Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas
Published: 27th, September 2025 GMT
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sauka a Lagos a jiya Juma’a domin ziyarar aiki yayin da ƙasar ke shirin bikin cikar shekaru 65 da samun ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka.
A cewar kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, Tinubu ya tafi Legas ne bayan ya halarci naɗin sabon Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, a garin Ibadan, jihar Oyo.
Yayin da yake a Lagos, shugaban ƙasa zai gana da manyan ƴan kasuwa da jiga-jigai a ɓangaren gwamnati domin tattaunawa kan ci gaban tattalin arzikin ƙasa. Haka kuma, a ranar Talata, 30 ga Satumba, zai ziyarci jihar Imo inda zai ƙaddamar da wasu muhimman aiyukan raya ƙasa na Gwamna Hope Uzodimma.
A wani ɓangare na bikin zagayowar ranar ƴancin kai, Tinubu zai kuma ƙaddamar da sabuwar cibiyar al’adu da fasaha ta ƙasa, wadda aka sake fasalta wa daga tsohuwar National Theatre zuwa Wole Soyinka Centre for Culture and the Creative Arts.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sibil Difens ta cafke mutum 3 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Kano
Hukumar Tsaro ta Sibil Difens a Jihar Kano, ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a Ƙaramar Hukumar Doguwa.
Hukumar ta miƙa su ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a kotu.
’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a BornoKwamandan hukumar na Jihar Kano, Bala Bawa Bodinga ne, ya bayyana hakan yayin da yake magana da ’yan jarida a hedikwatar hukumar a ranar Juma’a.
Ya ce an kama mutanen ne da sanyin safiyar ranar Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihin bayaai.
Jami’an hukumar daga sashen Doguwa sun tare su a ƙofar Riruwai da ke Doguwa yayin da suke ɗauke da manyan jakunkuna uku cike da tabar wiwi.
Babban wanda ake zargi shi ne Yusuf Alasan, mai shekara 25, tare da abokan aikinsa biyu; Muktar Musa da Musa Sani.
Kwamandan, ya ce hukumar ta kammala binciken farko kuma ta miƙa su tare da kayan da aka kama zuwa ofishin NDLEA na Jihar Kano don yin ƙarin bincike.
Bodinga, ya ƙara da cewa NSCDC za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin kawar da laifuka da tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar.