Wannan Bishiya Ta Bayyana Sirrin Ci Gaban Jihar Xinjiang
Published: 27th, September 2025 GMT
Tabbas, ko a zamanin yau ma, aikin raya tattalin arziki ba ya rabuwa da wahalhalu. Misali, a cikin gidajen da ake kiwon jatan lande, dole ne mutane su jure yanayi mai zafi da ya kan kai sama da digiri 40 na ma’aunin Celcius, da kuma tarin sauro dake cizon mutum. Har ila yau, akwai wasu kifayen da ake kiwonsu, misali Mullet, wadanda mazauna yankin Xinjiang ba su saba da cinsu ba, don haka ana bukatar karin kokari a fannin tallarsu a kasuwa.
Ci gaban Alar wani misali ne na ci gaban daukacin jihar Xinjiang mai cin gashin kanta, bayan da aka kafa ta shekaru 70 da suka gabata. Albarkacin matukar hakuri da juriya, da suka yi kama da halayyar bishiyar Hu-Yang, da yadda ake amfani da dukkan albarkatun da ake iya samu wajen neman ci gaba a cikin lokaci mai tsawo, jihar Xinjiang da ke yankin kan iyakar kasar Sin, ta tabbatar da kwanciyar hankali da hadin kan kabilu daban daban, da zama cibiyar kasuwanci da ke hada Asiya da Turai, da kuma babbar cibiyar dake samar da kayayyakin masana’antu iri-iri. Kana jimillar GDPn jihar ta karu da fiye da ninki 1,600 tun daga shekarar 1955, abin da ya sa mazauna jihar bayyana cewa, “Rayuwa a yau ba ta misaltuwa da ta baya.”
A halin yanzu, albarkacin kokarin da ake yi na hakar magudanar ruwa da sake amfani da ruwa mai gishiri da aka samu bisa wanke kasa mai gishiri yayin da ake gudanar da aikin noma, wajen ban ruwa a cikin hamada, dimbin itatuwan Hu-Yang na Alar sun koma kore kuma suka fara toho. Hakan na alamanta kyakkyawar makoma ta jihar Xinjiang. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya
A cewar NEMA, mutane 135,764 ne suka rasa matsugunansu, yayin da 115 aka bayyana bacewarsu, yayin da wasu 826 suka samu raunuka sakamakon ambaliyar. Bugu da kari, gidaje 47,708 sun lalace, yayin da gonaki 62,653 suka lalace a fadin jihohin da abin ya shafa.
Hukumar ta kara da cewa, daga cikin wadanda abin ya shafa sun hada da yara 188,118, mata 125,307, maza 77,423, tsofaffi 18,866, da kuma nakasassu 2,418.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA