2025-05-02@15:06:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 124
«a matsayin abokin takara»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma da sauran makamantansu. Bikin yaye ɗaliban shi ne karo na 39 da za a gudanar a jami’ar ta BUK. Bikin na kwana huɗu ya kunshi jawabai da laccoci da taruka da kuma bayar da kyaututtuka da takardun shaida a matakai daban-daban. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? Farfesa Sagir Abbas ya bayyana cewa a rana ta biyu za a...

Shugaban Kungiyar Hamas Yace: Iran Bata Gusheba Tana Taimaka Mana, Kuma Shirin Trump Na Kwace Gaza Zai Ya Lalace
Khalilul Hay, shugaban kungiyar Hamas a Gaza, wanda ya halarci gangamin bikin cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran, ya bayyana cewa yakin Tufanul Aksa ya na matsayin mataki na farko ne na kwatar kasar Falasdinu daga hannun wadanda suka mamayeta. Ya kuma kara da cewa JMI ta taimakawa kungiyar sa kuma tana ci gaba da taimaka mata, har’ila yau yana da yakini Iran zata ci gaba da taimakawa kungiyar Hamas har zuwa nasara. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta watsa jawabin Al-Hay kai tsaye daga birnin Tehran a safiyar yau litinin, inda ya yi Jawabi a dandalin Azadi dake tsakiyar birnin Tehran. Yace, farmakin ‘waadu Sadik na daya da na biyu duk...
Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 183 yau Asabar, a madadin wasu mutanenta uku daga cikin wadanda kungiyar Hamas ke garkuwa da su a Gaza a wani bangare na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza da suka cimma. Kamar dai a makon da ya gabata, za a yi musaya ta biyar a wurare biyu a zirin Gaza a jere inji rahotanni. A maimakon haka, Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 183, ciki har da 18 da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai, ciki har da wasu fitattun mutane irin su Iyad Abu Shidam, wanda Isra’ila ta yankewa hukuncin daurin rai da rai a Beersheva a shekara ta 2004. Bayanai sun ce kimanin 111 daga cikin wadannan...
Babban jami’in gudanarwa na kamfanin EDR Takale Uma, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kamfanin layin dogo na Ethio-Djibouti (EDR), yana samun ci gaba mai kyau, tare da kara karfinsa na jigilar kayayyaki zuwa kasashen waje. Uma ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Tare da karin kan jiragen kasa da taragu, yanzu mun samu damar baiwa karin wurare hidima, mun fadada zirga-zirga daga Indode da Adama zuwa Mojo, Dire Dawa, da kuma wurin ajiye kaya na Sabata.” Uma ya kara da cewa, EDR yana maye gurbin tsoffin kayayyakin aiki da sabbi, da kuma gyara wadanda suka lalace, kana ya kara yawan jiragensa daga jiragen kasa takwas zuwa 21 da taragu 892 zuwa 935. Yana mai cewa “Jajicewar da muka...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci al’ummar Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo domin jajantawa iyalan wadanda rikicin ya rutsa da su wanda ya yi sanadin asarar rayuka uku tare da jikkata wasu da dama. A ziyarar tasa, Gwamna Yusuf ya gana da iyalan wadanda suka rasu, inda ya jajanta musu tare da bayyana cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin iyalan mutanen uku da suka rasu. Ya kuma ba da umarnin a gaggauta biyan kudaden jinya ga duk wadanda suka jikkata tare da samar da kayan abinci don tallafawa iyalan wadanda abin ya shafa. A cikin nuna jin kai, gwamnan ya bayyana shirin gina sabon masallacin Juma’a a Rimin Zakara a matsayin sadaqatu jariya (dauwamammiyar...
Gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta ki bada kai ga bukatun Amurka duk tare da barazanar sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio na fasa zuwa taron G20 a kasar Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ronald Lamola ministan harkokin wajen kasar Afirka ta kudu na cewa “kasarmu yentacciyar kasa ce, kan tsarin democradiya, sannan tana mutunta bil’adama, tana daidaito tsakanin kasa, babu bambamcin launin fata” Lamola ya kara da cewa kasarsa na da tsarin zamanta kewa mai cikekken yanci daga duk wata kasa a duniya. Ministan ya kara da cewa, ba sauyin yanayi ne kawai muke tattaunawa a taron G20 ba, Kafin haka sakataren harkokin wajen Amurka yace, shi ba zai halacci taro inda babu ambaton bukatun...
Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a zaman lafiya da hakuri a tsakanin al’ummar garin Rimin Zakara sakamakon rikicin filaye da ya barke tsakanin al’umma da Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Sarkin ya yi wannan roko ne a ziyarar da ya kai yankin bayan dawowarsa daga aikin hajji. Da yake jawabi ga al’ummar yankin, Sarkin ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka jikkata cikin gaggawa. “Dole ne mu yi wa wadanda suka rasu addu’a da kuma baiwa iyalansu ikon jure wannan rashi, Allah ya sa wannan ya zama na karshe a cikin irin wannan mummunan lamari a cikin al’ummarmu,” inji...

An Samu Yuan Biliyan 9.51 Daga Sayen Tikitin Kallon Fina-Finai A Lokacin Hutun Bikin Bazara A Kasar Sin
An Samu Yuan Biliyan 9.51 Daga Sayen Tikitin Kallon Fina-Finai A Lokacin Hutun Bikin Bazara A Kasar Sin
Ancelotti ya shaidawa manema labarai ranar Talata cewa “Bellingham ya samu rauni yayin atisaye amma kuma Vinicius Jr zai buga wasan gobe duk da cewar har yanzu ya na kan murmurewa daga raunin da ya ji a watan jiya Ya kuma ce Mbappe ya yi atisaye kamar yadda aka saba a yau, amma gobe ba zai samu damar buga wasan ba, Madrid ce kan gaba a teburin La Liga da maki 49 a wasanni 22, maki daya tsakaninsu da Atletico Madrid wadda zasu hadu ranar Asabar a Santiago, bayan nan kuma zasu ziyarci zakarun Ingila, Manchester City a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar 11 ga Fabrairu.
Sojojin sama na JMI sun sami nasarar kakkabo jiragen yaki na makiyan da aka sawwara, tare da amfani da makami mai suna Majid a cikin atisayen sojojin sama da suke gudanarwa a kudu masu yammacin kasar. Jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa dai, suna da masu muhimmanci a yakin zamani a halin yanzu, don haka sojojin sama na kasar suka bawa al-amarin muhiommanci. Banda haka tana da makiya wadanda suke da su a yankin wadanda suek amfani da irin wadannan makamai. A atisayen dai an sawwara jiragen makiya da dama a sararin samaniya, wadanda suke kokarin fadawa kasar, sannan aka cilla makaman garkuwan sararin samaniya samfurin Majid wadanda suka kakkabosu gaba daya.

Sojojin Iran Sun Fara Atisayen Soje Karu Na Biyu Mafi Yawa A Bangaren Garkuwan Sararin Samaniyar Kasar
Sojojin JMI sun bada sanarwan fara isayen soje karo na biyu a yankun tsakiya da kuma kudancin kasarTashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa za’a fara wannan atisayen ne a yau Talata 04 ga watan Fabrairu, kuma atisayen zai fi maida hankali ne a kan garkuwan tsaron kasar , wanda kuma ya kasance daga cikin shirye-shiryen kasar na shirin kare sararin samaniyar kasar ta sama. Labarin ya kara da cewa a wannan karom ma sojojin Iran da kuma dakarun juyin juya halin musulunci zasu yi atisayen hadin giwa ne don gwada karfin sojojin kasar da kuma IRGC na kare sararin samaniyar kasar. Kafin haka dai sojojin sun gwada karfinsu a bangarori daban daban na sojojin kasar don...
Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909. Wanda yafi yawan jefa kwallaye: Andriy Shevchenko kwallaye 14. Nasara mafi girma: inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001). Dan wasan dayafi buga wasan Derbi Madonnina Paolo Maldini wasanni 56. Haduwar da akafi jefa kwallaye Inter Milan 6-5 Ac Milan (6 Nuwamba 1949). Dan wasan da yafi yawan kwallaye a wasa guda José Altafini kwallaye 4 (27 Maris 1960). Dan wasa mafi shekaru daya jefa kwallo a wasan Zlatan Ibrahimović Shekaru 39 (26 Janairu 2021). Gaba daya a tarihi, kungiyoyin biyu...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka hada da na tattalin arziki siyasa, zamantakewa, tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji Karin bayanani daga bakin masana gwagwadon lokacinda muke da shi. Dafan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///..Madalla, masu sauraro, shirimmu nay au za iyi Magana dangane da ‘abinda ya sa ranar 9 ga watan Day ko kuma 29 ga watan Decemba yake da matukar muhimmanci ga Iraniyawa ko JMI?. A nan Iran ranar 9 ga watan Day na ko wace shekara tun shekara ta 2009, wanda...
Bisa alkaluman da hukumar kula da zirga-zirgar layin dogo ta kasar Sin ta bayar, tun daga kaddamar da zirga-zirgar fasinjoji a lokacin bikin bazara na Sin daga ranar 14 zuwa ranar 30 ga watan Janairu, yawan fasinjojin da jiragen kasa suka dauka ya kai miliyan 206 a kasar, kuma an yi zirga-zirgar fasinjojin cikin kwanciyar hankali. Yayin bikin, hukumomin kula da layin dogo na sassan kasar sun kara karfin aiki a wuraren da aka fi amfani da su, da inganta karfin ba da hidimmomin jiragen kasa da tashoshi, da aiwatar da matakan saukakawa jama’a, da kuma kokarin samar wa fasinjoji ingantacciyar hanyar tafiya. Alal misali, reshen Beijing na kamfanin kula da layin dogo na kasar Sin, ya kara tashoshin caji...
An nada Al-Julani da ya jagorancin kifar da gwamnatin Siriya a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya kasar ta Siriya Majiyoyin watsa labaran kasar Siriya sun tabbatar a jiya Laraba cewa: Sassan soja sun amince da nada Ahmed al-Sharaa da aka fi sani da (al-Jolani) a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar. Tun a jiya Laraba ce, shugaban sabuwar gwamnatin Siriya Ahmed al-Sharaa (al-Jolani) ya gabatar da jawabi na samun nasara bayan ganawa da shugabannin bangarorin soja a birnin Damascus fadar mulkin kasar, a gaban dandazon bangarori da dakarun Siriya. A yayin jawabinsa na nasara, Al-Sharaa ya ce: A yau kasar Siriya tana bukata abubuwa fiye da kowane lokaci, yana cewa, kamar yadda suka kuduri aniyar ‘yantar da kasar a baya, wajibi...
Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa. Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20 da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can. A cikin kafafen sadarwa na...
Shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG na shekarar 2025 sun gabatar da wata “liyafar al’adu” mai kyau da ban sha’awa, kuma mai fasahohi ga masu kallo na gida da waje, bisa sabbin dabaru. Ya zuwa karfe 2 na sanyin safiyar yau Laraba, a dukkan kafafen yada labarai, yawan mutanen da suka kalli shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG ya kai sau biliyan 16.8, wanda ya karu da kashi 18.31 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. Bugu da kari, yawan masu kallon shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG na 2025 ta hanyar talabijin yayin da aka watsa shi kai tsaye a cikin kasar, ya kai kashi 78.88 cikin dari, wanda ya kafa sabon tarihi a cikin...

Hukumar Gidagen Radiyo Da Talabijin Na Kasar Iran Ta Bada Sanarwan Kama Dan Rahotonta A Kasar Falasdinu Da Aka Mamaye
A dai-dai lokacinda jijiyoyin wuya suke kara tashi tsakanin JMI ta kuma HKI, jami’an tsaron HKI sun kama daya daga cikin yan rahotomta sun tsare. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar gidajen radiyo da Talabijin ta kasar (IRIB), Peyman Jebelli yana fadar haka ya kuma kara da cewa dan rahoton hukumar baya Gaza, yana cikin kasashen Falasdinu da aka mamaye ne. Sannan hukumar ta fara kokarin ganin an sake shi. Labarin ya kara da cewa tun ranar da aka fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 jami’an tsaron HKI sun kashe yan jaridu 205, sannan ta kama wasu 75, sannan har yanzun wasu 42 kuma tana tsare da su....
Kalaman shugaban Amurka na cewa zai tsarkake Zirin Gaza na Falasdinu ta ruda kawayen kasarsa na Larabawa tare da hargitsa su Wani mai sharhi na jaridar Washington Post David Ignatius ya ce kalaman shugaban Amurka Donald Trump na tsarkake Gaza da mika Falasdinawa zuwa Masar da Jordan ya sanya kasashen Larabawa da suke kawancen da Amurka cikin halin fargaba da dardar. Shafin watsa labaran Al-Quds Al-Arabi, ta yi nuni da cewa Trump ya gabatar da tunaninsa domin hanyar gabatar da shawarwari da tunani tana da dama tare da sabani da siyasa a aikace. Ta ce Trump na fuskantar daukan matakin yin kasadar da zai lalata kyawawan ra’ayinsa da bayyana munanan tunaninsa. Jaridar ta kara da cewa: shugaban na Amurka zai...
Haka kuma, an naɗa Muhammad Yahaya Liman a matsayin sabon Daraktan Akanta. Ya samu ƙwarewa a fannonin rahoton kuɗi da sarrafa kuɗi, ana sa ran zai taimaka wajen ƙara ƙarfin tsarin kuɗi na jihar. An kuma naɗa Akibu Isa Murtala, wanda a baya ya kasance Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ma’aikata, a matsayin Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Gudanarwa. Aikin sa shi ne kula da gudanar da ayyukan ma’aikatu. Injiniya Abubakar Sadiq kuma an naɗa a matsayin Mataimakin Manajan Darakta na Hukumar Samar da Ruwa da Tsabtace Muhalli a Ƙauyuka (RUWASA). An ɗora masa alhakin inganta samar da ruwa da tsabtace muhalli a yankunan karkara. Haka kuma, an kafa kwamiti na musamman domin farfaɗo da Hukumar Sufuri...
Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila. Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe watanni 15 ana gwabza kazamin yaki a Gaza. An fara aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu, kuma ana sa ran za’a saki Falasdinawa sama da 1,890 da ‘yan Isra’ila 33, wadanda ke cikin 240 da kungiyoyin Hamas ta yi garkuwa dasu a harin ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Tun lokacin yakin ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 47,306,...

CMG Ya Gabatar Da Bidiyon Dandanon Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Kasar Sin A Amurka Da Myanmar Da Indonesia Da Habasha Da Faransa Da Jamus Da Paraguay
Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo. Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an fara watsa wannan bidiyo a manyan allunan dake titunansa har tsawon kwanaki 7 masu zuwa a jere. Wannan shi ne karon farko da aka watsa irin wannan bidiyo a wannan kasa dake kudancin nahiyar Amurka. An ba da labari cewa, UNESCO ta shigo da bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato Bikin Bazara cikin jeren sunayen dake wakiltar kayayyakin al’adun gargajiya na tarihi...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara da burin da ake son kai wa bayan samun nasarar gwada sabbin na’urori da gudanar da ayyuka daban-daban, tare da samun nasarar gwajin kai hari kan wuraren abokan gaba. A wata hira da ya yi da manema labarai a yau Lahadi, Admiral Tangsiri ya bayyana cewa: A rana ta biyu ta atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19”...