Aminiya:
2025-10-13@15:44:33 GMT

’Yan uwa sun samu Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a fanni iri ɗaya 

Published: 27th, September 2025 GMT

Wane irin farin ciki za ku ji a matsayinku na iyaye, a cewa ’ya’yanku biyu sun kammala jami’a da Digiri Mai Daraja ta Ɗaya (First Class) a lokaci guda kuma daga wani kwas mai farin jini a wannan zamani na kimiyyar zamani?

Wani labari mai sha’awa shi ne yadda wasu ’yan uwa biyu suka kammala karatun jami’ansu da maki iri ɗaya a matakin Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a wannan shekarar daga jami’o’i daban-daban.

Maryam Salisu da yayanta Suleiman Salisu kowannensu ya kammala karatun digirinsa na farko ne da maki 4.51 daga fannin Kimiyyar Kwamfuta, a wannan shekara ta 2025 a Jihar Katsina.

A halin yanzu Suleiman ya fara aikin Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) a yayin da ƙanwar tasa take jiran lokacin tafiyarta.

Maryam ta kammala karatunta ne daga Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-ma a Jihar Katsina a yayin da Suleiman ya halarci Jami’ar Al-istiƙama da ke jihar ta Katsina.

Game da yadda aka yi suka samu maki iri ɗaya ta yayanta, Maryam wadda suke zaune a Abuja, ta ce, “Gaskiya ba wani shiri muka yi ba, Allah ne Ya ƙaddara faruwar hakan. Kuma mun yin murna da wannan nasara, mun faranta wa iyaye da ’yan uwanmu rai,” in ji ta.

Abin da ya ƙara min ƙwarin gwiwa

A hirarsu da Aminiya, Maryam, ta ce wasu sun yi mamakin yadda ta zaɓi ta karanci fannin  Kimiyyar Kwamfuta alhali kwas ne da ake ganin maza ne ke tururuwar karanta shi.

Ta bayyana cewa ita da kanta ta zaɓi ta karanci kwas domin tana da sha’awar zama ɗaya daga cikin waɗanda za a dama da su a ɓangaren kimiyya da fasaha kuma tana da burin karantar abin da ya shafi ƙiƙirarriyar basira (AI).

Ta ce a lokacin da wasu suka ji kwas ɗin ta take son karantawa sun yi ƙoƙarin karya ƙwarin gwuiwarta, cewa kwas ne da mata ba su fiye yi ba saboda wahalarsa, amma sai hakan ya ƙara mata ƙarfin gwuiwar cika burinta, saboda tana so ta nuna cewa babu wani fannin ilimi da ya fi ƙarfin mace ta karanta.

Da aka tambaye ta ko ta yarda da cewa Suleiman ya fita ta hazaƙa, sai ta ce: “Eh, duk da cewa ina mishi dariya idan na ga yana hana kansa barci a lokacin, amma gaskiya yana aiki tuƙuru kuma yana da hazaƙa.

“Idan ban fahimci abu ba, sai ya koya mun da kansa. Wannan shi ne abin da nake matuƙar yaba masa a kai.”

‘Ba na iya barci’

Da yake bayyana wa wakilinmu irin faɗi tashin da ya yi a lokacin da yake makaranta, Suleimin ya bayyana yadda yake karatu wurjanjan tare da hana idonsa barci.

“Ni dai na sha wahala, ban fiye yin barci ba. Ba na kwanciya barci. Abin da ya kai ni ga wannan nasarar shi ne jajircewa da yin aiki tuƙuru da kuma dogaro ga Allah.”

Suleiman da Maryam sun bayyana cewa duk da cewa daban-daban kowannensu yake karatunsa, amma suna yawan tattaunawa da taimakon juna wajen karatu, musamman tun da tsarin karatunsu na kama da juna.

Game ya yaba da ƙwazon ƙanwar tasa, ya ce, “Eh, kowa ya san fannin nan maza ne suka fi yawa. A ajinmu, muna da mace ɗaya kacal daga cikin sama da mutum 50. Amma hakan ba ya nufin mace ba za ta iya ba. A gaskiya muna da buƙatar mata a wannan fanni, kuma ina alfahari da ƙanwata.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Digiri Mai Daraja ta Ɗaya

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Maryam Sanda afuwa, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Haliru Bello.

Maryam,’ mai shekara 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan yarin Suleja kafin yi mata afuwa.

Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro

Rahotanni sun nuna cewar an yi mata afuwar ne bayan yin nadama da aikata kyakkyawan halaye.

Iyayen Maryam sun roƙi gwamnati da ta sake ta saboda ’ya’yanta biyu da ta ke da alhakin kula da su, tare da alƙawarin sauya halayenta.

Shugaba Tinubu, ya kuma yi wa wasu mutane afuwa da suka haɗa da Manjo Janar Mamman Vatsa, Ken Saro-Wiwa, da kuma Sir Herbert Macaulay.

Gaba ɗaya mutane 175 ne shugaban ya yi musu afuwa, ciki har da masu manyan laifuka, tsoffin fursunoni, da waɗanda suka yi kyakkyawan tuba.

Wannan shi ne karon farko da Shugaba Tinubu ya yi amfani da ikon yafe laifi don tausaya wa waɗanda suka aikata laifuka tun bayan hawansa mulki.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa
  • Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
  • Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe
  • Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida
  • Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho
  • Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya Fito Takara A 2027 – Oshiomhole
  • Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya
  • Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata