HOTUNA: An kai gawar Arase Benin domin yi mata jana’iza
Published: 27th, September 2025 GMT
An kai gawar Tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Solomon Arase, zuwa Birnin Benin, Babban Birnin Jihar Edo, domin yi masa jana’iza.
Arase, ya rasu ne a ranar 31 ga watan Agusta, 2025, a Asibitin Cedarcrest da ke Abuja, bayan fama da rashin lafiya.
Mutum 7 sun rasu yayin da tirela ta murƙushe motoci a Madalla ’Yan uwa sun samu Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a fanni iri ɗayaA makon da ya gabata, aka gudanar da bikin tunawa da shi a Abuja.
Sai kuma a ranar Asabar Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kai gawarsa Benin domin kammala bukukuwan jana’izarsa.
Ga hotuna:
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arase rasuwa Tsohon Sufeto Janar Na Yan Sanda
এছাড়াও পড়ুন:
An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
Hukumar kula da makarantun firamare da sakandare ta Jihar Katsina ta sanar da sake buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarabawar zangon farko na shekarar karatu.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sani Danjuma Suleman, ya fitar a madadin Shugaban hukumar, ta ce makarantun firamare, sakandiren je-ka-ka-dawo da kuma makarantu masu zaman kansu za su buɗe daga yau Talata domin ci gaba da jarabawar zangon farko.
Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai lokacin da hali ya ba da dama.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun bayan ƙaruwar hare-haren sace ɗalibai da masu garkuwa da mutane suka sake farfaɗowa da su a wasu yankuna.
Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne da nufin daƙile matsalar tsaro da kuma sa ido a kan al’amura.
A ƙarshe, hukumar ta roƙi haɗin kan iyaye da masu kula da ɗalibai domin su ci gaba da ba wa shirin goyon baya tare da ƙarfafa ɗaliban su dage da karatu wajen rubuta jarabawar da suke yi.