Leadership News Hausa:
2025-11-27@21:15:53 GMT

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

Published: 26th, September 2025 GMT

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

Duk wani bangaren wayewa da kimiyya da fasaha za ka ga asali malaman Musulunci ne suka zo da shi, babu lokaci isasshe da mun kawo misalai masu yawa. yana daga cikin wayewar nan: tashi a sama zuwa duniyar wata, da duk “technology” din nan na zamani, harkar zane-zane, kade-kade, bushe-bushe. Amma duk aka kwashe wadannan aka bar mu sai dai halal da haram kawai! Su ma din an hana ma halal din gurbin ta, ba mu da wata magana sai dai haram! Da a ce malamai biyar za su taru, to za ka ga ba za su kago komai ba sai haram.

Amma sauran malaman kasar Turai kuwa da zarar sun hadu sai ka ga sun kago wata sabuwar kira, su kuma mutanenmu sai dai ka ji sun ce “ai duk wannan duniya ce suke kagowa!”. To wa ya kai ka lahirar in ba duniyar ba? Yanzu ba don sun kago jirgin sama ba waye zai kai ka Hajji da Umrah cikin sauri?

Jama’a mu waye, saboda addininmu wayayye ne, Annabinmu wayayye ne, Kur’aninmu wayayye ne. Abin da yasa bama fadar wadansu abubuwan ma saboda raunana. Amma yanzu an waye duka gaba daya, wayar salular nan taka babban malami ce, ka tambayi “Google” ko mene ne za ta zo maka da labarin komai, duk wasu abubuwa da aka canza a addinin nan siyasa ce ta jawo aka canza shi, amma asalinsa lafiya kalau yake, duk wayewa ce da sauki da ci gaba, idan ka duba Al-kur’ani duk haka za ka gani.

Mu yi murna dai jama’a, kuma yana ga kan malamai na addini, su rika binciken gaskiya duk inda take, su rika binciken ilimi, mu koma ma manyan littafai, littafan da aka yi tun daga wajen karni na biyu, abubuwa sun faru da yawa wanda ba za su fadu ba, amma ga littafai na karni na biyu tun daga nan aka fara, malamai sun yi kokari, mu rika koma ma wadannan da wayewa da fahimta da kwakwalwa irin ta zamani ba irin ta wancan zamani ba, saboda duk abin da suka yi mai kyau ne, amma kuma an ci gaba, Allah shi ne zamani, Allah ya kawo wayewa, Allah ya kawo wadanda Annabi da kansa ya fadi zuwan zamaninsu da wayewarsu. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce “Karshen zamani ilImi zai yawaita”. Amma ikon Allah, galibin littafan da muke karantawa suna nuni da karshen zamani ilimi zai kare. Ka san babu wanda ya isa ya ce ilimi ya kare a yanzu, yanzu ilmi ya fara ma! Ka ga ashe wannan hadisi da Manzon Allah ya ce karshen zamani ilimi zai yawaita gaskiya ne kuma shi ne daga Manzon Allah (SAW), ba littafan malaman nan ba.

Don Allah malamai ku duba manyan littafai, ku zama masu amana ta ilimi (amana ilmiyya), ku zamanto masu hango ma al’umma ci gaba, da wayewa, ba masu dakikantar da al’umma ba, ku zamanto jagorori a cikin duk abin da za ku fada, da duk abinda za ku rubuta, da duk littafin da za ku yi, duk abin da kuka yi zai same ku a cikin kabarinku. Kar don wani abu bai dace da jama’arku ba ku ce karya ne, ko ku ki yarda da shi, ko bai dace da kabilarku ba, ko bai dace da kungiyar da kake bi ba. Duk wadannan sun shiga cikin addini sun lalata shi, ba laifi rike akidu da maz’habobi amma kuma ya kamata a dauki abubuwan da suke ciki masu kyau a zubar da abubuwan da ba su da kyau. Zamani ya yi fa wanda in dai ba mu gyara ba Allah zai gyara mana fa! Manzon Allah (SAW) ya yi gaskiya, mai gaskiya ne abin gaskatawa, ya isar da sako kuma ya isar da amana. Mu zama masu adalci; asali shi ne wanda zai yi hukunci a tsakanina jama’a biyu kuma ya yi adalci a tsakaninsu. Kisdu kuma shi ne a tsakanin mutum biyu kawai, misali kamar tsakanin mai awo da wanda ake wa awon.

Muna taya dukkan al’ummar musulmi murnar ganin wannan lokaci mai tarihi na cikar Manzon Allah (SAW) shekara 1500 da haihuwa. Alhamdu Lillah!

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Murnaz Haihuwaz Maulidi SAW

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata

 

An sake tabbatar wa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya FG da suka yi ritaya cewa za a biya su wani bangare na kudaden ariyas a cikin wannan watan, kamar yadda hukumomin da abin ya shafa suka yi alkawari.

Mataimakin Sakataren ƙungiyar masu karɓar fansho ta ƙasa, Alhaji Ahmed Gazali, ya bayar da wannan tabbaci yayin da ake tattaunawa da shi ta wayar tarho daga Abuja.

Alh. Ahmed Gazali, ya yi bayanin cewas daraktan dake kula da kudade na ofishin akanta janar na tarayya ya tabbatar da daukan matakin hakan na biyan kudaden.

Ya bayyana fatan ganin kudirin FG na gaggauta biyan kudade, domin dakatar da duk wata zanga zanga wanda hakan bai dace ba ga ma’aikatan da suka yi ritaya domin bata martaban kasan nan.

Hakan kuma masu karban fensho a Radion Tarayya na kasa FRCN da Gidan talabijin na kasa NTA dake Kaduna sun nuna damuwarsu game da zargin da ake yi cewa ana kokarin wulakanta shugabannin kungiyar ma’aikatan da suka yi ritaya karkashin jagorancin kwamaret Munkaila Ogunbote.

DAGA SULEIMAN KAURA 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
  • ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau
  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon  Dake Takawa Makiya Birki
  • Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa
  • Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi da 34 a Kaduna
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta