Mun haramta amfani da littattafai masu wa’adin amfani ɗaya —Gwamnatin Gombe
Published: 27th, September 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Gombe ta haramta amfani da littattafan karatu da ba sa iya amfani sau biyu da kuma bukukuwan ‘sign-out’ da dalibai ke gudanarwa a bayan jarrabawar kammala karatu.
Daraktan Kula da Ingancin Ilimi na Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Sa’idu Dauda Gadam, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a.
Ya ce yin littattafai masu guraben amsoshi ko sarari na rubutu da ba sa sake amfani yana jefa iyaye cikin halin ƙuncin tattalin arziki, tare da haifar da asarar kuɗaɗe.
Don haka, daga ranar 15 ga Satumba, 2026, dukkan makarantu za su daina amfani da irin wadannan littattafai.
Yadda A ‘Daidaita Sahu’ ya ƙwace kasuwar bas da tasi Ƙasashen duniya sun ƙaurace wa Isra’ila a Babban Taron MƊDA maimakon haka, za a samar da littafi na koyarwa mai ɗorewa, sannan dalibai su riƙa amfani da takardun rubutu na daban don ɗaukar darussa da amsoshi.
Haka kuma, Gwamnati ta haramta bukukuwan sign-out da ake gudanarwa a makarantu, musamman a lokutan da ake samun munanan dabi’u da rashin tsaro daga dalibai.
Wannan al’ada, daliban da suka kammala aji shida na firamare da JSS 3 da SS 3 ne suke aikata ta, inda suke lalata kayan makaranta da faɗace-faɗace game da wasu abubuwa na fitsara.
Bugu da kari, Gwamnati ta dakatar da rijistar sababbin makarantu masu zaman kansu, na al’umma da na addini, har sai an kammala sake duba tsarin.
Duk makarantu da ba su kammala rijista ko karɓar takardar sahalewar aiki ba, an umarce su da su tabbatar sun gama kafin 31 ga Oktoba, 2025.
Sanarwar ta kara jaddada cewa dukkan makarantu masu zaman kansu su daidaita ayyukansu da manufofin gwamnati, ciki har da bin sabon manhajar NERDC, koyar da sana’o’i, da kuma aiwatar da manufofin yaƙi da cin zarafi da zaluncin ɗalibai.
Haka kuma duk manyan makarantu masu zaman kansu da ba su da cibiyar jarrabawar waje irin su WAEC, NECO, NABTEB ko NBAIS, an umurce su da su tuntubi Ma’aikatar Ilimi domin samun shawarwari.
Ma’aikatar ta jaddada aniyar gwamnatin jihar na tabbatar da ingantaccen ilimi mai araha, da kuma bai wa kowa damar samu a Jihar Gombe.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: makarantu
এছাড়াও পড়ুন:
Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin
Pars Today – Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, yana mai jaddada muhimmancin Pakistan a yankin, ya ce haɗin gwiwa tsakanin Tehran da Islamabad a fannoni daban-daban yana taimakawa wajen kawo kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin
Ali Larijani, Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, ya ce da sanyin safiyar Talata da ya isa Islamabad cewa Pakistan muhimmiyar ƙasa ce a yankin kuma tana da matsayi mai kyau wajen tasiri ga yanayin tsaro na yankin.
A cewar Pars Today, ya ƙara da cewa a matsayinta na maƙwabciyar gabas ta Iran, Pakistan ma tana taka rawa a al’adu, kuma dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu ta daɗe tana da zurfi kuma ta tarihi.
Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa a cikin yanayin da yankin ke canzawa a yanzu, haɗin gwiwa tsakanin Iran da Pakistan a fannoni daban-daban na iya taimakawa wajen kwantar da hankali da zaman lafiya a yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin Lebanon November 26, 2025 Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci