matakin kamawa da kuma duka, wani lokacin ma har da kisa na waɗanda aka kama da baburan suna ƙwace.

A watan Nuwambar 2022, kafafen watsa labarai da dama sun rawaito yadda aka yi amfani da bubur mai ƙafa uku wajen satar mutum a Jihar Katsina. Haka ma a shekarar 2023, inda rundunar ’yan sanda ta kama wasu matasa da ke amfani da nau’in baburin wajen aikata ƙwacen waya, sata, da ma kisa, musamman a jihohin Kano da Kaduna.

A Jihar Kano, rundunar ’yan sanda ta tabbatar da cewa a cikin watanni shida na 2024, an samu rahoton fashi sama da 400 da aka yi da babur ɗin.

Sai dai, duk da haka, yawan tsayawa jiran fasinjoji ya sa mutane da dama karkata ga A Daidaita.

Ra’ayin jama’ar gari

Isa Abubakar Goje ya ce shi ba ya iya hawa bas saboda yawancinsu ba su shiga cikin unguwanni sosai, kuma duk da haka za iya kashe kuɗi mai yawa kafin buƙatarsa ta biya.

“Misali ni da ke Ɗorayi, sai na sake biyan A Daidaita daga bakin titi. Farashin babu bambamci sosai da na ɗau A Daidaita kai tsaye zuwa gida. Ga shi na ɓata lokaci a hanya. To, gara kawai in biya sau ɗaya a kai ni akan lokaci.”

Amma ga wasu, kamar Hassan Musa Sharaɗa naganin mafita ita ce a dawo da bas, domin ci baya ne mutuwar sana’ar ko a ƙasashen da suka ci gaba.

“Gaskiya, idan gwamnati ta dawo da tsarin bas da tasi, za mu ji daɗi sosai. Bas ta fi arha kuma ba a cika jin rahoton satar mutane ko fashi ba. A kasashen da suka ci gaba ma. Bas ce a kan gaba wajen jigilar jama’a. Kuma nasu ma sun fi namu girma domin irin Macopolo ɗin nan ne da su jiragen ƙasa.

“Don haka raguwar bas a Kano ba matsala ce kawai ta sufuri ba, illa ce har ma ga tattalin arziki, tsaro, da walwalar jama’a.” in ji shi.

Yayin da A Daidaita ya kawo sauƙi da sauƙin shiga lungu da saƙo, tsadar rayuwa da barazanar tsaro na dabaibaye da shi.

A don haka ne ma ya sa al’umma ke kira ga gwamnati da hukumomi da su yi duba na tsanaki domin dawo da tsarin bas da ya fi araha, da tsaro domin samar wa da jama’a sauƙi a dadai wannan lokacin da ake fama da matsalolin tattalin arziki.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Super Falcons za su ƙaurace wa wasannin Nijeriya saboda riƙe musu alawus

’Yan wasan tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Mata, Super Falcons, sun yi barazanar ƙaurace wa wasannin sada zumunta da Najeriya za ta buga a watan Disamba mai kamawa.

’Yan wasan sun ce za su ƙaurace wa wasannin ne idan har Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta ci gaba da jinkirta biyan kuɗaɗen alawus-alawus da suke biyo tun na Gasar Olympics da aka yi a birnin Paris a 2024.

Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro

Wasu majiyoyi daga ƙungiyar sun tabbatar cewa ’yan wasan na ci gaba da jiran a biya su haƙƙoƙinsu na wasannin da suka buga, ciki har da alawus na nasarar da suka samu a gasar Olympics, duk da cewa Najeriya ta fice tun a matakin rukuni bayan shan kashi a hannun Brazil da Spain da Japan.

Wani jami’in tawagar, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce ’yan wasan gaba ɗaya sun amince cewa ba za su halarci kowanne wasa ba muddin ba a biya su haƙƙoƙinsu ba.

Ana sa ran Najeriya za ta buga jerin wasannin sada zumunta daga ranar 2 zuwa 10 ga watan Disamba, a wani ɓangare na shirye-shiryen Super Falcons domin tunkarar gasar cin Kofin Afrika ta Mata na 2026.

A halin yanzu, NFF ba ta fitar da jerin sunayen ’yan wasan da za su wakilci Najeriya a wasannin ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • Super Falcons za su ƙaurace wa wasannin Nijeriya saboda riƙe musu alawus
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
  • Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
  • Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makaamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan