Me ya sa wasu ƙasashen Afirka ba sa goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinu?
Published: 27th, September 2025 GMT
Yayin da ƙasashe irin su Birtaniya, Kanada da Ostareliya suka amince da kafa ƙasar Falasṭinu, ana tsammanin samun ƙarin wasu ƙasashe.
Shugaban Falasɗinu, Mahmud Abbas, ya yaba da wannan mataki tare da kira ga sauran ƙasashe su nuna irin wannan goyon baya.
Zargin ɓatanci: Kwamitin Shura na Kano ya fara sauraron koke-koke kan Malam Triumph An gano yarinya da aka sayar ₦3.7m a Ondo
Yawancin ƙasashen Afirka sun riga sun amince da Falasdɗinu tun shekarun 1980.
Shugabanni irin su Thomas Sankara da Nelson Mandela sun taɓa danganta gwagwarmayar Falasɗinawa da irin ta Afirka na neman ’yanci.
Amma har yanzu akwai ƙasashe biyu da ba su amince da kafa ƙasar Falasɗinu ba; wato Kamaru da Eritrea.
KamaruKamaru tana da alaƙa mai ƙarfi da Isra’ila musamman a fannin tsaro.
Isra’ila na bai wa dakarun Kamaru horo, tana kuma taimaka mata wajen tabbatar da tsaron gwamnatin ƙasar.
Wannan ya sa Kamaru ba ta son lalata alaƙarta da Isra’ila.
Haka kuma, gwamnatin na tsoron idan ta goyi bayan kafa Falasɗinu, masu fafutukar ɓallewar yankin Ambazonia a cikin ƙasar za su samu ƙarin hujja.
Saboda haka, Kamaru kan guji bayyana ra’ayinta kan kafa ƙasar Falasɗinu.
EritreaEritrea kuwa ta samo matsayarta daga tarihi.
Lokacin da Falasɗinu ta nemi goyon bayan Afirka a shekarun 1980, shugabanta Yasser Arafat ya fi kusanci da Habasha wadda ke da alaƙa da Tarayyar Soviet, ba da Eritrea ba, alhali a lokacin Eritrea na fama da yaƙin neman ’yanci daga Habasha.
Wannan ya haifar da ɓacin rai a tsakanin ’yan Eritrea.
Duk da haka, Shugaban Eritrea Isaias Afwerki ya taɓa nuna tausayawa ga Falasɗinu, har ma ya amince da matsayin Falasɗinu a Majalisar Ɗinkin Duniya a 2012.
Amma bai yadda da tsarin “ƙasashe biyu” na yarjejeniyar Oslo ba, yana ganin ba zai kawo zaman lafiya ba.
Sai dai matsin lamba na cikin gida na iya taso masa, domin kusan rabin jama’ar Eritrea Musulmai ne.
A mahangar masana, hakan zai yi kama da rashin adalci idan ƙasar da ta yi nasarar samun ’yanci ba ta goyi bayan wasu su ma su samu ’yanci ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yanci Kamaru Ƙasa kafa ƙasar
এছাড়াও পড়ুন:
Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa
Mahukuntan kasar Afirka Ta Kudu sun sanar da cewa, ya zuwa yanzu ba a sami wani dalili na musabbabin mutuwar jakadan kasar Nathi Mthethwa A Afransa ba.
Jami’an tsaron kasar Faransa suna aiki tare da takwarorinsu na kasar Afirka Ta Kudu da su ka isa kasar domin gano musabbabin mutuwar jakadan.
An ga gawar jakadan na kasar na Afirka Ta Kudu a kasar Faransa,Mthethwa a Hotel din Hyatt Regency dake birnin Paris. Alamu sun nuna cewa ya bude kofar dakinsa dake hawa na 22 ya fado kasa, ba tare da wata alama dake nuni da cewa turo shi aka yi baa.
Gabanin faruwar lamarin jakadan ya aike da sako na waya ga maidakinsa da a ciki ya bayyana mata shirinsa na kisan kai.
Kasar Afirka Ta Kudu ta aike da jami’an bincike su biyar zuwa Faransa domin su yi aiki da takwarorinsu na kasar akan binciko hakikanin abinda ya faru.
Mthethwa ya zama jakada ne tun a 2023, bayan da a can baya a kasarsa ya rike mukamai da dama a fagagen al’adu da wasanni.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Ta yi Watsi Da Yunkurin Balair Na Yiyuwar Shiga Gwamnatin Gaza. October 11, 2025 Cuba Ta Bayyana Bada Kyautar Noble Ga ‘Yar Kasar Veunzuelas machado A Matsayin Abin Kunya. October 11, 2025 Kasar Indunusiya Ta Hana Tawagar wasan Jiminastik din Isra’ila Visar Shiga Kasarta October 11, 2025 Ammar Hakim Ya Gargadi Kasashen Yamma Da su Kiyayi Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Kasar. October 11, 2025 Sarkin Morocco Ya yi Magana Tun Bayan Barkewar Zanga-zanga A Kasar . October 11, 2025 Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Ja Kunnen Amurka Kan Taba Jiragen Dakon Man Kasa October 11, 2025 Bayan Yakin Kwanaki 12, Kifar Da Gwamnatin JMI Ya Fita Daga Zabin Makiya: Aref October 11, 2025 Iran Ta Bukaci HKI Ta Aiwatar Da Yarjeniya Da Gaza Kamar Yadda Take October 11, 2025 HKI Ta Kashe Mutane 19 A Gaza Duk Tare Da Tsagaita Wuta October 11, 2025 Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Shirin Zaman Lafiya Da Ya Hada Da Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza October 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci