Aminiya:
2025-11-27@22:30:19 GMT

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda tare da ƙwato makamai a Neja

Published: 26th, September 2025 GMT

Dakarun rundunar sojoji ta 22 Armored Brigade da ke aiki a ƙarƙashin Operation Park Strike V tare da haɗin gwiwar  Jami’an tsaron gandun daji sun kashe wasu ’yan ta’adda da ba a tantance adadinsu ba a dajin Kainji da ke Ƙaramar hukumar Borgu a Jihar Neja.

Hakazalika an samu nasarar ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda 3 da babura 4 daga hannun maharan.

Babu wata jam’iyya dana ke shirin komawa — Kwankwaso ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a Masallaci a Zamfara

Muƙaddashin Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar soji ta 22 da ke Ilorin, Captain Stephen Nwankwo, a wata sanarwa ne ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce, ɗaya daga cikin jami’an da suke kula da gandun dajin yankin ya samu raunuka a harbin bindiga, amma ya fara samun sauƙi.

Wannan farmakin na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na samar da tsaro a dajin Kainji (KLNP) daga wuraren da ke da ’yan tada ƙayar baya.

Ya ƙara da cewa, an samu nasarar ne a safiyar ranar Alhamis 25 ga watan Satumba, 2025, lokacin da jami’an tsaro na haɗin gwiwa suka yi wa ’yan tada ƙayar bayan kwanton ɓauna a dajin Kainji.

Ya ce, “A ci gaba da ƙoƙarin da ake na samar da tsaro a dajin Kainji (KLNP) daga miyagu da ke haddasa rashin tsaro a yankin, sojojin na 22 Armored Brigade, da ke aiki a ƙarƙashin Operation Park Strike Ɓ, tare da jami’an gandun dajin Park Rangers, sun gudanar da wani samame na kwantan ɓauna a safiyar ranar Alhamis, 25 ga Satumba, 2025.

“A bisa sahihan bayanan sirri, sojojin sun yi kwanton ɓauna a mashigar ’yan tada ƙayar bayan a Tungan Talle, Sashen Zugurma na wurin shaƙatawa da misalin ƙarfe 1:15 na safe.

“A yayin arangamar, sojojin sun yi artabu da ’yan ta’addan da musayar wuta, inda suka kashe wasu da ba a tabbatar da adadinsu ba, yayin da wasu suka samu raunuka, inda suka samu nasarar ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda 3 da kuma babura 4.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza

Rahotanni sun bayyana cewa kididdigar da ma’aikatar harkokin wajen yankin falasdinu ta fitar ya nuna cewa sojojin Isra’ila sun kashe akalla yan mata 33000 a ci gaba da yakin kare dangi da take yi kan alummar Gaza.

Ma’aikatar fa fitar da wannan sanarwar ce a wajen taron ranar kawo karshen hare-hare kan mata ta duniya . kuma tayi kaca-kaca da gwamnatin sahayuniya game da irin muggan laifukan yaki da ta tafka, inda ta rika amfani da makamai na zamani kan alummar falasdinu

Kididdigar ta nuna cewa sama da mata 12500 da kuma yara 20,000 ne Isra’ila ta kashe a harin da ta kai tun daga watan oktoban shekara ta 2023.

Har ila yau ma’aikatar ta bayyana cewa lallai a kwai bukatar a dauki matakin gaggawa na matsin lamba domin kawo karshen ci gaba da mamaye yankunan falasdinawa da HKI ke yi, kuma tayi aiki da kudurin kafa kasashe guda biyu da zai bada garanti wajen kafa kasar falasdinu..

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu. November 26, 2025 Aljeriya Tayi Kira Da A Dakatar Da Israila Game Da Hare-haren Da Take Kaiwa November 26, 2025 Sojojin Sun Sanar Da Kwace Mulki A Kasar  Guinea Bissau November 26, 2025 Larijani Iran Tana Maraba Da Tattaunawa Ta Gaskiya Amma Ba Tsararren Sakamako Ba November 26, 2025   November 26, 2025 Isra’ila Tana Ci Gaba Da Rushe Gidaje A Yankin Gaza November 26, 2025 Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe November 26, 2025 Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta November 26, 2025 Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki November 26, 2025 Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin November 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
  • Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Harkar Tsaro Tare da Bada Umurnin Daukar Sabbin Jami’ai
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
  • Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS
  • Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba
  • Hizbullah: Isra’ila na kuskure idan ta na tunanin kashe-kashen kwamandodinmu zai kawo karshen kungiyar
  • Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano