2027: Abubuwan Da Jam’iyyun Siyasar Nijeriya Ke Tsammanin Samu Daga Sabon Shugaban INEC
Published: 27th, September 2025 GMT
Bisa sashe na 154 (1) na kundin tsarin mulkin na 1999 da aka yi wa kwaskwarima, ” shugaban kasa ne zai nada shugaban INEC da mambobin hukumar zabe ta kasa, sannan majalisar dattawa ta tabbatar da su.”
Dangane da tanadin da ke cikin tsarin mulki, Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ya tanadi jerin sunayen ‘yan takara da za su meye gurbin Yakubu.
Da yake jawabi kan tsammanin jam’iyyar APC mai mulki, daraktan yada labarai, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa yayin da jam’iyyar ke nufin lashe duk zabe, tana jaddada bukatar samun yin aldaci ga kowa.
Ibrahim, a cikin wata hira, ya bayyana cewa, “A matsayinmu na jam’iyya, abin da muka sa a gaba shi ne samun nasarar cin zabe mai cike da inganci.”
“Babban burinmu shi ne, yadda za mu karbe iko ta hanyar da za ta ba da riba ga dimokuradiyya ga mutane. burinmu ita ce yadda za mu tsaya takara a zabe kuma a ba mu damar taka ba tare da an dakatar da mu ko an cire mu daga zabe ba.
“Don haka, muna sa ran samun shugaban hukumar zabe wanda zai ba da dama ga kowa, wanda zai ba da damar gudanar da zabe cikin ‘yanci da adalci. Muna bukatar shugaban INEC da zai yi aiki ka doka.”
Sakataren yada labarai jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya jaddada cewa dole ne shugaban INEC da zai zo ya zama mutum mai nagarta.
Ologunagba ya kuma kira ga shugaban kasa da masu ruwa da tsaki masu alkakkin zaben shugaban INEC su yi la’akari da halayen ‘yan takarar sosai kuma su tabbatar an nada mutumin da ke da kwarewa.
Ya bayyana cewa, “Shugaban INEC na gaba ya zama wani mutum mai nagarta, ya zama wanda ba zai kasance mai mummunan hali ba, ya zama mai adalci, wanda zai zama mai ‘yanci kuma ya gudanar da hukumar ta wannan hanyar, kamar yadda doka ta tanada. Don haka wannan shi ne abin da muke tsammani.”
Ita kuwa jam’iyyar hadaka, ta bakin sakataren yada labarai na kasa, Bolaji Abdulahi, ta bayyana damuwa kan rikicin bai wa INEC ‘yancin kanta.
Abdullahi ya bayyana cewa sabon shugaban INEC da za a zaba dole ne ya yi aiki don dawo da amincewa ta hanyar tabbatar da gudanar da zabe mai inganci a 2027.
Ya ce, “Abu mafi muhimmanci shi ne, ina tunanin INEC ta sha fama da rikice-rikice na samun amincewa a idon masu kada kuri’a a Nijeriya a cikin shekaru da dama.”
“Sabon shugaban INEC ya kamata ya tabbatar da cewa hukumar ta ci gaba da kasancewa a matakin amincewa. Ka san cewa, tabbatar da tsarin zabe yana karfafa gwiwar kowa, kuma shi ne kawai hanyar da za a tabbatar da kwanciyar hankali a cikin kasar nan.
“Dole ne su tabbatar da nada mtumin da zai kasance tsayayye da kuma jajircewa. Idan aka kasa yin hakan, hakan na iya haifar da shakku a cikin zukatan ‘yan kasa game da ingancin zaben 2027, ko za su kasance masu ‘yanci da adalci kan zaben.
“Don haka, ina tsammanin shekara ta 2027 za ta zama mai muhimmanci ga kowa. A matsayin jam’iyya, muna fatan cewa nadin zai ba da damar ga wanda ya fahimci muhimmancin tarihi na aikin.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Siyasa ya bayyana cewa tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta
Daga cikin wadanda shugaban kasar ta Nigeria ya yi wa afuwa da kawai Maryam Sanda ‘yar shekaru 37 wacce aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunta da kashe mijinta da wuka a 2017.
Mai Magana da yawun shugaban kasa Bayo Onangua ya saki bayanin afuwar da shugaban kasar ya yi, wacce kuma ta hadad a Faruka Lawan tsohon dan majalisa da aka samu da laifin cin hanci da rashawa a 2021.
Sai kuma Ken Saro-wiwa wanda dan fafutuka ne mai rajin kare muhalli a yankin Ogoni da aka zartarwa hukuncin kisa a 1995.
Har ila yau afuwar ta shugaba Tunibu ta shafi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa wanda aka zartarwa da hukuncin kisa a 1986 saboda juyin Mulki.
Haka nan kuma shugaba Tinibu ya yafewa Sir Herbert Macaly dan kishin kasa da ya yi fada da ‘yan mulkin mallaka. ‘Yan mulkin mallaka ne su ka yanke masa hukunci a 1913.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Yi Musayar Wuta A Tsakanin Masu Tsaron Iyakokin Kasashen Afghanistan Da Pakistan October 12, 2025 Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa October 12, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Yunkurin Balair Na Yiyuwar Shiga Gwamnatin Gaza. October 11, 2025 Cuba Ta Bayyana Bada Kyautar Noble Ga ‘Yar Kasar Veunzuelas machado A Matsayin Abin Kunya. October 11, 2025 Kasar Indunusiya Ta Hana Tawagar wasan Jiminastik din Isra’ila Visar Shiga Kasarta October 11, 2025 Ammar Hakim Ya Gargadi Kasashen Yamma Da su Kiyayi Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Kasar. October 11, 2025 Sarkin Morocco Ya yi Magana Tun Bayan Barkewar Zanga-zanga A Kasar . October 11, 2025 Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Ja Kunnen Amurka Kan Taba Jiragen Dakon Man Kasa October 11, 2025 Bayan Yakin Kwanaki 12, Kifar Da Gwamnatin JMI Ya Fita Daga Zabin Makiya: Aref October 11, 2025 Iran Ta Bukaci HKI Ta Aiwatar Da Yarjeniya Da Gaza Kamar Yadda Take October 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci